Najeriya a Yau
Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Abin Da Ya Sa Rashin Tsaro Ke Neman Cinye Abuja 18.01.2024 14:31
Send us Fan Mail A ‘yan kwanakin nan hankali ya koma birnin tarayya Abuja ta fannin tsaro. ‘Yan bindiga da masu garkuwa dan neman kudin fansa suna ta farmakar yankunan birnin da ake ganin wuri mafi tsaro a Najeriya. Shin me ya sa ‘yan bindigar suka karkato da ayyukansu a yankin? Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa masu garkuwan suka maida hankali kan birin tarayya Abuja.
Dabarun Cin Jarabawar 'JAMB' Cikin Sauki 16.01.2024 14:53
Send us Fan Mail A duk lokacin da ɗalibai ke shirin rubuta jarabawar share fagen shiga jami'a wato JAMB a kan karfafa musu gwiwa gameda dagewa da dabarun da za su sa suyi nasara. Yawanci akan ce ba a cika samun nasarar JAMB a tashin farko ba. To amma akwai wasu dabarun da ya kamata masu shirin jarabawar su bi cikin sauki. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazarin matakan da ya kamata masu shirin r...
Mece Ce Makomar Jam'iyyar APC A Jihar Kano ? 15.01.2024 14:50
Send us Fan Mail Tun bayan hukuncin kotun koli kan zaben gwamnan Jihar Kano da aka yi ranar Juma'a 12 ga Janairun 2024, hankali ya koma kan makomar jam'iyyar APC mai mulki a matakin kasa da ta zamo jam'iyyar hamayya a jihar. Ko mece ce makomar APC a Kano? Shirin Najeriya A Yau na tafe da karin bayani.
Yadda Ake Huce Gajiya Cikin Sauki 12.01.2024 14:54
Send us Fan Mail Mutane da dama na bayyana rashin samun cikakken hutu koda kuwa sun kwashe lokaci mai tsayi suna bacci, wadansu kuma in sun kwanta sai tunani ya mamayesu har baccin ya gagara. Shin wadanne hanyoyi mutum zai bi domin ya ware gajiya? Shirin Najeriya A Yau ya yi nazari kan wannan batu lura da yadda rashin hutu da shan maganin gajiya ke neman zama aláda a tsakanin alúmma.
Anya Bola Ahmed Tinubu Na Duba Makomar Siyasarsa? 11.01.2024 14:41
Send us Fan Mail Daukar matakin ba sani ba sabo da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ke yi ya fara janyo ce-ce-ku-ce dangane da makomar siyasarsa. Shin ko nuna halin ba sani ba sabo da shugaban ke nunawa zai shafi siyasarsa? Shirin Najeriya A Yau ya yi nazari kan wannan batu ta hanyar tattaunawa da ýan kasar na da kuma masana kimiyyar siyasa da sharhi akan alámuran yau da kullum. Domin sauyke...
Makomar Ministar Jinkai Betta Edu Da Shugabar NSIP Halima Shehu 09.01.2024 13:57
Send us Fan Mail Tun bayan dakatar da ministar jin kai ta Najeriya Betta Edu a jiya Litinin 8 ga Janairu da kuma Halima Shehu daga matsayin shugabar hukumar bada tallafin dogaro da kai ta kasa kwanaki 6 tsakani 'yan Najeriya sun fara bin kwakkwafin wane hali su ke ciki, kuma mene ne abin da ya sa aka dakatar da su? Shirin Najeriya A Yau ya binciko cikakken abin da ake zarginsu, ya kuma ji t...
Dabarun kauce Wa Talauci A Watan Janairu 08.01.2024 14:47
Send us Fan Mail Biyo bayan bukukkuwan da ake gudanarwa a karshen shekara musamman a watan Disamba, mutane na fadawa cikin halin yaya zan yi a watan Janairu, sakamakon biyan albashi da wuri da ake yi a watan 12. Shin kun san hanyoyin da zaku bi domin kaucewa mummunan talauci a cikin wannan watan na Janairu? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da karin bayani da shawarwari na musamman,...
Matakan Magance Matsalar Tsaro Kafin 2024 Ta Ƙare 05.01.2024 14:52
Send us Fan Mail Tun bayan da gwamnatin tarayya ta sha alwashin dakile matsalar tsaro kafin shekarar 2024 ta kare, jama’a ke ta diga ayar tambayar kan salon da take shirin bi. Wasu na ganin ba lallai su yarda da kalaman gwamnatin ba. Saidai masana tsaro sun yi hasashen wasu matakai da gwamnatin za ta iya dauka idan har gaske tana son magance matsalar tsaro kafin 2024 ta kare. Shirin Najeriya a Yau...
Yadda Injin Rubutu Na 'Braille' Ke Taimakawa Makafi Cimma Buri 04.01.2024 14:59
Send us Fan Mail Ranar 4 ga watan Junairu ce ranar da Majalisar Dinkun Duniya ta ware albarkacin wane sashe na rayuwar masu lalurar gani a fannin iliminsu Mutane masu lalurar gani suna amfani da wani inji da ake kira ' Braille ' wajen rubutu a madadin allo da alkalami. Yau ita ce ranar da ake kira da 'World Braile day' a turance. Shin ya mahimmancin wannan rana take a garesu,...
Hanyoyin Samun Kuɗi A 2024 02.01.2024 14:26
Send us Fan Mail Sabuwar shekara tana zuwa da sabbin fata daga al’umma musamman ta fannin tattalin arzikinsu. Duba da yanayin matsin tattalin arziki, masu fashin baki na shawartar al’umma da su nemi wasu hanyoyin da za su rika samun kudaden shiga fiye da guda daya ko kuma kaucewa dogaro da albashi kaɗai. Shirij Najeriya a Yau ya duba wasu dabaru da hanyoyin da za ku samu kudaden shiga fiye da daya...
2024: Yadda Za Ku Tafiyar Da Sabuwar Shekara Salim-Alim 01.01.2024 14:00
Send us Fan Mail Shekara sabuwa ba wuya ga mai yawancin rai. Kowacce shekara na zuwa da nata yanayin. Jama'a na da kyakkyawan fata a wannan shekara ta 2024 miladiyya, duk da yake ana cikin yanayi na matsi. Amma ta yaya za ku gudanar da sabuwar shekarar ku salim-alim? Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ya kamata ku saisaita al'amuran yau da kullum domin tafiya bisa tsari.
Dambarwar Siyasar Da Suka Faru A 2023 29.12.2023 15:57
Send us Fan Mail Shekarar 2023 ta kasance cikin zazzafar siyasa da aka gudanar da babban zaben shugaban kasa da gwamnoni. Abubuwa da dama sun faru masu daukar hankali da kuma yadda aka samu sauyin salon siyasa a wasu sassan kasar a shekarar dake karewa. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan wasu mahimman abubuwan da suka faru a fagen siyasa a 2023.
Yadda Aka Sha Fama Da Matsin Tattalin Arziki A 2023 28.12.2023 14:58
Send us Fan Mail Shekarar 2023 ta fara da yanayi na matsin tattalin arziki a lokacin da gwamnati take gab da karewa. Ana sa ran ganin sauyi da zuwan sabuwar gwamnati a fannoni daban-daban da suka shafi tattalin arziki da tsadar rayuwa gami da hauhawar farashi. Shin a wane mizani za a auna tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2023? Shirin Najeriya a Yau ya yi waiwaye da nazarin halin da tattalin ar...
Tsadar Rayuwa: ‘Ba Mu Da Zarafin Bayar Da Kyautar Kirsimeti A Wannan Shekara’ 26.12.2023 13:04
Send us Fan Mail Wannan rana ta washe garin Kirsimeti ce ake kira ‘ Boxing Day’ a turance. Rana ce ta raba kyaututtuka ga ‘yan uwa da abokan arziki. Sai da a yanayin da ake ciki na matsin tattalin arziki, shin al’umma na da zarafin yin kyautuka kamar yadda aka saba? me ya sa ake mata laƙabi da ‘boxing day’, kuma wace irin kyauta ya kamata a bayar? Ku biyo mu cikin shirin Najeriya A Yau domin jin y...
Kirsimeti: "Mun Kasa Zuwa Ko Ina Saboda Tsadar Rayuwa" 25.12.2023 14:01
Send us Fan Mail Bikin kirsimetin wannan shekara ya zo a yanayi na matsin tattalin arziki, amma duk da haka wasu na gudanar da shagali yadda aka saba Ranar 25 ga watan Disambar kowace shekara, mabiya addinin kirista a fadin duniya na gudanar da bikin tunawa da Almasihu, kamar dai yau litinin ta shekarar 2023. Shirin Najeriya A Yau ya duba yadda mutane ke gudanar da bikin kirsimetinsu da yanayin ma...
Dalilin Da Aka Samu Ƙaruwar Masu Taɓin Ƙwaƙwalwa a 2023 22.12.2023 14:45
Send us Fan Mail Yayinda ake gargarar kammala shekarar 2023, abubuwa da dama sun faru da al’umma masu ban sha’awa da ban mamaki. Hukumomi sun ce an samu karin kashi 100 na wadanda aka kai asibiti domin duba lafiyar kwakwalwarsu a shekarar 2023. Shirin Najeriya A Yau ya duba yadda mutane suka tsallake wasu damuwa da kuma abinda masana suke ganin shine ummul haba’isin shigar jama’a cikin dimuwa da r...
Zazzaɓin 'Dengue': Haɗarin Da Ya Kamata Ku Sani Gameda Cutar 21.12.2023 14:50
Send us Fan Mail Hukumar Lafiya ta Duniya ta lissafa zazzaɓin Dengue cikin cutuka masu barazana ga bil'adama a fadin duniya. A 'yan kwanakin Cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce ana zargin sama da mutum 71 sun kamu da cutar zazzaɓin Dengue, yayin da tuni aka tabbatar cewa mutum 13 sun harbu da ita a jihar Sokoto. Shirin Najeriya a Yau ya maida hankali kan matakan d...
Yadda Za Ku Gane Kayan Abinci Marasa Inganci Nan Take 19.12.2023 14:37
Send us Fan Mail Ana yawan cin karo da kayan abinci ko na sha da basu da inganci, kuma ga dukkan alamu sun cika sharuddan sahihanci a ido. Hukumomi na yawan kama darurwan kwalaben kayan sha da ci na jabu ne amma kuma ga su dauke da lambar dake nuna sahihancin su. Akwai masu kirkirar kayan jabu da dama domin shigar da su kasuwa. Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda za ku gane kayyakin da ba su da...
Me Ya Sa Ake Daukar Masu Kwarewar Aiki A Bar Masu Digiri? 18.12.2023 14:55
Send us Fan Mail Jama’a da dama na burin da zarar sun mallaki takardar digiri, za su samu domin sun kammala jami’a. Saidai a yanzu da alama masu daukar aiki suna yawan tallata neman ma’aikata, amma kuma a cikin sharudda za a ce dole sai mai kwarewa a da sanin makamar aiki a fannin. Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa masu daukar aiki suka fi sha’awar masu kwarewa fiye da masu kwalin digiri...
Munanan Cututtukan Da Fitsari A Waje Ke Haifarwa 15.12.2023 12:25
Send us Fan Mail Mutane da dama na fakewa idan sun matsu wajen yin bawali a kan titi, ko gefen wuraren shakatawa. Ko kun san irin cututtukan da yin bawali a fili ke janyowa? Ku saurari shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci dake tafe da karin bayani gameda munanan cututtukan da fitsari a waje ke janyowa.
Matakin Da Zai Sa Farashi Ya Sauka Bayan Ya Ƙaru 14.12.2023 14:28
Send us Fan Mail ‘Yan kasa na kokawa kan yadda farashin komai ke hauhawa yayinda samun al’umma bai cika karuwa ba. Ya riga ya zama al’ada da zarar farashin wani abu a Najeriya ya hau sama, ba lallai ya sauko kasa ba. Shirin Najeriya a yau ya maida hankali kan sauyawar farashi abubuwa a Najeriya da yadda za a dauki matakin dakatar da hakan.
Yadda Ma’aikaciyar Gwamnatin Kano Ta Rasu Saboda Rashin Albashi 12.12.2023 14:51
Send us Fan Mail Tun bayan da gwamnatin jihar Kano tace ta tantance tare da dawo da wasu ma'aikatan da ta dakatar saboda rashin bin ka'ida, suke ta zura ido domin ganin an biya su hakkokinsu. Sai dai a yayin da suke jiran, rayuwarsu ta shiga cikin tasku da halin ni 'yasu ta yadda har aka kai ga rasa rai da wasu kalubale da dama. Shirin Najeriya a Yau ya duba halin da ma'aikatan...
Yadda Ake Rubutun “Project” A Manyan Makarantu 11.12.2023 14:38
Send us Fan Mail Rubutun kundin kammala karatu da ake kira da “project” daya ne daga cikin abin da ke dagula lissafin dalibai a makarantun gaba da sakadire. Mene ne gaskiyar abin da ake bukata a “project”? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe cikakken bayani kan abin da ake bukata a rubutu.
Abin Da Mutumin Da Ya Wuce Shekara 30 Ya Kamata Ya Yi 08.12.2023 14:43
Send us Fan Mail A Jiya Alhamis cikin shirin Najeriya A Yau mun dubi yadda da zarar an ga shekaru sun dan fara ja ana sa ran a cimma wani buri na rayuwa da zai sa a ga cewa mutum ya fara samun cigaba da zama cikakken mutum. Mun yi amfani da shekaru 30. Shin ka saurari wannan shirin da ya yi magana kan Matakin Da Ya Kamata Matashi Ya Kai Kafin Ya Cika Shekara 30? A yau shirin na tafe da shawar...
Wane Mataki Ya Kamata Mutum Ya Kai Kafin Shekara 30 07.12.2023 14:58
Send us Fan Mail Shin kun taba tambayar kanku matsayin da ya kamata matashin da bai wuce shekara 30 ya taka? Da zarar shekaru sun ja ana sa ran a cimma wani buri na rayuwa da zai sa a kalli cewa mutum ya fara samun cigaba da zama cikakken mutum. Shirin Najeriya a Yau ya duba matakin da ya kamata a ce mutum ya kai kafin cika shekara talatin a rayuwa.
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.