Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Yadda Za Ku Mori Rayuwa Kafin Ku Wuce Shekara 30 01.03.2024

Send us Fan Mail A lokacin da matashi ke cikin kuruciya a tsakankanin shekara 30, ana sa ran ya cimma wasu burika a rayuwarsa. Toh amma a wannan yanayi da ake ciki, ta yaya matashi zai iya jin dadin rayuwarsa ta tafi kan tari kafin ya haura 30?   Shirin Najeriya a Yau na tafe da shawarwarin mafita ga wadanda su ka wuce shekaru 30 amma babu kwakkarar madafa. 

Abin Da Zai Sa Farashi Ya Riƙa Sauka Bayan Ya Tashi 29.02.2024

Send us Fan Mail Yan kasa na kokawa kan yadda farashin komai ke hauhawa yayinda samun al’umma bai cika karuwa ba. Ya riga ya zama al’ada da zarar farashin wani abu a Najeriya ya hau sama, ba lallai ya sauko kasa ba. Shirin Najeriya a yau ya maida hankali kan sauyawar farashi abubuwa a Najeriya da yadda za a dauki matakin dakatar da hakan.

Alaƙar Da Ta Rage Tsakanin Ecowas Da Nijar, Mali Da Burkina Faso 27.02.2024

Send us Fan Mail Bayan daukar lokaci ana kai ruwa rana tsakanin ECOWAS da Nijar, Mali da Burkina Faso, daga kashe kamar yadda watakila wasun ku ke da masaniya an janye takunkuman kasashen. Ana ganin cire takunkuman da aka yiwa kasashen dake karkashin mulkin soji zai dawo da ‘yar alakar da ta rage a tsakaninsu duk da yake wasu na ganin shin alaƙa kamar irin ta da za ta ɗore a yanzu? Shirin Najeriya...

Abin Da Yasa Dala Ke Wahalar Da 'Yan Najeriya 26.02.2024

Send us Fan Mail Kusan duk abin da ka yi niyyar saya a Najeriya sai ka ji kuɗinsa ya ninka, idan ka tambayi dalili, sai a ce Dala ta tashi.  Mene ne abin da ya sa Dala ke wahalar da 'yan Najeriya?  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya binciko gaskiyar alaƙar Dala da harkokin kasuwanci a Najeriya.

Tallafin Da 'Yan Najeriya Ke Bukata 23.02.2024

Send us Fan Mail 'Ƴan Najeriya sun samu kansu a yanayi na tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur. Wane tallafi 'ƴan Najeriya suka fi bukata a yanzu? Wasu na bayyana tallafin kayan abinci da Gwamnatin Najeriya ke cewa tana bayarwa ba shine abin da ƴan ƙasar ke buƙata ba.  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya dubi wannan batu. 

Hanyoyin Samun Karin Kudin Shiga Baya Ga Albashi 22.02.2024

Send us Fan Mail A shekarun baya, idan mutum ya samu aikin albashi har murna ake taya shi, dan ana zaton ya kai tudun mun tsira, amma a ýan shekarun nan, masu daukar albashi na cikin wani hali domin kuwa duk karshen wata wani lokaci na biyan bashin da aka ci a tsakiyar watan, wani lokacin ma sai an ciyo wani bashin a iya biyan wani.  Ko kun san akwai wadansu hanyoyi halastattu da mai daukar alabsh...

Yadda Za a Ceto Najeriya Daga Mawuyacin Hali 20.02.2024

Send us Fan Mail Kusan duk wurin da kaga taron 'yan Najeriya sai kaji suna tattaunawa akan matsalolin da suka yi wa ƙasar ɗaurin minti.  Ko waɗanne hanyoyi za a bi domin ceto ƙasar daga mawuyacin halin da ta tsinci kanta?  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe ƙarin bayani 

Hanyoyin Kauce Wa Manyan Cututtuka A Lokacin Zafi 19.02.2024

Send us Fan Mail Lokacin zafi wani yanayi ne da mutane da dama ke bayyanawa a matsayin wanda ke takura musu. Ko kasan akwai waɗansu manyan cututtuka uku da ke yanayin zafi yake haddasawa? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya binciko cututtukan da kuma hanyoyin kauce musu.

Abin da Zai Faru da Tattalin Arzikin Najeriya 16.02.2024

Send us Fan Mail Tsadar rayuwa sakamakon karyewar darajar Naira da tashin farashin Dala, da kuma cire tallafin man fetur na cigaba da gasawa ýan Najeriya aya a hannu.  A tunaninku mene ne zai faru da tattalin arzikin kasar nan idan aka cigaba a haka?  Wani dan kasuwa ya bayyana mana hasashensa, kuma mun ji ta bakin wani masanin tattalin arziki. Ku biyo mu sannu a hankali

Bincike: Yadda Mayanka A Abuja Ke Samar Da Nama Mai Ƙazanta 15.02.2024

Send us Fan Mail Yana da kyau a kowane lokaci mu yi nazarin tsaftar naman da muke ci. Ta iya yiwuwa ba ku taɓa damuwa da sanin yadda ake sarrafa naman dabbobi a mahautu ba. Za ku yi mamakin irin ƙazantar da bincikenmu ya banƙado ana yi da yaɗa cututtukan ga naman da mutane ke siya daga mahautu. Shirin Najeriya a Yau ya maida hankali kan yadda wasu mahauta a birnin tarayya Abuja ke gudanar da aikin...

Yadda Tasirin Rediyo Ya Sauya Al’ummar Duniya 13.02.2024

Send us Fan Mail Ranar 13 ga watan Fabrerun kowace shekara Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar Rediyo ta duniya. Gudummuwar da Rediyo ya kawo ta fi gaban a nanata ga mutanen karkara da na birni. Albarkacin Ranar Rediyo, shirin Najeriya a Yau ya maida hankali kan wasu batutuwa a wannan rana.

Hanyoyin Haɗa Kan 'Yan Najeriya Ta Wasan Ƙwallo 12.02.2024

Send us Fan Mail Faɗin ƙasa da yawan kabilun da ke Najeriya sun sa zaman 'yan ƙasar uwa ɗaya uba ɗaya masu ƙawazucin juna gagara tun samun ƴancin kai.  Ko kun san hanyoyin da ya kamata abi domin haɗa kan ƴan ƙasar wuri guda masu so da ƙaunar juna domin ciyar da ƙasar gaba ta hanyar ƙwallon ƙafa?  Lura da goyon baya da fatan alkhairin da 'yan Najeriya suka nuna wa tawagar ƙwallon ƙafar Na...

AFCON: Yadda Za Ku Kauce Wa Bugun Zuciya Yayin Kallon Kwallo 09.02.2024

Send us Fan Mail Rahotanni sun tabbatar da mutuwar 'yan Najeriya uku sakamakon firgita da suka yi bayan an baiwa kungiyar kwallon kafar kasar bugun da ga kai sai mai tsaron gida yayin wasan su da takwararta ta Afirika ta Kudu.  Mene ne ke sanya zuciya bugawa har ta kai ga ajali ko mummunan jinya? Mun binciko yadda wadannan bayin Allah suka gamu da ajalinsu yayin kallon wasan, mun kuma ji ta b...

Matsalolin Da Ke Damun Arewacin Najeriya 08.02.2024

Send us Fan Mail Labarun da ke fitowa daga Arewacin Najeriya na nuna yadda yankin ya koma baya sakamakon ta'adancin Boko Haram, ýan bindiga masu satar mutane da karbar kudin fansa, ya janyo karuwar  rashin aikin yi da rashin karatu a tsakanin jamaár yankin. Mene ne gaskiyar matsalar wannan yanki? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da masu ruwa da tsaki daga Arewacin Najeriya,...

Yadda Ƙwai Ke Nema Ya Gagari 'Yan Najeriya 06.02.2024

Send us Fan Mail Kwai, daya daga cikin abinci mai gina jiki da ke da arha a da a Najeriya yanzu na shirin fin karfin talaka.  Nawa a ke sayar da kwai a yankin ku?  Kaso 80% cikin 100% na masu harkar kwai a jihar Kano sun bar harkar, wadan da suka rage suna yi sun rage maaikatansu. Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya bi diddigin tsadar kwai a Najeriya. 

Yadda Talakawa Za Su Biya Karin Da Akan Yi Wa Masu Shigo Da Kaya 05.02.2024

Send us Fan Mail Karin da Gwamnatin Najeriya ta yi wa masu karɓar dala domin shigo da kaya a jirgin Kago na ci gaba da shan fassara daga bakin masu ruwa da tsaki.  Ko ka san hanyoyin da manyan 'yan kasuwa za su tatsi kuɗaɗensu daga jikin talakawan ƙasar nan?  Shirin Najeriya A Yau ya dubi wannan batu da idon basira, ya ji ta bakin masu shigo da kaya ta wannan hanyar, ya kuma tattauna da masan...

Da Gaske 'Yan Jarida A Najeriya Na Azuzuta Matsalar Tsaro? 02.02.2024

Send us Fan Mail A lokuta da dama ýan siyasa da masu riƙe da madafun iko na bayyana ayyukan ýan jaridar ƙasar nan a matsayin wani yunkuri na azuzuta matsalar tsaron da ƙasar ke fama da shi, wani lokacin ma cewa su ke yi 'yan jaridar na firgita 'yaan wadansu ƙasashen da ke da niyyar saka hannun jari a Najeriya.  Shin da gaske ne ayyukan 'yan Jarida na azuzuta matsalar tsaron Najeriya...

Abin Da Ya Sa Ba Zan Iya Daina Sa Hijabi Ba 01.02.2024

Send us Fan Mail Zamani ya zo da waɗansu ke yi wa mace mai saka hijabi kallon wacce bata cika ba, ko kuma wacce bata waye ba.  Shin ko har yanzu akwai matan da suka ji suka gani kan sanya hijabi?  Shirin Najeriya A YAU na wannan lokaci ya tattauna da waɗansu fitattun mata da suka yi fice a ilimin zamani amma kuma suna saka hijabi, mun tattauna kan dalilansu, mun kuma ji ta bakin malamai kan yadda...

Yadda Za Ku Danne Fushi Idan Ranku Ya Ɓaci 30.01.2024

Send us Fan Mail Saurin fushi na yawan haifar da da-na-sani musamman ga masu ɗaukar lamari da zafi. Yana da kyau mutum ya iya sarrafa fushinsa a duk lokacin da ya fahimci wani abu na damunsa ko yayin saɓanin fahimta da wani. Shirin Najeriya A Yau ya duba yadda za ku iya sarrafa fushinku.

Yadda Tsadar Rayuwa Tasa Aka Koma Hawa Jaki A Arewa, Kudu Kuma Tafiyar Kafa. 29.01.2024

Send us Fan Mail 'Yan Najeriya na ci-gaba da fito da dabarun rayuwa a halin matsanancin haihuwar farashin da ya samo asali daga cire tallafin man fetur a kasar.  Ko kun san a kwai yankunan da Ar wacin Najeriya suka koma sufuri da jakuna a kudu kuma suka koma tafiyar kafa? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da karin bayani dangane da yadda rayuwa ke cigaba da canzawa a kasar nan. 

Abin Da Ya Kamata Ýan Najeriya Su Tambayi Gwamnatin Tinubu 26.01.2024

Send us Fan Mail Gwamanatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na shan suka kan wasu tsare-tsare da ke takura tattalin arzikin Ýan Najeriya. Baya ga korafe-korafe Ko mene ne abin da ya kamata ýan Najeriya su tambayi wannan gwamnatin ? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya biki jaki ya bigi taiki.

Yadda Wata Mata Ta Haihu A Kofar Gida A Mangu Saboda Yaki Bayan Dokar Hana Fita 25.01.2024

Send us Fan Mail Hukumomi a Jihar Filato sun bayyana saka dokar ta baci sakamakon rikicin kabilanci da ya rikide ya koma na addini a karamara Hukumar Mangu  amma mahara sun ci gaba da kai hare-hare.  Mene ne abin da ya sa har yanzu ba a daina kai hari a Mangu ba?  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya binciko halin da ake ciki. ku biyo mu sannu a hankali. 

Halin Da 'Yan Adawa Ke Ciki A Kano Da Filato 23.01.2024

Send us Fan Mail Jihohin Kano da Filato na hannun jam'iyyun adawa a matakin ƙasa. Tun bayan hukuncin kotun ƙoli ana ta hasashen ya makomarsu za ta kasance. Akwai yiwuwar su iya saita alƙiblar gwamnati idan sun yi  adawa mai ma'ana, yayinda ake sa ran gwamnati ta tafi da kowa. Shirin Najeriya a Yau ya duba halin da 'yan adawa ke ciki a waɗannan jihohi.

Dabaru 10 Na Kaucewa Masu Garkuwa Da Mutane 22.01.2024

Send us Fan Mail A wannan hali da masu garkuwa da mutane ke matsa ƙaimi wurin ayyukan taaddanci da cin zarafin jama'a, shin ka san hanyoyin da ya kamata ka bi domin kaucewa hatsarin gamuwa da su?  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya binciko waɗansu hanyoyi na kaucewa hatsarin gamuwa dasu cikin sauƙi. 

Za A Yi Wa Masu Sayar Da Rake Katin Shaida A Jihar Bauchi 19.01.2024

Send us Fan Mail Rahotanni daga Jihar Bauchi dake Arewa Maso Yammacin Najeriya sun bayyana cewa, gwamnatin jihar za ta yiwa masu sanaár sayar da rake katin shaidar sanaársu.  Ko mene ne ya yi zafi har ake shirin daukar wannan mataki a daidai wannan lokaci?  Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya jiwo ta bakin gwamnatin jihar, dama masu raken.  Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.