Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Shin NLC Za Ta Iya Shiga Yajin Aiki Ko Kumfar Baki Ce Kawai? 27.07.2023 14:47
Send us Fan Mail A lokuta da dama idan gwamnati ta ɓullo da wani tsarin da ya ci karo da muradun 'yan kasa, ana sa ran ƙungiyar ƙwadago ta shige gaba wurin adawa da wannan tsari har sai an sauya matsaya. Sai dai irin wannan gargaɗi na yajin aiki da zanga-zanga da kungiyoyin ƙwadago ke yi a Najeriya, wasu na ganin barazana ce kawai, amma ba su iya aiwatar da komai, domin suna ganin kamar sun...
IPOB Na Kassara Tattalin Arzikin Kasuwanci A Dalilin Dokar Zaman Gida 25.07.2023 14:38
Send us Fan Mail Aƙalla kusan Shekaru biyu kenan da ƙungiyar 'yan awaren IPOB ta ƙaƙaba wa mutane zaman gida dole a duk ranakun litinin a yankin kudu maso gabashin Najeriya, a wani mataki na nuna adawa da cigaba da riƙe jagoran su Nnamdi Kanu. Saidai za a iya cewa lamarin kasuwancin yankin ya soma koma baya sosai, sakamakon yadda ake fargabar ziyartar wannan yanki. Ko da yake su ma wasu mazau...
Me Zai Faru Idan Tinubu Bai Miƙa Sunayen Ministoci A Wannan Makon Ba? 24.07.2023 14:08
Send us Fan Mail A yayin da 'yan Najeriya suka matsu su ji labarin cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sunayen ministoci majalisa, a yanzu dai kwanaki kaɗan suka rage wa shugaban a dokance. Makusantan shugaban ƙasar sun taɓa cewa “ba za a wuce kwana 30 ba tare da an gabatar da sunayen ministocin Tinubu ba” amma har yanzu saidai jita-jita. Ko meyasa aka kasa cika wannan alƙawarin? A c...
Hukuncin Taya Murnar Sabuwar Shekarar Musulunci!!! 21.07.2023 14:53
Send us Fan Mail Da Zarar an zo irin wanna lokaci da ake shiga sabuwar shekarar musulunci bayan kammala aikin hajji, yawancin mutane da kamfanoni za su rika tuwara ‘yan uwa da abokan arziki sakon barka da sabuwar shekarar musulunci. Sai dai ana ganin mutane basu cika ɗokin shekarar kamar ta miladiyya ba. To amma mene ne hukuncin taya murnar shiga sabuwar shekara a ka'idar addinin Musulunci. A...
Hanya Ɗaya Da Za Ta Sa Farashin Man Fetur Ya Sauka 20.07.2023 14:33
Send us Fan Mail Abu kamar wasa gameda batun ƙarin farashin man fetur, sai ga shi an wayi gari ana siyan shi sama da Naira 600, wanda kuma shi ne ƙari karo na biyu da aka yi cikin watanni biyu a wannan gwamnati. Tun bayan cire tallafin man fetur ɗin farashin sufuri da kayan masarufi ya riƙa hauhawa. Saidai akwai mafita guda daya da yawancin masu ruwa da tsaki suka yi amanna za ta kawo sauƙin man f...
Wane Ne Zai Zamo Sabon Shugaban Jam’iyyar APC? 18.07.2023 14:59
Send us Fan Mail An shiga ruɗani a jam’iyar APC bayan saukar Sanata Abdullahi Adamu daga shugabancin jam’iyar, duk da yake bai wuce shekara guda a muƙamin nasa ba, inda wasu rahotanni ke cewa rashin jituwa tsakanin shugaban na APC da Bola Tinubu ne ya tursasa masa sauka daga kujerar. Dama wasu sun dade suna jiran ganin yadda za ta kaya tsakanin shugaban kasar da Shugaban jam'iyyar APC mai mur...
Shin Ya Kamata A Sanya Sarakuna A Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa? 17.07.2023 14:20
Send us Fan Mail Sarakunan gargajiya na taka mahimmiyar rawa wajen gudanar da mulki da cigaban al’umma, saidai za a iya cewa babu wata saɗara da ta fayyace aikin su ƙarara a kundin tsarin mulki, lamarin da sarakunan ke cewa da yawa daga cikin 'yan siyasa, da zarar sun ci zaɓe sukan manta da su. Wasu na ganin lokaci ya yi da ya kamata su kasance a hukumance cikin kundin, duk da yake wasu na...
Illar Cin Bashi Daga Kamfanonin Bayar Da Bashin Ta Waya 14.07.2023 14:55
Send us Fan Mail Yadda kamfanonin da ke ba da rance ta waya ke addabar rayuwar jama’a na jefa su cikin kunci da damuwa. Lamarin yakan kai ga matakin kiran 'yan uwa da abokan arzikin wanda ya ci bashin domin bata musu suna. A gefe guda kuma, wasu na fadawa tarkon 'yan damfara. To amma me doka ta ce akan mutumin da ya ci bashi sannan ya kasa biya? A cikin shirin Najeriya A Yau, mun duba ya...
Abin Da Ya Hana Rikicin Mwaghavul Da Fulani Ƙarewa A Filato 13.07.2023 15:03
Send us Fan Mail Jihar Filato dake Arewa ta tsakiyar Najeriya ta yi ƙaurin suna wajen rikice-rikicen ƙabilanci da addini, domin dai ba kasafai ake shafe dogon lokaci ba tare da an sanya dokar ta ɓaci ba. Yawancin rikicin ya fi ƙamari tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma. To amma, wa ke da alhaki akan rura wutar wadannan rikice-rikice, kuma ta ina za a lalubo bakin zaren? Shirin Najeriya a Yau y...
Dalilin Da Ya Sa Shinkafa ‘Yar Gida Ke Ƙara Tsada 11.07.2023 13:58
Send us Fan Mail Har yanzu shinakafa ‘yar gida a Najeriya na ta ƙara tashin gwauron zabi duk da cewa a cikin gida ake sarrafa ta, lamarin da ya sa mutane da dama dake da ƙaramin ƙarfi ba sa iya saya. ‘Yan kasuwa kan shafe tsawon wuni guda ba tare da sun samu cinikin sisi ba. Ko kun san dalilin da ya sa shinkafa ‘yar gida ke ƙara tsada a Najeriya? A cikin shirin Najeriya a yau, za ku ji dalilin da...
Asarar Da Aka Yi Wurin Ritayar Manyan Sojoji 10.07.2023 14:52
Send us Fan Mail Tun sati uku da suka gabata da shugaban Najeriya Bola Ahmed ya nada sabbin hafsoshin sojin Najeriya ake ta sharhi kan yadda ya zama dole sama da manyan sojojin Najeriya 100 za su yi ritayar gaggawa. Shin akwai wata asara da ritayar gaggawar da manayan sojojin Najeriya za ta jan yo? Saurari shirin Najeriya domin jin cikakken bayani daga masana da kuma wadanda abin ya shafa.
Yadda Daily Trust Ke Bada Gudunmawa Tsawon Shekara 25 07.07.2023 14:19
Send us Fan Mail A bana jaridar Daily Trust ta cika shekara 25 da kafuwa. A tsawon wadannan shekaru, wadanne gudunmawa Daily Trust ta bayar a Najeriya? Shirin Najeriya A Yau na tafe da bayanan irin gudunmawar da jaridar Daily Trust ta bayar tsawon shekaru 25 da kafuwa a Najeriya.
Yadda Ake Neman Shugabanci A Majalisar Tarayyar Najeriya 06.07.2023 15:38
Send us Fan Mail Tun bayan kammala zaben shuwagabbanin majalisar tarayyar Najeriya da ya gudana a shekaran jiya Talata 4 ga Yulin Wannan shekara a zauren majalisar, hankali ya koma kan yadda za ayi rabon kwamitocin da ke zauren. Wane hali ake ciki a yanzu haka dangane da neman shugabancin kwamitoci a zauren Majalisar Tarayyar Najeriya? Shirin namu na wannan lokacin na tafe da cikakken bayani, Ku...
Dalilin Rashin Lafiyar Alhazan Najeriya Dubu 42 04.07.2023 15:49
Send us Fan Mail Rahotanni daga kasar Saudiyya na nuna cewa kusan rabin alhazan da suka je aikin Hajji bana sun gamu da rashin lafiya. Ko mene ne dalilin da Alhazan Najeriya suka samu kansu a yanayin rashin lafiya? Shirin Najeriya A Yau na tafe da karin bayani kan wannan batu.
Yadda Ake Shirin Bude Makarantu A Jihar Kano 03.07.2023 15:08
Send us Fan Mail Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce daga hawa mulkinsa zuwa yanzu ya buɗe makarantu 20 da gwamnatin da ta gabata ta rufe, ya kuma sake bude makarantun koyar da harkokin addinin musulunci na kananan hukumomin 44 da ke fadin Jihar domin samar da ingantaccen ilimi ga al’umma. Sanin cewa yau sabuwar gwamnatin Kano ke cika kwanaki 33 da karbar mulki, shirin Najeriya a yau ya ziy...
Dalilin Da Litar Mai Za Ta Iya Haura 700 A Arewa 30.06.2023 14:59
Send us Fan Mail A ranar 30 ga watan Mayu da ya gabata ne kamfanin Man Fetur Na Najeriya (NNPCL) ya bayyana cewa sabon farashin man fetur a Arewacin Najeriya ya zama sama da Naira 530 yayin da a Kudancin kasar ya ke tsakanin 470 zuwa 530, biyo bayan tabbatar da cire tallafin man fetur da sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi a jawabin kama aiki a ranar 29 ga Mayun 2023. Mene ne dalilin...
Yadda 'Yan Najeriya Su Ka Yi Sallah Cikin Tsadar Rayuwa 29.06.2023 14:48
Send us Fan Mail A yayin da ake cigaba da bikin babbar sallah a Najeriya, shirin Najeriya A Yau ya ziyarci jihohin Najeriya domin sanin yadda bikin sallar ke gudana. Ko ta wadanne bangarori tsadar man fetur da tsadar rayuwa suka shafi bikin babbar sallah bana? Shirin Najeriya A Yau na tafe da karin bayani.
Yadda 'Yan Najeriya Ke Tsayuwar Arfa Yau 27.06.2023 14:39
Send us Fan Mail Yau 9 ga watan Dhulhijja akwai 'yan Najeriya kusan dubu 95.000 a kasar Makka domin gudanar da ibadan aikin Hajji ba. A wane hali 'yan Najeriya ke gudanar da wannan ibada? Shirin Najeriya A Yau ya ziyarci Makka, ya kuma tattaro bayanan yadda aikin hajjin bana ke wakana.
Yadda Rukunin Gidaje 116 Suka Nitse A Abuja 26.06.2023 15:00
Send us Fan Mail Mamakon ruwan sama ya yi gyara a babban birnin tarayya, Abuja ranar Juma'ar da ta gabata, har aka yi ambaliyar da ta cinye rukunin wadansu gidaje 116. Ko yaya aka yi ruwan ya kutsa ya riski wadannan gidaje mallakar kamfanin Trademore har suka lume a ruwa? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da bayanai daga bakin mazauna wurin, ya kuma jiwo ta bakin hukumar bad...
Ko me ya jawo arahar raguna a bana 23.06.2023 14:52
Send us Fan Mail Da alama dai bana ragunan layya na da saukin farashi idan an kwatanta da bara warhaka, ko me ya jawo wannan saukin farashi? Shirin ya tuntubi jihohin Kano, Legas da kuma Sakkwato kan yadda ragunan layya ke araha a bana. Shirin ya kuma tuntubi malamin addini inda ya ja hankalin masu cewa dole sai sun yi layya ko da bashi ko da roko.
Yadda Tsadar Harkokin Zabe Ke Shafar Dimokuradiyya 22.06.2023 15:04
Send us Fan Mail Lura da yadda ake kai ruwa rana a kotunan sauraron kararrakin zabe, da irin manya-manyan lauyoyin da ake dauka ka san 'yan siyasa da hukumar zabe ta kasa na kashe makudan kudade wurin gudanar da wadannan shari'o'i. Ko ta wadanne hanyoyi wadannan kudade ke shafar dimukuradiyya da cigaban jama'a? Saurari shirin Najeriya A Yau domin wurin da gizo ke saka.
Yadda 'Yan Bindiga Ke Shirin Hana Noma Bana 20.06.2023 15:10
Send us Fan Mail A shekarar da ta gabata 'yan bindiga sun hana noma a wurare da dama a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya. Wanda hakan ya yi sanadiyyar wahalar abinci da tsadarsa a wadansu wuraren. Ko a wane hali ake ciki bana, ganin cewa damina ta fara kankama? Ku biyo mu cikin shirin sannu a hankali.
Yadda Cire Tallafin Man Fetur A Najeriya Ya Shafi Makwabtanta 19.06.2023 14:25
Send us Fan Mail Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya furta cewa wasu kasashen dake makwaftaka da Najeriya suna jin radadin cire tallafin man da aka yi fiye ma da ‘yan kasar Najeriya. Shirin namu na yau ya tsallaka kan iyaka ya shiga wasu kasashe makwaftan Najeriya domin mu ji ko abin da shugaban majalisar dattawan ya fada da gaske ne ko kuwa. Shin ko cire tallafin mai a Najer...
Dalilin Takaddamar Siyasa A Jihar Filato 16.06.2023 15:00
Send us Fan Mail Matakin sallamar shugabannin kananan hukumomi 17 da gwamna Caleb Muftwang ya dauka a jihar Filato bisa umarnin majalisar dokokin jihar ya haifar da rikicin da dole sai da hukumar 'yan sanda ta shiga tsakani. Shin dokar kasar Najeriya ce ta yarje wa gwamnan har ya iya daukar wannan mataki? Idan babu dokar da ta ba shi hurumin yin hakan, ke nan siyasa ce? Ku saurari shirin Naje...
Me Zai Faru Da Wanda Ya Ba Da Agajin Jini? 15.06.2023 15:09
Send us Fan Mail Bayar da agajin jini, ko kyautar jini, daya ne daga cikin ayyukan da ake kwadaitar da yi. Ko mene ne dalilin da ya sa ake son mutane su rika bada agajin jini? Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da masu abin cewa dangane da alfanun da ke tattare da bada agajin jini.
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.