RFI Hausa

Muhallinka Rayuwarka

News HA ↓ 24 episodes

Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

Author

RFI Hausa

Category

News

Podcast website

www.rfi.fr

Latest episode

Jun 20, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Matsalar ambaliyar ruwa da kan dagula lamuran al’uma a Najeriya 20.06.2026

Kamar kowace shekara, a bana ma ana hasashen samun ambaliyar ruwa a wasu ƙasashen yammacin Afrika, inda akan samu rasa rayuka da dukiya mai tarin yawa. A Najeriya, an sha samun hasarar rayuka a sanadin matsalar ambaliyar ruwan, da kan rutsa da wasu yankunan ƙasar.

Masana na ci gaba da tsoratar da al'umma game da illolin da ke tattare da gurɓatacciyar iska 13.06.2026

A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan tasirin gurɓatacciyar iska ga lafiyar halittu da muhalli wato air pollution a turance. Iska na gurɓa ta ne ta hanyoyi da dama, kama daga hayaƙin na’urori wato injina a masana'antu, zuwa tarkacen bola ko kuma ƙone wasu abubuwa, wanda su ke kawo cikas ga yanayin muhalli tare kuma da kawo tazgaro ga lafiyar ɗan Adam.

Kananan manoma a Najeriya na nan kan tsarin noma na kaka da Kakanni 06.06.2026

A yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan yadda har yanzu, kananan manoma a Nigeria na nan kan tsarin noma na Kaka da Kakanni, lamarin da ake gani yana hana ruwa gudu wajen tabbatar da cimma burin kasar na kasancewa mai dogaro da-kai a fannin samun wadatar abinci.

Yawaitar takin jabu ya zamewa Manoman Najeriya ƙalubale a bana 23.05.2026

Shirin 'Muhallinka Rayuwarka na wannan makon, ya tattauna ne da masu ruwa da tsaki kan sha'anin Noma, a kan matsalar yawaitar taki da kuma magungunan ƙwari na jabu, matsalar da ta zamewa manoman Najeriya ƙalubale babba a shekarar bana.

Sauyin Yanayi ya jefa Manoma cikin ruɗani kan lokacin da ya dace su fara shuka 16.05.2026

Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna na a kan yadda samun saukar Ruwan Sama na farko a bana ya jefa manoma a jihohin Arewacin Najeriya cikin ruɗani dangane da lokacin da ya dace su fara shuka. Wannan na zuwa ne a yayin da hukumar hasashen Yanayi ta Najeriya wato NIMET, da uma wasu masana ke gargaɗi game da yiwuwar ɗaukewar ruwan saman da wuri, lamarin da zai yi janyo tafka hasar...

Yadda saukar ruwan sama na farko ya jefa manoma cikin ruɗani 09.05.2026

A yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan yadda Ruwan sama na farko da aka samu a baya-bayan nan ya jefa manoma a jihohin Arewacin Najeriya cikin ruɗani da fargaba, yayin da hukumar hasashen yanayi ta ƙasa, NiMet, da masana ke gargaɗi game da tsagaitawar ruwan saman da wuri wanda zai iya lalata duk wani amfani da aka yi a wannan lokaci.

Matsalar karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar iyalai a sassan Nigeria 02.05.2026

Matsalar nan ta karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar miliyoyin iyalai a sassan Nigeria, kila ko saboda rashin samun damar jan ruwan famfo a gidajensu, ko kuma rashin samun ruwan daga hukumomin samar da ruwan famfo na jihohinsu, duk da makudan kudin da gwamnatocin jihohin ke warewa, da sunan samar da ruwa wa jama’arsu. Wannan matsala ba kawai ta tsaya kan iyalai da kan rasa ruwan amfan...

Karfafa gwiwa ga jama'a su koma noma a jamhuriyar Nijar 25.04.2026

Shirin muhallinka rayuwarka na wannan mako zai maida hankali ne kan yanda ake karfafa gwiwa ga jama'a su koma noma don ita ce babbar hanyar dogaro da kai ta fuskar abinci. Tun bayan halin matsin da jama'ar Jamhuriyar Nijar suka shiga biyo bayan juyin milkin soja da ta haddasa karamcin da tsadar abinci a cikin kasar aka rika zaburar da mutane su kama aikin noma musamman abincin da aka shigo da shi...

Matasan kasashe 11 da ke cikin tsarin shingen kare Hamada suka kai rangadi a Nijar 19.04.2026

A yau shirin zai leka jamhuriyar Nijar ne inda matasa daga kasashe 11 da ke cikin tsarin shingen kare Hamada da zaizayewar kasa don mayar da yankin tsanwa suka kai rangadi a Nijar musaman a Jihohi 5 na kasar da suka hada da Tillaberi Niamey, Dosso, Maradi da Zinder don duba irin cigaban da Nijar ta samu a wannan fannin da nufin kwaikwayonsa don kaddamar da shi a kasashensu.

Dalilan da suka sanya Manoma Albasa a Nijar fuskantar ƙalubale a bana 14.04.2026

Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon, ya yi tattaki zuwa Jamhuriyar Nijar, inda aka fuskanci ƙalubale kan noman Albasa a shekarar bana. Bayanai daga ƙasar ta Nijar na cewa a halin da ake ciki, Manoma da dama sun shiga halin ƙaƙa-ni-kayi saboda rashin samun kuɗaɗen shiga, la'akari da irin rawar da noman na Albasa ke taka wa wajen sama musu abin kashewa.

Yadda sare itace a Nijar ke haifar da koma baya wajen samun amfanin gona 04.04.2026

Shirin, ‘Muhallinka Rayuwarka a wannan makon ya yi duba ne kan yadda ake samu canjin yanayi ta hanyar saran icen "Gawo" barkatai daga Makiyaya da su kansu Manoman, wanda ake ganin ke haifar da koma baya wajen samun yalawar abinci kamar, bakamar yadda aka saba ba a shekarun baya a cikin gonaki na Jamhuriyar Nijar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson..........

Hukumar NIMET ta yi hasashen samun saukar ruwa da wuri a daminar bana a Najeriya 14.03.2026

Shirin ‘Muhalinka Rayuwarka’ a wannan makon ya yaɗa zango ne a Tarayyar Najeriya, inda ya mayar da hankali kan hasashen ruwan sama da Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya NIMET ta yi, gabanin kamawar daminar bana, inda ta bayyana cewa damina za ta sauka da wuri a jihohi irin su Kano da Niger da Rivers da wasu jihohi 12 na ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kud...

Yadda cutar tumatiri ta kasara manoma a wasu jihohin arewacin Najeriya 31.01.2026

Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ tare da Michael Kuduson a wanan  mako ya yi duba kan  wata mummunar cutar tumatiri da ake kira Tuta Absoluta ko kuma cuta mai karya garkuwar tumatir. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....

Dalilan da masana suka ce su ke ƙara bayyana sauyin yanayi 11.01.2026

Shirin muhallinka rayuwarka na wannan makon ya tattauna ne  kan yadda sauyin yanayi ko dai na zafi ko na sanyi ko kuma damina ke bayyana ƙarara, musamman a yankin yammacin Afirka. Ga misali a Najeriya, ɗaya daga cikin sauye-sauyen yanayin da aka shaida shi ne rashin hunturu a shekarar  bana, musamman a Yankin arewacin ƙasar, inda aka saba ganin kankamar Yanayin na sanyin mai tsanani daga ƙarshen w...

Noman rani na fuskanta barazana a Najeriya sabida tsadar kayan noma irinsu taki 13.12.2025

Shirin, ‘Muhallinka Rayuwarka’ a wannan makon ya yaɗa zango ne Tarayyar Najeriya, inda ya duba irin barazanar da  noman rani ke fuskanta, musamman a wannan lokaci da farashin kayyakin gona suka faɗi warwas a yayin da farashin taki da sauran mahimman kayakin da ake amfaani da su wajen noman suke a can ƙololuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Michael Kuduson..........

Yadda manoman Jamhuriyar Nijar ke fama da ɓarnar makiyaya a ƙarshen damina 29.11.2025

Shirin muhallinka rayuwarka na wannan karon zai mayar da hankali ne kan irin fama da ake sha a karshen damina tsakanin manoman da suke tattarar Kayan gona da makiyayan dake dawowa daga kiwo zuwa wuraren da ake aikin noman a  wasu sasaan Jamhuriyar Nijar. A duk karshen damana makiyayan da suka tafi mashekari wurin kiwon dabbobinsu inda ke da isassar ciyawa nesa da gonaki na sabkowa wuraren da ake a...

Abubakar Ibrahim kan taron sauyin yanayi na COP30 da ke gudana a Brazil 15.11.2025

An buɗe taron Majalisar Dinkin Duniya a kan sauyin yanayi da ake kira COP 30 a Brazil inda masana muhalli da sauyin yanayi daga kasashen duniya za su mayar da hankali da kuma samar da dabaru kan sauyin yanayi. Za'a kwashe makwanni biyu ana gudanar da wannan taro wanda zai mayar da hankali a kan ci gaba ko akasin haka da aka samu a kan wannan matsala.

Yadda wani ruwa da ke ɓulɓulowa ta ƙasa ke zubar da gidaje da kashe bishiyu a Nijar 08.11.2025

Shirin muhallinka rayuwarka na wannan yau zai maida hankalin ne kan wani ruwan dake bullowa daga kasa Wanda ya yi sanadiyar zubewar gidaje da kashe bishiyoyi da ga gurbata hanyoyi a unguwar Garin Malam ta Damagaram a Jamhuriyar Nijar. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.

Barazanar wutar daji da ke lakume gonakai a Jamhuriyar Nijar 01.11.2025

A cikin wannan shirin ,za mu leko Jamhuriyar Nijar inda a duk shekara ake fuskantar barazanar wutar daji da ke lakume gonakai da cimaka. Hukumomin Nijar sun dau matakai domin kawo karshen  wannan al'amari da manoma da kuma jama'a ke kuka  a kai.

Yadda manoma suka karkata akalar noman barkono bana a Najeriya 25.10.2025

Shirin wannan makon zai tare ne a jihar Kano dake Tarayyar Najeriya, inda aka samu manoma da dama a wasu yankuna da suka duƙufa wajen noman barkono a wannan shekarar. Ba shakka sun yi aiki tuƙuru, kuma haƙarsu ta cimma ruwa duba da ɗimbim barkono da suka girba. Wannan lamari dai ya tayar da hankalin waɗannan manoma, waɗanda sun sauya alƙibla ne saboda ganin yadda farashin amfanin gona dangin hatsi...

Masana game da fallen da ke bai wa ɗan Adam kariya daga sinadaran hasken rana 19.10.2025

A wannan makon, shirin zai mayar da hankali ne akan wani rahoton da masana suka fitar, wanda ke nuna cewa fallen nan ko shimfidar da ke bai wa ɗan Adam kariya daga wasu sinadaran hasken rana masu haɗari, da ake kira Ozone Layer, wanda kafin yanzu ake bayyana damuwa a game da lalacewar da ya fara yi, sakamakon ayyukan da ɗan Adam ke aiwatarwa ya fara gyaruwa. Sai ku biyo mu domin za mu tattaunawa d...

Alfanun cibiyar bunƙasa noma a jihar Kano ga ci gaban samar da abinci a Najeriya 11.10.2025

Shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Michael Kuduson a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda aka samar da wata katafariyar cibiyar bunƙasa harkokin noman Damuna dana Rani ga al'ummar jihar Kano wadda aka samar a garin Kadawa da ke ƙaramar hukuamr Garin Malam. bayanai sun ce wannan cibiyar bunƙasa noma na ƙunshe da tarin kayakin buƙata a lokacin noman walau na rani ko kuma na damuna duk dai a ƙo...

Yadda manoma a Jahuriyar Nijar suka koma noman Gyaɗa da Gujiya gadan-gadan 27.09.2025

Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda manoma a Nijar suka koma noman Gyaɗa da riɗi gadan-gadan bayan sun yi watsi da shi tsawon shekaru, saboda matsaloli da noman ke fuskanta. Maraɗi ce kan gaba a noma Gyada ko Gujiya shekaru aru aru, sai Zinder da kuma Doso, waɗanda suka taimaka wajan hada-hadar kasuwancin Gyaɗa har a Kano inda ake tattara Dalar Gyadar. Yaw...

Ƙorafin makiyaya a Jigawa kan yadda ake saida filayen kiwo 20.09.2025

Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ a wannan makon ya mayar da hankali ne kan wata matsala da ta kunno kai tsakanin makiyaya da manoma a yankin ƙananan hukuomin Guri da Kiri Kasamma da kuma Kaugama na jihar Jigawa a Arewacin Najeriya, inda Fulani makiyaya suka koka kan yadda aka salwantar da wuraren kiwon dabbobinsu da wurin shayar da su. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michae...

Listen to the Muhallinka Rayuwarka podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.