Najeriya a Yau

News HA ↓ 958 episodes

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Category

News

Podcast website

www.buzzsprout.com

Latest episode

Jun 23, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Yunwar Wata 9 Ce Ta Sa Mu Yajin Aiki —Likitoci 04.08.2021

Send us Fan Mail A yanzu haka al’amura sun kusan tsayawa cik a asibitocin gwamnati da dama a sassa daban-daban na Najeriya sakamakon yajin aikin likitoci masu neman kwarewa.    Ranar Litinin 2 ga watan Agusta ne dai likitocin suka tsunduma yajin aiki saboda wasu dalilai.     Ku saurari shirin domin jin dalilan liitocin, baya ga yunwar da suka ce sun yi wata tara suna ji.

'Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Alhakin Al'umma Ne' 03.08.2021

Send us Fan Mail Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana 1 zuwa 7 ga watan Agustan kowace shekara  a matsayin Makon Shayar da Jarirai Nonon Uwa na Duniya. Manufar makon ita ce karfafa gwiwar iyaye mata su shayar da jariransu nono, amma taken bikin a bana shi ne "Sahayar da Nonon Uwa Alhaki ne da ya Rataya a Wuyan Kowa". Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari a kan muhimmancin shayar da nonon da k...

Ambaliyar Ruwa: Yadda Wasu Al'ummomi Ke Kokarin Kare Kansu 02.08.2021

Send us Fan Mail Hukumar Nazari da Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa a wasu sassan Najeriya za a samu ruwan sama fiye da yadda aka saba da ma ambaliyar ruwa. Tuni dai aka samu rahoton ambaliyar ta fara barna, inda a wasu wurare ta mamaye gine-gine, ko ta share hanyoyin mota, ko ta tafi da gonaki, ko ma ta yi sanadin mutuwar mutane. A wannan shiri na Najeriya a Yau za mu duba...

Safarar Mutane: Damuwar Duniya Kan Yadda Najeriya Ta Ciri Tuta 30.07.2021

Send us Fan Mail Albarkacin Ranar Yaki da Safarar Mutane ta Duniya, wadda ke fadowa ranar 30 ga watan Yuli, an ja kunnen hukumomin Najeriya da su dauki matakin gaggawa don kawo karshen lamarn.    Hukumar Kula da  Kaurar Jama'a ta Duniya, wadda ta yi kiran, ta ce Najeriya ce kasar da ta fi yawan mutanen da ake safarar su a duniya.

Haramta Wa 'Yan Canji Dala: Abin Da Ka Iya Biyo Baya 29.07.2021

Send us Fan Mail 'Yan canji a Najeriya sun yi korafi. Cewa tun bayan da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da daina sayarwa musu dala farashinta ya fara tashi, harkokinsu kuma na fuskantar barazana. A iya nan abin ya tsaya ko kuwa?  A wannan karon, shirin Najeriya A Yau ya yi duba a kan yadda wannan lamari zai shafi talaka.  

Kwarya-Kwaryar Kasafin Kudin 2021: Wa Zai Amfana? 28.07.2021

Send us Fan Mail Gwamnatin Tarayya ta ce kwarya-kwaryar kasafin kudin 2021 da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu a ranar Litinin zai fara aiki nan take. Shirin Najeriya a Yau ya yi nazara a kan wadanda za su amfana da kasafin na sama da Naira biliyan 900. 

Sabon Salon Karbar Kudin Fansa: Dabara ko Wauta? 27.07.2021

Send us Fan Mail  Wani lamari da ya daure wa 'yan Najeriya da dama kai shi ne labarin yadda wasu masu satar mutane don neman kudin fansa suka bukaci a tura musu kudi ta banki. A wannan shirin, mun yi nazari a kan abin da hakan ke nufi da kuma yanayin barayin mutanen. 

Bullar Cutar Kwalara A Najeriya: Me Ya kamata Ku Yi? 26.07.2021

Send us Fan Mail Daya daga cikin labaran da ke daukar hankali a Najeriya yanzu shi ne na barkewar cutar amai da gudawa a jihohi 18 gami da Yankin Babban Birnin Tarayya, Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da Dr Salihu Ibrahim Kwaifa a kan me ke jawo ta, mene ne alamunta, da kuma yadda ya kamata a tunakare ta.

Listen to the Najeriya a Yau podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.