RFI Hausa
Bakonmu a Yau
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Be sure to visit the podcast's website and support the creator: www.rfi.fr
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Alzubair Abubakar akan makomar ƴan takarar sunayensu ba su fito a kundin INEC ba 15.10.2026 3:24
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya ta ɗauki matsaya ta ƙarshe game da makomar ƴan takarar da ke son a dama da su a zaɓukan gwamnoni a jihohinsu, inda ta tabbatar da cewa waɗanda aka cire daga jerin sunayen da hukumar ta fitar a ranar Asabar da ta gabata sun ciru, muddin su na cikin waɗanda hukuncin kotun ƙoli na watan Satumba ya shafa. A kan haka Michael Kuduson ya gana da masanin doka a Naje...
Dr Kabiru Musa Ƴanɗaki kan shigar da ƴan adawa kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu 14.10.2026 3:38
Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya sake yin kwaskwarima ga kwamitin yaƙin neman zaɓensa, inda a wannan karon aka shigar da wasu gwamnoni da kuma sanatoci na jam’iyyun adawa, lamarin da ke zaman wani sabon abu a siyasar Najeriya. Wasu daga cikin gwamnonin da aka shigar cikin kwamitin yakin neman zaɓen akwai gwamnan jihar Osun, Anambra, Delta sai kuma ministan Abuja da tsohon sanata Ibrahim Dan...
Maniru Nakura kan sassauta haramcin shigo da wasu kayayyaki a Najeriya 13.10.2026 3:32
A cikin shekaru uku da zuwanta kan karagar mulki, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta soke wasu daga cikin tsauraran matakan hana shigar da kayayyaki daga ƙetare zuwa cikin Najeriya, da suka haɗa da shinkafa, tufafi da wasu nau’ukan kayan abinci da dai sauransu. Alhaji Dr Maniru Garba Nakura, shi ne shugaban ƙungiyar ƴan Najeriya mazauna jamhuriyar Benin, ƙasar da wasu ƴankasuwa ke amfani da tashar jir...
Tattaunawa da Emoud Issif kan janye shirin ƙara kuɗin man fetur a Nijar 12.10.2026 3:39
Mahukuntan Jamhuriyar Nijar sun jingine batun ƙara farashin mai, bayan da a can da farko ministan makamashi ya ce gwamnati na kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayo mai daga ƙetare don cike giɓin da ƙasar ke fuskanta. Duk da cewa ana haƙowa da kuma tace shi ne a cikin gida, amma an share makonni da dama ana fama da ƙarancin mai a Nijar. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Emoud Issif, mamba a Majalisa...
Engr Saad Abdullahi kan rashin sanya Arewa cikin aikin sabunta tashoshin jiragen ruwa a Najeriya 08.10.2026 6:33
Yayin da gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shirin sabunta tashoshin jiragen ruwan ƙasar domin inganta ayyukan su, wasu ƴan arewacin ƙasar na zargin cewar ba a yiwa yankin su adalci ba, wajen rashin sanya tashar jiragen ruwa ta Baro cikin aikin, wanda gwamnatin tarayya ce za ta biya. Engr Saad Abdullahi, tsohon jami'in kamfanin mai na ƙasar, wato NNPC ya bayyana damuwa a kan yadda ƴan majalisun are...
Dr Abdulhakeem Garba kan cika shekaru 3 da faro yaƙin Gaza 07.10.2026 3:28
Yau ake cika shekaru uku da harin da mayaƙan Hamas suka kai cikin Isra'ila, lokacin da ake gudanar da bukukuwan Yahudawa a ƙasar, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar Yahudawa sama da dubu ɗaya da ɗari biyu. Sai dai bayan wannan hari, Isra'ila ta maida martani kan Hamas da wasu alƙaluman hukumomi suka ce sama da Falasɗinawa dubu 70 sun rasa ransu a wannan yaƙi cikin shekaru 3. Ku latsa alamar sauti...
Daraktan Amnesty International kan yadda ake tsare ƴan adawa a Najeriya 06.10.2026 3:40
Ƙungiyar Amnesty International ta bayyana damuwa game da yadda ake kama ƴan adawa ana tsarewa a jihar Borno dake Najeriya ba tare da aikata laifuffuka ba. Ƙungiyar ta bayyana matakin a matsayin wani yunkuri na tirsasawa jama’a bayyana ra’ayoyin su da suka saɓa da na hukuma, musamman ganin yadda aka kama wasu matasa 11 aka tsare a gidan yarin Maiduguri, cikin su harda biyar da suka sanya rigar dake...
Kaftin Bakoji kan banbancin kudanci da arewacin Najeriya wajen tunkarar matsalar tsaro 05.10.2026 3:32
Wata matsala da masana tsaro ke tsokaci a kai a Najeriya, shi ne yadda ake samun banbanci tsakanin jihohin Arewacin ƙasar da na kudanci wurin tunkarar ƙalubalen tsaro a yayin da aka samu ibtila’i na garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa ko kuma hare-haren yan ta’adda. Galibi dai jihohin kudancin Najeriya na matsawa gwamnatin tarayya a duk sanda irin wannan lamari ya faru ta yadda take aikewa...
Dakta Kabiru Musa kan yadda Tinubu ya ƙi tabo batun tsaro yayin jawabinsa na ranar ƴanci 02.10.2026 3:35
A Najeriya ana cigaba da tataunawa tareda yin tsokaci a game da jawabin da shugaba Bola Tyinubu ya gabatar a ranar tunawa da samun yancin kai, wato 1 ga watan Oktoba, duba da yadda har ya ƙarƙare jawabin nasa bai kawo wani batu da ya shafi matsalar tsaro da ake fuskanta a akasarin sassan ƙasar ba. Akan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da masanin kimiyyar siyasa, Dakta Kabiru Musa Ƴanɗaki na ja...
Yau Najeriya ke bikin cika sheakru 66 da samun 'yancin kai 01.10.2026 3:11
A wannan rana ta 1 ga watan Oktoba Najeriya na bikin cika shekaru 66 da samun ƴancin kai, bayan share tsawon shekaru ƙarƙashin mulkin mallakar Turawan Ingila. Abubawa da dama ne suka faru a Najeriya a cikin waɗannan shekaru, da suka haɗa da na cigaba da kuma na asha, yayin da wasu ke ganin cewa ya kamata a ce ƙasar ta zarta inda take a yau ta kowanne fanni. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da s...
Ko janyewar dakarun Amurka sama da 4,000 a ƙasar Iraƙi nasara ce ga Iran? 30.09.2026 3:36
Amurka ta sanar da shirin janye sojojinta daga sansanoninsu na ƙarshe a Iraƙi zuwa ranar Laraba, matakin da Iran da ƙawayenta ke ɗauka a matsayin wata nasara, a ƙasar da sojojin Amurka 4,500 suka mutu cikin sama da shekaru 20 na yaƙi. Ana ganin wannan a matsayin wata nasara ga ƙasar Iraƙi da ƙawayenta, ganin yadda ficewar sojojin Amurkan ke cikin sharuddan da Iran ta gindaya kafin dakatar da yakin...
Tattaunawa da Malam Nazifi Alaramma kan shata iyakar Najeriya da Kamaru 29.09.2026 3:37
Shugaban hukumar kula da iyakokin Najeriya Adamu Adaji, ya ce ƙasar na dab da kammala aikin shata iyakarta da Kamaru, bayan kwashe kusan shekaru 24 da kotun duniya ta ICJ ta yanke hukuncin mallaka yankin Bakassi ga Kamaru. A yayin wata zantawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Abuja, ya ce a yanzu abinda ya yi saura a aikin bai wuce kafa tubali 260 a ɓangaren jihar Adamawa ba...
Tattaunawa da Rabi'u Kwankwaso kan iƙirarin Atiku na dawo da tallafin man fetur 28.09.2026 3:27
A kwanakin baya ne tsohon shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugabancin ƙasar a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC mai adawa, Atiku Abubakar ya sha alwashin maido da tallafin mai idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasar, lamarin da ya janyo tattaunawa a tsakanin ƴan Najeriya a yayin da a gefe guda ya kaɗa hantar gwamnati mai ci. Akan batun tallafin ne Michael Kuduson ya gana da dan takaran mataim...
Ambasada Suleiman Ɗahiru akan taron Majalisar Ɗinkin Duniya 24.09.2026 3:39
An shiga rana ta uku a ci gaba da gudanar da Babban Taron Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, wanda ke matsayin dama ga illahirn shugabannin ƙasashe don gabatar da jawabai kan batutuwan da suka shafi duniya. To sai dai tun a ranar farko da aka buɗe wannan zama, shugaban Amurka Donald Trump ya fito fili inda ya yi fatali da wasu batutuwa da suka shafi ƙasa da ƙasa. Abdoulkarim Ibrahim Shikal...
Alhaji Shehu Ashaka kan yadda lamura ke tafiya bayan buga kugen siyasa 23.09.2026 2:53
A Najeriya, yayin da jama’a ke ci gaba da kokawa dangane da rashin tsaro da kuma tsadar rayuwa, a nasu ɓangare kuwa ƴan siyasa waɗanda ke da alhakin tafiyar da lamurran jama’a da kuma samar da tsaro, sun duƙufa ne ta fannin yaƙin neman zaɓe. Bashir Ibrahim Idris ya zanta da Alhaji Shehu Ashaka, ɗaya daga cikin dattijai a yankin Arewacin Najeriya, domin jin yadda yake kallon makomar alaƙa tsakanin...
Aissami Mahamadou kan dalilin Amurka na zuba jari a sashen Uranium ɗin Nijar 22.09.2026 3:32
Ana ci gaba da ɗiga ayar tambaya a game da dalilan da suka sa Amurka ta amince ta bai wa kamfanin Global Atomic Corporation na ƙasar Canada dala million 414 don gaggauta zuba jarin haƙo makamashin uranium a jamhuriyar Nijar, duk da cewa alaƙa ta yi rauni tsakanin mahukuntan birnin Yamai da na Washington tun bayan kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya a ƙarƙashin Mohamed Bazoum. A game da wannan batu n...
Ƙungiyoyi sun yunƙura don tabbatar da adalci ga matasan da suka mutu a jihar Neja 21.09.2026 3:41
A Najeriya, ƙungiyoyi masu zaman kansu sun yunƙuro domin tabbatar da cewa an gudanar da bincike tare da hukunta masu hannu wajen mutuwar matasa aƙalla 37 lokacin da suke tsare a hannun jami’an tsaro n Civil Defense a jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar, lamarin da ya yi matuƙar tayar da hankula. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Comrade Abubakar Abdullahi, shugaban ƙungiyar Human Freedom Internat...
Muhd Ladan kan dakatar da samar da takardun kuɗin bai ɗaya da BRICS suka yi 18.09.2026 3:36
Ƙasashe mambobin Ƙungiyar BRICS da suka gudanar da taronsu na shekarar bana a ranakun 12 da kuma 13 ga wannan wata na Satumba, sun yanke shawarar dakatar da shirinsu na samar da takardar kuɗin bai ɗaya, domin kawo ƙarshen amfanin da Dalar Amurka a tsakaninsu. Domin jin dalilin ɗaukar wannan mataki da kuma sabuwar dabarar da suka runguma, Nura Ado Suleiman ya tattauna da mai magana da yawun ƙungiya...
Hamza Idris kan yadda ƴan Jarida a Najeriya da sassan Afrika ke fuskantar barazana 17.09.2026 3:35
Ƙungiyar Editocin kafafen yaɗa Labaran Najeriya ta koka kan ƙaruwar yadda jami’an tsaro ke cin zarafi da kuma take hakkin da ‘Yan Jarida, matsalolin da ka iya daƙile ‘yancin manema labarai. Cikin sanarwar da ta fitar bayan ganawa a Kano, ƙungiyar Editocin Najeriyar ta buƙaci kawo ƙarshen yadda ake fakewa da wasu dokoki ciki har da na hukunta laifukan da suka shafi Intanet, wajen yin barazana ga ay...
Dr Kabiru Adamu kan ƙara yawan makaman da Najeriya ta sayo daga ƙetare 16.09.2026 3:25
Wani rahoton hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS ya nuna cewar, yawan makaman da gwamnatin ƙasar ke sayowa daga ƙetare da zummar inganta tsaro a ƙasar ya ƙaru da kaso 104, inda ta kashe Naira biliyan 55 a cikin watanni shidda na farkon wannan shekara, idan aka kwatanta da abinda aka kashe wajen sayen makaman a shekarar bara. Tuni dai masana da sauran ƴan Najeriya suka fara bayyana ra’ayoyi mabanbant...
Souleyman Yahaya kan tasirin al'ummar Hausawa a ƙasar Togo 15.09.2026 3:32
Hausawa a ƙasar Togo kamar dai a sauran ƙasashe, sun gudanar da bukukuwan ranar Hausa ta duniya, inda suka yi amfani da wannan damar don tattauna al’adu da kuma tasirin wannan al’umma a cikin wannan ƙasar da ke Yamancin Afirka. Abdoulaye Issa ya zanta da Souleyman Yahaya, shugaban cibiyar yaɗa al’adu da kuma kare muradun Hausawa a Togo, wanda ya yi masa ƙarin bayani a game da yanayin zamantakewars...
Alhaji Ibrahim Muhammad kan yadda shirin samar da ɗan takarar adawa ɗaya a Najeriya ya rushe 14.09.2026 3:37
Hukumar Zaɓen Najeriya ta fitar da jerin sunayen mutane 18 da suka cancanci tsayawa takarar shugabancin ƙasar da mataimakansu, sai kuma wasu mutane dubu 4 da 860 da za su tsaya takarar neman kujerun Majalisun Tarayya a zaɓen da za a yi shekara mai zuwa. Wannan dai na nuni da cewa yunƙurin ƴan adawa na fitar da ɗantakarar ɗaya tilo don tunkarar jam’iyyar mai mulki ya ci tura. Abdoulkarim Ibrahim Sh...
An naɗa sabon kwamandan da zai jagoranci yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci a Najeriya 11.09.2026 3:29
A Najeriya an naɗa sabon kwamandan da zai jagoranci yaƙin da ake da ƙungiyoyin ta’addancin na ISWAP da Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar, lamarin da ke nuni da cewa an maye gurbin wanda ke jagorantar wannan runduna ƙasa da shekaru biyu bayan naɗa shi kenan. Shin wanan sauyi ya dace da halin da ake ciki na yaƙi da ta’addanci ko kuma dai kawai garambawul ne da aka saba yi? Akan haka ne Michae...
Kamilu Sani Fagge kan tsanantar rikici a Gabas ta tsakiya 10.09.2026 3:27
Rikicin Gabas ta Tsakiya da ya tsananta tsakanin Amurka da Iran na cigaba da faɗaɗa, inda a ‘yan kwanakin nan ya kai ga sake tayar da rikicin Yemen tsakanin gwamnatin ƙasar da Saudiya ke marawa baya, da kuma ‘Yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran, ɓangarorin da zuwa yanzu suka rasa mayaƙa fiye da 500. Baya ga datse mashigin ruwan Hormuz, a halin yanzu rikicin na Gabas ta Tsakiya ya shafi...
Hon Sama’ila Mohammed kan saida hannun jarin matatar man Dangote 09.09.2026 3:33
A ranar Litinin da ta gabata, matatar man fetur ta Ɗangote ta dasa ɗambar shirinta na shiga kasuwar hada-hadar hannayen jari, waɗanda shugaban rukunin kamfanonin na Ɗangote, Alhaji Aliko, ya ce ana iya mallakar aƙalla guda 10 da ƙasa da Naira dubu 6. Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Honorable Sama’ila Mohammed, masanin tattalin arziƙi a Najeriya, wanda ya yi tsokaci kan tasiri da kuma y...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.