RFI Hausa
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalin’ariziki, al’adu da dai sauransu…
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwan mabanbanta 10.07.2026 10:58
Kamar yadda aka saba, yau rana ce da sashen Hausa na RFI ke bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga tsaro, siyasa, tattalin arziƙi da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan buƙatar majalisa na a dakatar da afuwa ga ƴan ta'adda 09.07.2026 10:38
Majalisar dattijan Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar da ta dakatar da shirin yin afuwa ko kuma sauya ɗabi’un tubabbun ƴan ta’adda a wani yunƙuri na dawo da su cikin al’umma, wanda ta ce ba ya taimakawa ƙoƙarin da ƙasar ke yi wajen yaƙi da ta’addancin da ya yi mata katutu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyi kan ziyarar da wakilan Vatican suka kai wa Sarkin Musulmin Najeriya 08.07.2026 10:52
Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Muhammadu Sa’ad Abubakar na uku, ya ce mutunta addinan juna, daina furta kalaman ƙiyayya ko tsatsauran ra’ayi, abubuwa ne da za su iya taimakawa ta fannin kyautata zamantakewa a tsakanin al’umma. Wannan dai gargaɗi ne da ke ƙunshe a sanarwar da aka fitar bayan ganawar da aka yi a babban masallacin birnin Abuja tsakanin mai alfarma Sarkin Musulmin da kuma tawaga...
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta 03.07.2026 9:19
Yau juma'a, kamar yadda aka saba, rana ce da sashen Hausa na RFI ke bai wa masu sauraro damar faɗin albarkacin bakin su kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga tsaro, tattalin arziƙi, siyasa, da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
Ra'ayoyin masu sauraro kan ambaliyar da ta afkawa ƙasashen gaɓar ruwan teku a Afrika 02.07.2026 9:59
Birane da dama da ke gaɓar ruwan tekun ƙasashen Yammacin Afrika sun fuskanci ambaliyar ruwa wadda ta haddasa asarar rayuka da kuma salwatar dukiyoyi masu tarin yawa. Birnin Accra na ƙasar Ghana da Abidjan Ivory Coast, a can ne aka samu asarar rayuka, yayin ambaliyar ta haddasa ɓarna ga gidaje da kadarori a biranen Lagos, Cotonou, Lome da sauransu. Lura da abin da ya faru a waɗannan birane da kuma...
Ra'ayoyin masu sauraro kan ci gaba da zanga-zangar ƙyamar baƙi a Afrika ta Kudu 01.07.2026 9:30
Bayan cikar wa’adin ranar 30 ga watan jiya da suka bai wa ƴan-ci rani don ficewa daga ƙasar, daga ƙarshe dai masu adawa da zaman baƙi a Afirka ta Kudu sun ƙaddamar da zanga-zangar neman ala dole sai sun fice daga ƙasar. Masu tarzomar dai na kallon ƴan asalin ƙasashen ƙetare a matsayin waɗanda suka mamaye gurabobin aiki, lamarin da ya jefe ɗimbin Ƴan Afirka ta Kudu cikin yanayin zaman kashe wando....
Ra'ayoyin masu sauraro kan tsadar mai duk da faɗuwar farashinsa a duniya 30.06.2026 10:16
Duk da cewa an samu faɗuwar farashin ɗanyan man fetur a kasuwar duniya sakamakon sulhun tsakanin Amurka da Iran, amma har yanzu ana ci gaba da fama da tsadar wannan makamashi a mafi yawan ƙasashen duniya. A Najeriya tuni Hukumar kare masu amfani da kayan masarufi ta ƙasar ta yi gargaɗin cewa ko dai dillalan mai su karya farashi ko kuma ta ɗauki matakan ladaftarwa a kansu. Latsa alamar sauti don sa...
Ra'ayoyin masu sauraro kan rawar ƙasashen Afrika a Gasar Kofin Duniya 29.06.2026 9:36
Ƙasashen Afrika 9 daga cikin 10 da ke halartar gasar cin kofin duniya ne suka samu nasarar tsallakawa zuwa zagayen ƙasashen 32 na wannan gasa da ke gudana a ƙasashen Amurka da Canada da kuma Mexico. Wannan dai shi ke matsayin babban tagomashi da nahiyar ta Afrika ta taɓa samu a irin wannan gasa ta cin kofin duniya. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta 26.06.2026 10:49
Yau juma'a kamar yadda aka saba, rana ce da sashen Hausa na RFI ke bai wa masu sauraro damar faɗin albarkacin bakinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga siyasa, tsaro, tattalin arziƙi, zamantakewa da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
Ra'ayoyin masu sauraro kan yadda matsalar tsaro ke kawo tarnaƙi ga manoma 24.06.2026 11:02
Yayin da damina ta fara kankama a Tarayyar Najeriya, wani abu da ake fargaba shi ne yadda matsalar tsaro ke iya haddasa tarnaki ga aikin gona hatta ma a wannan shekara. Kusan a kowace rana za a samu labarin cewa an kai hare-hare kan manoma da kan yi sanadiyyar kisa, yin garkuwa domin neman kuɗin fansa, yayin da a wasu lokuta ake tilasta wa manoman biyan haraji kafin ba su damar shiga gonakinsu. La...
Ra'ayoyin masu sauraro kan ƙaryata zargin kisan Kiristoci da MDD ta yi 23.06.2026 10:06
Tawagar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tura zuwa Najeriya don gudanar da bincike a game da zargin kisa, yin garkuwa da mutane da kuma tilasta wa wasu barin muhallansu saboda dalilai na addini, ta ce wannan ba gaskiya ba ne. Jagorar tawagar Farfesa Nazila Ghanea, a ƙarshen ziyarar gani da ido ta kai a ƙasar, ta ce mutane na yin waɗannan zarge-zarge ne saboda gazawar gwamnati wajen ba su kariya da ku...
Ra'ayoyin masu sauraro kan taƙaddamar ƴan siyasa a kotunan Najeriya 18.06.2026 10:10
Yayin da ake shirin gudanar da zaɓuka cikin watan Fabarairun shekaru mai zuwa a Najeriya, wani abu da ke faruwa shi ne taƙaddamar ƴan siyasa a gaban kotunan ƙasar. Kusan a kowane mako, za a ji cewa kotu ta yanke hukunci kan jam’iyyun siyasa, lamarin da ke iya nisantar da su daga tsayawa takara a waɗannan zaɓuka. Wannan ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti...
Ra'ayoyin masu sauraro kan ganawar shugabannin Nijar da Benin 03.06.2026 9:12
Nijar da Jamhuriyar Benin sun amince da yin aiki a tare don yaƙi da ta’addanci da ke addabar ƙasashen biyu na Yammacin Afirka, yayin da a hannu ɗaya suka kafa wani kwamitin da zai bayar da shawarwari cikin kwanaki 15 a game da yadda za a sake buɗe iyakokin ƙasashen da ke rufe yau kusan shekaru uku. An dai cimma wannan matsaya ce a ziyarar da shugaban Benin Romuald Wadagni ya kai a birnin Yamai...
Saƙon gaisuwar sallah daga masu bibiyar shafin RFI 27.05.2026 10:33
A yau take Sallah Babba! Ranar da ɗaukacin Musulmi a faɗin duniya ke murnar zagayowar Sallar layya. Wannan biki na zuwa ne a daidai lokacin da lamura suka yi tsauri, musamman ta ɓangaren tattalin arziƙi. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta 21.05.2026 10:00
Kamar yadda aka saba a kowace ranar alhamis, shirin Rayuwata na bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan maudu'an da shirin ya tattauna a wannan mako. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan yarjejeniyar Nijar da kamfanin ƙasar China 20.05.2026 10:04
Bayan share kusan shekara ɗaya ana taƙaddama tsakanin gwamnatin Nijar da kamfanin mai na CNPCN na ƙasar China, ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniya da ke bai wa Nijar damar ƙarin jari da kuma faɗa-a-ji a harkar man fetur. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan giɓin kuɗaɗe da WHO ke fuskanta 19.05.2026 10:15
Yanzu haka ƙasashe masu tasowa na ci gaba da ƙoƙarin cike giɓin da aka samu bayan da Donald Trump ya janyewa tallafin da Amurka ke bai wa Hukumar Lafiya don yaƙi da wasu curutuka a duniya. A jawabinsa gaban Taron Hukumar Lafiya WHO da ke a birnin Geneva, shugaban Ghana John Dramani Mahama ya ce ya kamata Afirka ta samar da tsarin kula da lafiyar al’ummarta a maimakon barin lamarin a hannun hukumar...
Ra'ayoyin masu sauraro kan ƙara yawan jihohi a Nijar 14.05.2026 10:24
Gwamnatin Nijar ta fitar da wani daftari da ke ƙara adadin jihohi zuwa 19 ta hanyar ƙirƙiro sabbin 11 a maimakon 8 da ake da su a kasar yau kusan shekaru 30 kenan. Gwamnatin ta ce za ta ƙirƙiri sabbin jihohi da kuma gundumomi ne domin samar da ci gaba da ta hanyar ƙara matso da jama’a zuwa kusa da hukuma. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti d...
Ra'ayoyin masu sauraro kan taron Afrika da Faransa da aka kammala a Kenya 13.05.2026 10:42
A taron Afirka da Faransa da aka kammala jiya talata a ƙasar Kenya, Faransa ta sanar da shirin saka jarin Euro bilyan 23 don ƙarfafa kasuwanci tsakanin ɓangarorin biyu. Shugaba Emmanuel Macron ne ya sanar da haka, yana mai cewa daga yanzu ɓangarorin biyu za su gudanar da mu’amala ce irin ta ba ni gishiri in ba ka manda a maimakon bai Afirka tallafi kamar yadda ake yi a baya. Latsa alamar sauti don...
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta 08.05.2026 10:00
Yau juma'a sashen Hausa na RFI na bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga fannin siyasa, tattalin arziƙi, tsaro, da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
Nijar ta bayar da umarnin garƙame masallatai bayan kammala sallar farilla 05.05.2026 10:08
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayar da umarnin garƙame masallatai, da zarar an kammala sallolin farilla, tare da tabbatar da cewa an hana jama’a kwana a wuraren ibada ciki har da makarantun Islamiyya. Tuni ministan cikin gida ya sanar da gwamnoni, shugabannin ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya matakin a hukumance, saboda dalilai na tsaro. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan ranar ƴancin aikin jarida ta duniya 04.05.2026 10:43
Rahoton shekara-shekara da ƙungiyar kare ƴan jarida ta Reporters Without Borders ta fitar, na nuni da cewa an samu gagarumin koma-baya ta fannin ƴancin aikin yaɗa labarai a cikin ƙasashe 100 daga cikin 180 na duniya. RSF ta fitar da rahoton ne a jajibirin ranar ƴancin aikin jarida da ake gudanarwa ranar 3 ga watan Mayun kowace shekara. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'aoyin Masu Saurare na ranar Jumma'a 1 ga watan Mayun 2026 01.05.2026 10:34
A kowace ranar Jumma'a filin ra'ayoyin 'Masu Sauraro kan bada damar tsokaci kan bututuwa da ke ci wa mai sauraro tuwo a kwarya. Ku latsa alamar sautin domin jin wasu daga cikin ra'ayoyin da wasu masu sauraro suka aiko mana.
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.