Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Abin Da Ya Bambanta Sheikh Giro Argungu Sauran Malamai 08.09.2023

Send us Fan Mail Rasuwar Sheikh Abubakar Giro Argungu sakamakon rashin lafiya a daren shekaranjiya Laraba 6 ga Satumba, ta ruda mutane da dama, a Najeriya da kuma  makwabta.  Ko mene ne ya banbanta Sheikh Abubakar Giro Argungu da sauran al'umma?  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da bayanai game marigayin, daga bakin makusantansa.

Abin Da Ya Bambanta Kotun Zaɓen 2023 Da Na Baya 07.09.2023

Send us Fan Mail Abubuwa da dama sun faru a kotun sauraren ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a zaman ta na jiya. An yi fatali da wasu ƙararrakin yayin da jam'iyyu ke ta nuna bara'a da hukuncin. A shirin Najeriya a Yau, mun duba abin da ya bambanta zaman kotun da kuma hukunce-hukuncen da aka yi waɗanda suka sha bamban da na shekarun baya da aka saba yi

Dalilin Rufe Kasuwannin Dabbobi 8 A Jihar Zamfara 05.09.2023

Send us Fan Mail A kokarin magance kalubalen tsaro dake addabar jihar Zamafara, gwamnatin jihar ta ce a rufe dukkanin wasu kasuwannin dabbobi a jihar. Hakan ya biyo bayan korafe korafen da ake na cewa ana yawan kai dabbobin sata a irin wadannan kasuwanni. To amma meyasa aka maida hankali a kasuwannin dabbobi kadai? abin da shirin mu na Najeriya a yau ya maida hankali kenan.

‘Har Yanzu Ba Wacce Aka Tabbatar Ta Sume Bayan Yi Mata Sallama’ 04.09.2023

Send us Fan Mail Jita-jita ta karade kafafen sada zumunta cewa wadansu mata suna zuwa gidajen jama'a da zarar sun yi sallama an amsa sai wanda ya amsa ya sume.  Shin da gaske ne akwai wanda a ka taba yi wa sallama ta sume?  Shirin Najeriya A Yau ya ziyarci jihohin Najeriya hudu domin binciko gaskiyar labarin. 

Yadda Bawali A Waje Ke Yada Cututtuka 01.09.2023

Send us Fan Mail Mutane da dama na fakewa da sun matsu su rika yin bawali a kan titi, ko gefen wuraren shakatawa.  Ko kun san irin cututtukan da yin bawali a fili ke janyowa?  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da karin bayani. 

Mece ce Makomar Kwankwaso A Siyasar Najeriya? 31.08.2023

Send us Fan Mail Batun dakatarwar da jam’iyyar NNPP ta yi wa dan takararta na Shugaban Kasa a zaben 2023, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso na daya daga cikin batutuwan da ke daukar hankalin ’yan siyasa a Najeriya.  Shin da gaske ne wannan takalar hancin makomar Kwankwaso ne a siyasar Najeriya? Shirin Najeriya A Yau ya doki jaki ya doki taiki. A yi sauraro lafiya.

Yadda Masu Son Fara Ƙananan Sana’o’i Ke Wahala Wajen Yin Rajista 29.08.2023

Send us Fan Mail Masu son fara ƙananan sana'o'i kan fuskanci kalubale da dama a lokacin suke yunƙurin ganin sun tsaya da kafafun su, musamman gameda batun rijista da samun haƙƙin mallaka a wasu matakan. Irin waɗannan matakai ne ke sa mutum ya iya cin gajiyar wani abu idan ya taso da ke buƙatar sai an cika wasu sharuɗɗa. Sai dai ba kasafai ake samun iya cika ƙa'idojin cikin sauki ba....

Yadda Bude Madatsar Lagdo A Kamaru Zai Shafi 'Yan Najeriya 28.08.2023

Send us Fan Mail Hukumar kula da Harkokin Kasashen Waje Ta Najeriya ta aikewa Hukumar Bada Agajin Gaggawa NEMA sakon Kasar Kamaru na niyyar bude madatsar ruwan Lagdo, sakamakon cikar da madatsar ya yi. A bara bude wannan madatsa ya raba 'yan Najeriya sama da Miliyan guda da matsugunansu, ko ta wadanne bangarori wannan ruwa zai shafi Najeriya bana? Shirin Najeriya A Yau na tafe da karin bayani...

Shin Tinubu Zai Naɗa Ɗansa Ministan Matasa? 25.08.2023

Send us Fan Mail A daidai lokacin da aka zura ido domin ganin wanda za a naɗa ministan matasa, tuni shugabannin matasan APC suka cimma matsaya a kan shugaban ƙasa Tinubu ya naɗa ɗan sa a wannnan kujera. Sai dai kawunan matasan ya rabu, sakamakon yadda suka ce mulki ba abin da za a maida shi na 'yan uwa da iyali ba ne. Shirin Najeriya A Yau ya maida hankali kan yadda matasa ke ta kara-kai-na g...

Yadda Ministoci Ke Gasar Burge Tinubu 24.08.2023

Send us Fan Mail Tun bayan da aka rantsar da ministocin gwamnatin Tinubu, kowannen su ke ta shan alwashin cimma wani muradi ga 'yan Najeriya. Wasu ganin akwai alƙawuran da za a iya siffanta su da romon-baka, amma ba lallai su cika ba. A cikin shirin Najeriya a Yau, mun duba hanyoyin da ministocin za su bi domin ganin sun baiwa maraɗa kunya a kan alƙawuran da suka ɗauka.

Wuraren Da Wike Ke Shirin Rushewa A Abuja 22.08.2023

Send us Fan Mail Ana gama rantsar da sabbin ministocin Tinubu, aka hangi sabon ministan Abuja ya nufi ofishin sa inda ya gana da manema labarai kuma ya shaida musu cewa duk wanda ya yi ginin da ya saɓa da tsarin Abuja, zai rushe shi. Jin wannan sanarwa ta sa hantar wadanda ke zaune a wuraren da ministan ya kira da "Green Areas" a turance. To amma ina ne waɗannan wurare da lamarin zai sha...

Yadda Nadin Mata 131 Mukaman Siyasa Ya Tayar Da Kura A Neja 21.08.2023

Send us Fan Mail Nadin mata 131 mukamin masu taimakawa na musamman da Gwamnan Jihar Neja Muhammad Umar Bago ya yi a karshen makon jiya na ci gaba da daukar hankalin 'yan jihar.  Mene ne wannna nadin ke nufi, kuma ta wadanne bangarori zai shafi gwamnati da jama'ar jihar Neja? Ku biyo mu sannu a hankali cikin shirin. 

Me Ya Sa A Ke Naɗa 'Yan Arewa Ministocin Tsaro 18.08.2023

Send us Fan Mail Ƙididdiga ta nuna cewa yawancin ministocin da ake naɗa wa su jagoranci fannin tsaro a mulkin dimokraɗiyya suna fitowa ne daga yankin arewa. Ƙalubalen tsaro ya fi ƙamari a wannan yanki, abin da ya sa wasu ke ganin hakan wani salo ne da zai sa su maida hankali wajen magance damuwar yankin. A cikin shirin Najeriya a Yau, mun duba tasirin da nadin 'yan Arewa a matsayin ministocin...

Yadda Hauhawar Farashi Ke Hana ’Yan Najeriya Cin Abinci 17.08.2023

Send us Fan Mail Hukumar Kididdiga Ta Kasa NBS ta ce an samu hauhawan farashin kayan masarufi da kaso 24.08 a watan yunin da ya gabata.  Mene ne wadannan alkaluma ke nunawa, kuma ta wadanne bangarori suke shafar rayuwar 'yan Najeriya?  Shirin Najeriya A yau na tafe da karin bayani 

Abin Da Ya Sa Tarin Fuka Ya Yi Ƙamari A Kano 15.08.2023

Send us Fan Mail Rahotanni na cewa aƙalla mutum dubu takwas aka samu ɗauke da cutar tarin fuka a jihar Kano cikin sati guda. Ƙididdigar da aka fitar kwanan nan na nuna cewa jihar ita ce ta ɗaya a Najeriya dake ɗauke da wannan cuta. Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa cutar ta yi ƙamari a jihar Kano.

Abin Da Ke Hana Matasan Najeriya Ci-gaba 14.08.2023

Send us Fan Mail Matasan Najeriya na zama abin alfahari a kasashen duniya, sai dai a cikin gida abin ba haka yake ba, domin kuwa akwai daruruwan matasa da ke tafka abin kunya a kowace rana. Ko mene ne ke hana matasan Najeriya cigaba a cikin ƙasar? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya dubi wannan batu da idon basira. A yi sauraro lafiya.

Ƙuncin Da Ake Ciki A Kan Iyakar Najeriya Da Nijar 11.08.2023

Send us Fan Mail Rufe iyakar Najeriya da Nijar ya sa al'ummar dake rayuwa a waɗannan yankuna shiga wani hali na tsadar rayuwa, da tsayawar lamura cak. Masu sana’o’i a iyakokin dake maƙwabtaka da Nijar sun ce rayuwa tana neman tagayyara. Frashin kayan masarufi na daya daga cikin abin da ya fi tada hankali. Shirin Najeriya a Yau ya leƙa wasu iyakokin Najeriya da Nijar domin ganin yadda rayuwa t...

Yadda Kasuwannin Zamanin Gwamnoni Ke Karya ’Yan Kasuwa 10.08.2023

Send us Fan Mail Gwamnatoci a jihohi da dama sun rushe kuma sun gina sabbin kasuwanni na zamani. Abin da ya sa dole ake tashin 'yan kasuwa daga inda suke a baya. Saidai 'yan kasuwar na kukan lamarin ya fi ƙarfin su, domin ba sa iya mallakar shaguna a sabbin kasuwannin. Shirin Najeriya a yau ya duba yadda 'yan kasuwannin ke ci gaba da gudanar da rayuwa.

Yadda Za Ku Yi Rayuwar Abuja Cikin Sauƙi 08.08.2023

Send us Fan Mail Ana lasa ma mutane zuma a baki da cewar Abuja garin daɗi ne da samun kuɗi. Abin da ya sa mutane ke rububin zuwan ta da tsammanin ciko aljihun su Amma wasu sun ce da zarar sun sanya ƙafa a birnin, lissafi ke canzawa. A cikin shirin Najeriy a yau, mun lalubo muku hanyoyin da za ku iya rayuwa cikin sauƙi a birnin tarayya Abuja.

Yadda Zabin Ministocin Tinubu Ya Bar Baya Da Kura 07.08.2023

Send us Fan Mail Mika sunayen wadanda shugaban Kasar Najeriya BOla Ahmed Tinubu ya mika majalisa domin tantancewa ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan Najeriya.  Koi mene ne dalilin da ‘yan Najeriya ke ta musayar ra’ayi kan sunayen ministoci?  Shirin Najeriya A  Yau na wannan lokaci na tafe da karin bayani.   

Makomar Jam’iyyar APC Bayan Zaɓen Ganduje 04.08.2023

Send us Fan Mail Jam’iyyar APC mai mulki ta tabbatar da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugabanta na ƙasa. Ko da yake lamarin bai zo da mamaki ba, kasancewar an daɗe ana yaɗa wannan jita-jita, wanda wasu ke ganin shi ya sa babu sunansa a cikin ministoci daga jihar. Ganduje ya maye gurbin tsohon gwamnan Jihar Nassarawa, Abdullahi Adamu wanda ya sauka bisa raɗin kansa, lamari...

Abin Da Ya Hana 'Yan Najeriya Fita Zanga-Zangar NLC 03.08.2023

Send us Fan Mail Jiya Laraba 'ya'yan kungiyar kwadago ta Najeriya su ka fara zanga-zangar lumana domin nuna adawa da wadansu tsarukan gwamnatin tarayya.  Sai dai gama garin 'yan Najeriya ba su shiga wannan zanga-zangar ba. Ko mene ne ya sa 'yan Najeriya kauracewa wannan zanga-zanga a dai-dai wannan lokaci?  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da karin bayani

Yadda Kanawa Ke Gwara Kawunan Su Akan Hotunan Sarakuna 01.08.2023

Send us Fan Mail Bayyanar hotunan sarki Sanusi na II a ɗakin taro na fadar gwamnatin jihar ya sa ana ta tunanin ko dai gwamnati jihar na shirin mayar wa sarkin sarautar shi ce, kamar yadda wasu ke ta hasashe da zarar sun shiga gwamnati. Lamarin dai ya yi ta jawo ce-ce-ku-ce, musamman da ake ganin Sanusin na ɗasawa da gwamnatin Jihar. Saidai gwamnatin ta ce ba a saka hoton saboda wata manufa ba sai...

Abin Da Kungiyar Kwadago Ke Shirin Yi A Jihohi 31.07.2023

Send us Fan Mail Tun bayan tabbatar da cire tallafin man fetur da shugaban Najeriya Bola Ahmed ya yi a ranar da ya kama aiki a Najeriya 'yan kasar ke kukan tsanantan tattalin arzika, da ya jefa rayuwar mutane da dama cikin tashin hankali.  Kungiyar kwadago ta Najeriya ta shirya gangami na gama gari a ranar Laraba mai zuwa, ko a wane hali a ke ciki a jihohin kasar nan?  Shirin Najeriya A Yau y...

Halin Ƙuncin Da Aka Jefa Marasa Lafiya Sakamakon Yajin Aiki 28.07.2023

Send us Fan Mail Yajin aikin ƙungiyar likitocin Najeriya NARD ya sa harkokin kiwon lafiya a fadin Najeriya sun tsaya cak. Marasa lafiya na ta zuwa asibitoci amma kuma sai dai su su mayar da yan uwansu gida saboda babu likita da zai duba su. A cikin shirin Najeriya a yau, mun duba yanayin da yajin aikin ya jefa al'umma musamman marasa lafiya.

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.