Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Makomar Kakakin Majalisa Ɗan Jam'iyar Adawa A Filato 05.12.2023 12:51
Send us Fan Mail Ana ta kai ruwa rana a majalisar jihar Filato gameda yadda shugabanci zai kasance daga ɗan jam'iyar adawa da ba su da rinjaye. Akwai 'yan majalisar APC da kotu ta baiwa nasara bayan tsige mafi yawancin yan jam'iyar PDP, duk da yake ba a rantsar da su ba amma majalisa tana hutu. Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ake tirka-tirka a majalisar dokokin jihar Filato da z...
Manyan Cututtukan Da Zazzabin 'Malariya' Ke Iya Janyowa 04.12.2023 14:50
Send us Fan Mail Jama’a na yi wa zazzabin malariya kallon wani zazzabi da bai taka kara ya karya ba. Sai dai kuma masana suna yiwa wannan zazzabi wani irin kallo. Ko kun san manyan cutukan da zazzabin malariya zai iya haifarwa? Shirin namu na wannan lokaci na tafe da gamsassun bayanai kan hanyoyin kariya.
Yadda Ýan Damfara Ke Turawa Mutane “Rasit” Da “Alat” Din Bogi 01.12.2023 14:56
Send us Fan Mail Ýan damfara kullum na kara kaimu wurin fito da sabbin dabarun cutar jamaá ta hanyoyi daban daban. Shin ko kun san ana iya tura maka alat da rasit din kudi na bogi? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da wadansu da aka turawa rasit da alat na bogi, ya kuma ji ta bakin wani masani kuma mai sharhi akan dabarun sadarwa ta intanet.
Yadda Mabaratan Zamani Ke Neman Hana Bayar Da Sadaka 30.11.2023 14:59
Send us Fan Mail Lamarin ya kai da wuya mutum ya fito ya koma gida ba tare da wani ya yi masa ba-zata ya roke shi kudi ko abin ci ba. Yawancin masu irin wannan rokon sukan fito ne tsaf-tsaf kamar wasu ma’aikata ko ’yan kasuwa. Shin yaya jama’a ke kallon wannan dabi’a da ta zama ruwan dare? Shirin Najeriya A Yau na wanna lokaci na tafe da karin bayani.
Abin Da Ya Sa Masu Zaman Waƙafi Ke Shafe Shekaru Ba Hukunci 28.11.2023 13:25
Send us Fan Mail Rayuwa ta kan sauya a duk lokacin da mutumin da ke zaman waƙafi a gidan kaso ya shafe dogon lokaci babu hukunci amma daga bisani aka sake shi. Akwai dubban mutane da ke jiran yanke hukunci a kotuna da kuma waɗanda basu san makomar su ba. To amma me ya sa ake samun wannan tsaiko? Abin da shirin Najeriya na yau ya duba kenan.
Yadda ‘Yan Najeriya Ke Tafka Asara Saboda Wasa Da Lokaci 27.11.2023 13:41
Send us Fan Mail Lokaci daya ne daga cikin abubbuwan da ake wasa dasu masu matukar muhimmamnci a Najeriya. Wanda sakamakon hakan mutane na tafka asara. Shin Mene ne abin da yasa ‘yan Najeriya ke wasa da lokaci? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya dubi wannan batu da idon basira.
Shin Ko Akwai Lalaci Kan Yadda Wasu Mazan Kan Sakarwa Matan Su Ragamar Gida 24.11.2023 14:54
Send us Fan Mail Tun dauri a arewacin Naijeriya, Maza aka sani da rike da ragamar gida, ta hanyar fita a nemo abun da za a ciyar da iyali, yayin da mata ke lura da aikace-aikacen gida. Wasu matan kan yi sana’o’i na gida da niyyar samun kudin kashewa da ba dole sai an tambayi maigida ba. To a yanzu an shiga yanayin da wasu mazan ke sakarwa mata ragamar gida kacokan. Shirin Naijeriya A Yau, ya yi d...
Matakan Da Za Ku Kare Lafiyar Ku A Lokacin Sanyi 23.11.2023 14:58
Send us Fan Mail Da zarar an shiga lokacin sanyi, a kan samu cututtuka da dama dake yawo saboda kaɗawar iska. A gefe guda kuma akwai batun kula da lafiyar fata ga masu kaushin jiki da bushewar fata. Shirin Najeriya a Yau ya duba matakan da ya kamata ku dauka wajen kare lafiyar ku a lokacin sanyi da hunturu.
Shin Hukuncin Kotuna Kan Gwamnoni Ya Sauya Dimokariɗiyya? 21.11.2023 14:55
Send us Fan Mail Kotuna da dama sun yanke hukunci mabanbanta a kan kujerun gwamnoni, inda aka soke wasu da suke jam'iyyar adawa da ma jam'iya mai ci. Ana ganin hakan kamar wani sauyi ne ga dimokraɗiyya wajen yanke hukunci ba sani ba sabo. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan ci gaban da aka samu ga dimokraɗiyya bayan hukunce-hukuncen kotuna kan kujerun gwamnoni.
Yadda TikTok Ke Lalata Tarbiyyar Matasa 20.11.2023 14:33
Send us Fan Mail Raye-raye da tsalle-tsalle na rashin tarbiyya na ci gaba da samun karbuwa a kafar sada zumunta na zamani da ake wa lakabi da Tiktok. Ta yadda kusan babu irin rashin tarbiyyar da ba a bayyanawa a wannan kafa. Shin wace irin illa wannan kafa take yi ga cigaban karatun matasan Najeriya?
Hanyar Da Za A Kaucewa Tsadar Albasa 17.11.2023 14:57
Send us Fan Mail Buhun albasa a kasuwannin Arewacin Najeriya ya kai sama da Naira Dubu Dari a ýan kwanakin nan. Shin mene ne abin da ya sa albasa tsada fiye da sauran shekaru a Najeriya? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da manoma, manyan ýankasuwar albasa da kuma wata likitar abinci akan tsadar albasa da amfaninta a jikin dan Adam.
Yadda Yajin Aiki Ke Shafar Fannin Ilimi 16.11.2023 13:29
Send us Fan Mail Yajin aikin 'yan ƙwadago ya haɗa har da na malaman jami'o'i a Najeriya, inda aka kulle makarantu a matakai daban-daban. Hakan yana shafar ɓangaren ilimi da wasu ke ganin za a samu koma baya idan ba a dakatar da yajin aikin ba. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan tasirin yajin aiki ga fannin ilimi ko akasin haka.
Abin Da Ke Hana Magani Aiki A Jikin Mutum 14.11.2023 14:21
Send us Fan Mail Mutane da dama kan ce wani magani ya daina yi musu aiki ko kuma baya yi musu aiki bayan a wani lokaci da ya wuce yana yi musu aiki. Mene ne abin da ke hana magani aiki a jikin mutum? Shirin namu na wannan lokaci na tafe da tattaunawa ta musamman akan abin da ke hana magani yin aiki a jikin dan-Adam.
Abin Da Za A Yi In Ana So A Hana Sayen Kuri’a-Masana 13.11.2023 14:26
Send us Fan Mail Sayen kuri’a daya ne daga cikin abubbuwan da masana ke bayyanawa a matsayin wani abu da ke tadiye kafar Dimukuradiyya a Najeriya. Mene ne abin da ya kamata a yi domin hana sayen kuri’a? Shirin Najeriya A Yau ya dubi yadda ake sayen kuri’a a zabukan Najeriya, ya kuma tattauna da masana kan hanyoyin da za a bi domin magance wannan matsala.
Yadda Ake Wahalar Tsabar Kudi A Wadansu Jihohin Najeriya 09.11.2023 14:29
Send us Fan Mail Wahalar tsabar kudi na cigaba da karuwa a wadansu jihohin Najeriya duk da bayanin cigaba da amfani da tsoffin kudaden da CBN ya ce a ci-gaba da yi. Idan ba a manta ba, a watan Mayun wannan shekarar kotun kolin Najeriya ta ce a cigaba da amfani da tsoffin kudaden har 31 ga Disamba mai zuwa, sai kuma gashi CBN ta fitar da sanarwa kafin wannan lokaci, duk da cewa sanarwar ta CBN ba...
Tsadar Gas Ya Tilasta wa Magidanta Yin Griki Da Itace 09.11.2023 14:47
Send us Fan Mail Farashin Gas din girki yana ta hawa da sauka a kasuwanni daban-daban, lamarin da ya sa iyalai da dama ke kukan yadda hakan ke tilasta su ajiye amfani da tukunyar Gas. Wasu diloli na cewa abin da ke faruwa ba laifinsu bane, yayinda magidanta ke ganin ba yadda suka iya yanzu tunda sun saba da yin girki da Gas. Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda hauhawar farashin Gas ya tilastawa ma...
Dalilin Dawowar Hare-Haren ’Yan Ta’adda A Arewa Maso Gabas 07.11.2023 13:09
Send us Fan Mail Ana murna da raguwar hare-haren 'yan ta'adda a yankin Arewa maso gabas, sai ga shi wasu alamu na nuna akwai yiwuwar wasu na shirin dawo da hannun agogo baya. A 'yan kwanakin nan an samu barazanar kai hare-hare da wasu bayanan sirri a yankunan da ake ganin an ci ƙarfin 'yan ta'addan. Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda 'yan ta'adda ke yunƙurin daw...
Yadda ’Yan Najeriya Za Su Kwaci Hakkinsu Daga Gwamanti Cikin Sauki 06.11.2023 14:51
Send us Fan Mail Ana bayyana mulkin dimukuradiyya a matsayin tsarin mulkin da ke bada dama ga 'yan kasa su tofa albarkacin bakinsu dangane da ayyukan da ake yi, suna iya sa wa a yi ko kuma a bari. Shin 'yan Najeriya sun san hanyoyin da za su karbi hakkinsu daga wurin gwamanati kuwa? Shirin Najeriya A Yau na tafe da karin bayani.
Yadda Cin Abinci Sau Uku Ya Zama Rahama A Wurin Masu Aikin Albashi 03.11.2023 14:54
Send us Fan Mail Yawancin mutane na tunanin da zarar mutum na aikin albashi, to za a iya cewa yana shan ƙarfin matsalolinsa. Saidai da dama daga cikin ma'aikata na cewa albashi ko da nawa ake biyan mutum ba ya iya riƙe shi zuwa ƙarshen wata, sai an yi da ƙyar da cin bashi. Shirin Najeriya a Yau ya duba yanayin da ma'aikatan albashi ke iya rayuwa tare da albashin su cif-cif har wata ya ƙa...
Abin Da Ya Sa Hisba Ta Yi Kame A Kano 02.11.2023 14:54
Send us Fan Mail Rahotanni daga Jihar Kano sun bayyana cewa Hukumar HISBA ta kai samame wani hotel da kuma wasu gidaje a jihar. Ko mene ne abin da ya sa hukumar HISBA kai wannan samame a wannan lokaci? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya binciko abin da ya sa HISBA ta dauki wannan mataki a yanzu.
Shin Ya Kamata A Goyi Bayan Mulkin Shekara Shida-Shida A Najeriya? 31.10.2023 14:58
Send us Fan Mail Kiran da jagoran jam'iyar adawa ta PDP a Najeriya ya yi na a sauya tsarin shugabancin ƙasar nan zuwa shekara shida-shida ga kowane yanki ya sa ana ta tunanin ta ya hakan zai iya faruwa. Wasu ƙasashe dai na bin tsarin gudanar da zaɓe har zagaye biyu, kuma ana mulkin kujerar shugaban ƙasa tsawon shekara shida kacal. A cikin shirin Najeriya a yau ya duba yiwuwar tsarin mulkin sh...
Abin Da Ya Kamata A Yi In Ana Son Hana ‘Yan Najeriya Fita Ci-Rani Turai 30.10.2023 14:43
Send us Fan Mail Matsin tattalin arziki da rashin tsaro na daga cikin dalilan da ke turasasawa ‘yan Najeriya tafiya ci-rani kasashen duniya. Mene ne abin da ya kamata a yi domin kawo karshen wadannan matsalolin? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da masu neman fita, ya kuma bankado gaskiyar abin da ya kamata a yi domin magance yawon ciranin ‘yan Nakeriya a kasashen duniya.
Abin Da Ke Sa Wasu Zargin Allurar Riga-Kafi Ta Cutar Da Su 27.10.2023 13:59
Send us Fan Mail Mutane da dama na tsoron allurar riga-kafi, domin labarin zargin cutarwar da ta yi wa wani, ko kuma zaton cutarwar da ta yi musu. Mene ne gaskiyar abin da ke sa allurar riga-kafi zama kamar ta cutar da lafiyar wanda aka yi wa? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya bi diddigin wannan batu, ya ji ta bkin wani da ke zaton allurar riga-kafi ta cutar da wani nasa. Kuma shirin ya...
Yadda ‘Yan Damfara Su Ka Tara Miliyoyi Daga Masu Neman Tallafin Gwamnati 26.10.2023 14:39
Send us Fan Mail A wannan yanayi da ake ciki, yawancin ‘yan najeriya na fatan ganin sun ci gajiyar tallafin gwamnatin tarayya ga magidanta miliyan 15 da aka ce za a raba, domin rage radadin cire tallafin man fetur. Saidai an samu wasu mutane da suka yi amfani da wannan dama wajen damfarar mutum sama da dubu tara miliyoyin kudi da sunan za su sanya su cikin wadan da za su ci gajiyar tsarin. Shirin...
Ainihin Abin Da Ya Hana Farashin Dala Sauka 24.10.2023 14:44
Send us Fan Mail Dakile hauhawar farashin dala da dawo da martaba da kimar Naira daya ne daga cikin abubuwan da masu neman shugabancin kasar nan a lokacin yakin neman zabe duk suka sha alwashin mayar da hankali akai. A kasuwannin bayan fage dai yanzu Dala ta haura Naira dubu daya. Ko mene ne abin da ya hana farashin Dalar sauka? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da masu ruwa da...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.