Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Abin Da Ya Sa Iyaye Ke Tsoron Malamai Su Hukunta ‘Ya’Yansu 23.10.2023

Send us Fan Mail A Shekarun baya iyaye kan damka amanar ‘ya’yansu kacokan ga malamai domin karatu da tarbiyya, wannan kuma ba iya malaman addini kadai ba, harda malaman makarantun  boko.  Sai dai a ‘yan shekarun nan, iyaye sun samu shakku dangane da hukunta ‘ya’yansu a makaranta, mene ne abin da ya janza har aka samu kai a irin wannan hali?  Shirin Najeriya A Yau na tafe da tattaunawa ta musamman...

Martanin Tubabbun ’Yan Boko Haram Kan Tuban Muzuru 20.10.2023

Send us Fan Mail Rahotanni daga Jihar Borno sun tabbatar da cewa an mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram 6,900 cikin al’umma a bayan dogon lokaci ana yi musu bitar zaman lafiya da sauya musu tunani.  Anya babu masu tuban muzuru a cikinsu kuwa?  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya dubi wannan batu, ya ji ta bakin wasu tubabbun mayaƙan Boko Haram da kuma masana harkokin tsaro. 

Yadda Mazauna Iyakar Najeriya Da Nijar Suka Shiga Ha’ula’i Bayan Rufe Boda 19.10.2023

Send us Fan Mail ’Yan Najeriya mazauna yankunan da ke iyakar kasar Jamhuriyar Nijar na dandana kudarsu sakamakon tsadar rayuwa da tashin gwauron zabon kayan masarufi, tun bayan rufe bodar da Najeriya ta yi a watan Agusta. Anya wannan rufe boda da Kungiyar ECOWAS ta sa aka yi, ba za a ci kai da kai ba? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya ziyarci garin Illela a Jihar Sakkwato da Maigatari a Ji...

Yadda Barace-Baracen Ƙananan Yara Ke Karuwa A Najeriya 17.10.2023

Send us Fan Mail Rahotanni daga wadansu jihohin Najeriya na bayyana cewa an samu karuwan adadin yara kanana da ke shekarun zuwa makaranta a matsayin mabarata a kan titunan da lungunan manyan unguwanni a sassan kasar nan.  Shin mene ne ya kawo wannan lamari na adadin yaran da ke bara a tsakanin jamaá a daidai wannan lokaci da ake kurin cigaba, wayewa da sanin kimar bil-Adama?  Shirin Najeriya A Yau...

Yadda Ba Wa Masu Shigo Da Shinkafar Waje Dala Zai Shafi Farashin Ta Gida 16.10.2023

Send us Fan Mail Babban Bankin Najeriya CBN ya dage dakatar da bada dala ga masu shigo da shinkafa daga kasashen ketare da kuma wasu kayayyaki 43 bayan sama da shekara bakwai.  Ka wannan mataki zai sa farshin shinkafar gida ya sauka?  Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci ya dubi wannan batu. Latsa nan, domin sauke shirin da sauraro a lokacin da ku ke so. 

“Abin Da Ya Tabarbarar Da Tarbiyya A Wannan Zamani” 13.10.2023

Send us Fan Mail A ‘yan shekarun nan, kullum batun tabarbarewar tarbiyya na kara yawa, ha ta kai ga yara sun fara nadar murya da hotunan iyayensu in suna musu fada kan wani abu da su ka yi ba daidai ba.  Shin mene ne ya faru tarbiyya ta tabarbare haka?  Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci ya dubi wannan batu. Latsa nan, domin sauke shirin da sauraro a lokacin da ku ke so. 

Yadda Gwamnati Ke Shirin Sanya Takunkumi Kan Soshiyal Midiya 12.10.2023

Send us Fan Mail Hukumar kula da Kafofin Yaaɗa Labarai ta Najeriya (NBC) na shirin ɓullo da wasu matakai kan masu amfani da shafukan sada zumunta na zamani a wani yunkuri na tsaftace ɓangaren domin hana gurbata tarbiyyar ’yan kasar nan. Anya zai yi wu a sanya ido yadda ya kamata a kan kafofin sada zumunta yadda ya kamata a Najeriya? An sha kai ruwa rana da ’yan Najeriya kan wannan kuduri na gwamna...

Yadda Ake Maganin Ciwon Damuwa 10.10.2023

Send us Fan Mail Hukumar Lafiya ta Duniya W.H.O ta ware ranar 10 ga watan Oktoba a ko wace shekara a matsayin ranar lafiyar kwakwalwa ta Duniya. Mene ne fahimtar ýan Najeriya kan lafiyar kwakwalwa, kuma wadanne hanyoyi mutum ya kamata ya bi domin inganta lafiyar kwakwalwarsa?  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da karin bayani. 

Gaskiyar Batun Satar Mazakuta (Shafimulera) 09.10.2023

Send us Fan Mail A 'yan kwanakin nan, wani abu da ake ganin kamar al'mara,  batun satar mazakuta (shafimuleara) ya kara bayyana a tsakanin jama'a.  Shin da gaske ne ana satar mazakuta?  Shirin Najeriya A Yau ya bi diddigin wannan batu, ya tattauna da wani da ake zargin an sace masa mazakuta, kuma ya ji ta bakin likitoci. 

“Yadda Amicewa Da Yarjejeniya A Takarda Zai Iya Jefa Ka A Rigima ” 06.10.2023

Send us Fan Mail Mutane da dama na sanya hannu a takardu ko amincewa da manhaja ba tare da sun karanta kaídojin da ke kunshe a cikinsu kwarai da gaske ba.  Shin ko ka san rigimar da sanya hanu a takarda ba tare da cikakken nazari ba zai iya shigar da kai?  Saurari shirin NAjeriya A Yau na wannan lokaci domin sanin hanyoyin kaucewa shiga rigima sakamakon sanya hannu a takarda ko kuma yarjewa manhaj...

An Hana Ni Aure Saboda Ni Malamin Makaranta Ne 05.10.2023

Send us Fan Mail Majalisar ɗinkin duniya ta ware kowace ranar 5 ga watan Oktoba, a matsayin ranar malamai ta duniya. Saidai bincike ya nuna cewa jama'a da dama na kallon aikin malunta a matsayin aikin marasa galihu. A cikin shirin Najeriya a Yau mun zanta da wani malamin makaranta da aka hana shi aure saboda yana aikin koyarwa.

’Yan Bindiga Sun Mayar Da Zamfarawa Bayi A Wurin Hakar Zinare 03.10.2023

Send us Fan Mail Ta’addancin ’yan bindiga ya dauki sabon salo a Jihar Zamfara, duk da kokarin gwamnati na murkushe su. Lamarin ya kai ga jama’a na barin gidajensusu, su kwana a dokar daji a yayin da ’yan bindigar suka mamaye wuraren hakar zinare, inda suke tilasta mutane hako musu ma’adinai. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da karin bayani.

Bai kamata ƙarin albashin wucin gadi ya tsaya a wata shida ba 02.10.2023

Send us Fan Mail Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta kara Naira Dubu Ashirin Da Biyar kan albashin kananan ma’aikatan Najeriya  A jawabinsa na ranar cika shekaru 63 da samun ‘yancin kan kasar nan.  Ta wadanne bangarori wannan kari zai shafi rayuwar ku?  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya dubi wannan batu, ya ji ta bakin masana, ya kuma binciko shin bayan watann...

Abin Da Hukuncin Zaben Jihar Kaduna Ke Nufi 29.09.2023

Send us Fan Mail Kotun sauraron karar zaben 2023 na gwamnan Jihar Kaduna karkashin jagorancin mai shari’a Victor Oviawe ya ba da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 24 da ke mazabu bakwai na kananan hukumomi hudu da suka kunshi masu rajista 16,300 a zaman yanke hukunci da ya gudana ta kafar zoom a jiya Alhamis a jihar Kaduna, nan da kasa da kwanaki 90.   Mene ne wannan hukuncin ke nufi? ...

‘Yadda Yawan Ciyo Bashi Zai Durƙusar Da Najeriya’ 28.09.2023

Send us Fan Mail Bayanai na cewa bashin da Najeriya ka kai a yanzu ya haura Naira tiriliyan ɗaya a ƙarƙashin gwamnatin Bola Tinubu. Masu sharhi na ganin idan har aka cigaba da karɓo basuka irin haka, nan ba da jimawa ba ƙasar za ta iya rasa ikonta. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan wannan lamari na cin bashi a Najeriya.

Wa Ya Kamata Ka Sa A Matsayin Magajinka? 26.09.2023

Send us Fan Mail Kowane mutum na fatan ganin ya samu magaji amintacce wanda ba zai iya cin amanar sa ba, musamman wajen cike wasu takardu a rayuwa. Wasu mutanen kan saka matansu ko 'ya'ya ko miji. Amma akwai masu fargabar hakan kuskure ne saboda komai na iya faruwa. A shrin Najeriya a Yau mun yi nazari a kan mutumin da ya kamata a riƙa sakawa a matsayin magaji.

“Yadda Na Sayar Da Gado Na Na Yi Karatu” 25.09.2023

Send us Fan Mail Alkaluma da ke bayyana binciken da ake yawan yi kan wadanda basa zuwa makaranta  musamman a Arewacin Najeriya na nuna cewa mata ne suka fi yawa a cikin wadan da  basa zuwa karatu.   Mene ne ke hana mata da dama karatu a Arewacin Najeriya?  Shirin Najeriya A Yau na tafe da bayanai daga bakin ‘yan mata, da matan da suka  samun damar yin karatu, da kuma shawarwarin yadda za a magance...

Wane Mataki Za A Ɗauka Kan Cin Zarafi Da Kisan ‘Yan Jarida 22.09.2023

Send us Fan Mail A duk lokacin da ake wani al’amari da jama’a ke bukatar masaniya a kai, ‘yan jarida na sahun gaba wajen ganin sun kutsa domin samun rahotanni. Sai dai a lokuta da dama a kan samu cikas daga wasu jami’an tsaro da a ko da yaushe kokarin su shine hana ‘yan jarida shiga wasu wurare musamman idan abun ya shafi manyan jami’an gwamnati. A gefe guda kuma, wasu ‘yan jaridan na gamuwa da aj...

Me Zai Faru Bayan Hukuncin Kotu Kan Zaɓen Kano 21.09.2023

Send us Fan Mail Za a iya bakin aƙalami ya bushe a tashin farko na matakin kujerar gwamna a jihar Kano. An gudanar da shari'ar da ta baiwa Nasiru Gawuna na jam'iyar APC nasa a kan gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a wani salo na zamani da wasu basu taɓa gani ba. Shirin Najeriya a Yau ya duba me zai iya faruwa bayan wannan hukuncin.

Shin Matasa Sun Gamsu Da Ministocin Da Ake Son Naɗa Musu? 19.09.2023

Send us Fan Mail An bayyana sunan matasa sabbin jini har mutum 2 da ake son naɗawa a muƙamin ministocin ma’aikatar matasa ta Najeriya. Yawanci an saba ma’aikatar matasa akan haɗe ta da ta wasanni a damƙawa mutum guda, sai gashi a wannan karon an yi ƙarami da babbar mnistan matasa, kuma dukansu ba wanda ya haura shekara 35. To ko yanzu za a iya cewa waɗannan matasa da za a naɗa zai gamsar sabbin ji...

Yadda 'Yan Kasuwa Ke Neman Hana Kayan Abinci Sauka 18.09.2023

Send us Fan Mail Rahotanni daga wadansu jihohin Najeriya na bayyana cewa farashin kayan abincin ya sauka a kasuwanni, sakamakon fara shigowar kaka, sai dai a wadansu jihohin kuma kamar Katsina farashin hawa ya ke.  Ko mene ne dalilin karuwar farashin kayan masarufi a wadansu kasuwannin?  Shirin Najeriya A Yau ya bankado gaskiyar dalilan da farashin kayan abincin ke hauhawa duk da shigowar kaka.  D...

Wa Zai Kula Da Motocin Sufurin Da Zulum Ya Kawo? 15.09.2023

Send us Fan Mail Gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum ya kaddamar da motocin sufuri a kwaryar birnin jihar, domin rage radadin cire tallafin man fetur din da aka yi a Kasar nan.  Shin ta wadanne hanyoyi za a bi domin kula da wadannan motoci?  Shirin Najeriya A Yau ya ji ta bakin jamaar Borno, ya kuma bi diddigin hanyoyin da gwamnatin za ta bi wurin kula da motoci...

Yadda Matsin Tattalin Arziki Ke Shafar Karatu A Najeriya 14.09.2023

Send us Fan Mail A yayin da aka dawo karatu a makarantun Firamare da Sakandare a wadansu sassan Najeriya a farkon wannan makon.  Ko a wane irin hali  iyayen yara su ka tsinci kan su?  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya zanta da iyayen, ya kuma ji ta bakin wani mai makaranta domin sanin yadda matsin tattalin arziki ke shafar dawowar yara makaranta. 

Dalilin Da Ake Yawan Samun Hatsarin Jirgin Ruwa A Neja 12.09.2023

Send us Fan Mail Daga watan Agustan 2023 zuwa yanzu,  an samu hatsarin jirgin ruwa sau 3 a Jihar Neja wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama, da kuma dukiya mai tarin yawa. Shin mene ne ke janyo yawaitar  hatsarin jirgin ruwan? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da karin bayani. Latsa nan domin sauke shirin kai tsaye.

"Hanyoyi 5 Da Sarakunan Gargajiya Za Su Kawo Karshen Taadanci" 11.09.2023

Send us Fan Mail Kungiyar gwamnonin Arewa Maso Gabashin Najeriya ta bayyana cewa akwai sarakunan gargajiya da ke sauke baki ba tare da bincike ba, wadanda wasu kan rikide zuwa yan ta'adda. Ko mene ne abin da ya kamata a yi domin magance gurbacewar al'umma? Shirin Najeriya A Yau ya ji ta bakin sarakunan gargajiya, ya kuma ji ta bakin wani masanin tsaro domin gano bakin zaren.

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.