RFI Hausa

Mu Zagaya Duniya

News HA ↓ 24 episodes

Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.

Author

RFI Hausa

Category

News

Podcast website

www.rfi.fr

Latest episode

Jul 11, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Faɗa ya sake ɓarkewa tsakanin Amurka da Iran bayan rugujewar yarjejeniya 11.07.2026

Shirin a wannan makon zai leka Gabas ta Tsakiya inda rikici ya sake barkewa tsakanin Amurka da Iran abin da ya kawo karshen yarjejeniyar fahimtar juna ta watanni uku da suka cimma a tsakaninsu. Bayan nan, shirin zai taɓo wasu mahimman lammuran da suka wakana a sassan yammacin nahiyar Afirka, musamman Najeriya, Nijar da Kamaru.

Bitar muhimman labarun da suka faru a mako daga Rfi hausa 04.07.2026

Ƙungiyar kare hakin bil Adam Amnesty International ta zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu da gaza kare ƴan Najeriya daga matsalolin ta’addanci da na tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya.........

Ana ci gaba da laluben dubban mutanen da suka ɓata a girgizar kasa a Venezuela 27.06.2026

Shirin na wannan mako zai soma ne daga Venezuela inda a yammacin ranar laraba girgiza ƙasa mai karfin maki 7 a ma’aunin celcius ta afkawa arewa maso yammacin ƙasar abin da ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali da alhini sakamakon rasa rayuka da dukiyoyi. Alkaluman hukumomi sun ce sama da mutum 900 ne suka rasayukansu kawo yanzu yayin da sama da 4,000 suka jikkata bayaga sama da 50,000 da suka yi ɓa...

Shirin yayi bita kan harin da aka kai filin jirgin saman Yamai da ma wasu labarai 20.06.2026

Shirin na wannan mako ya mayar da hankali kan bitar muhimman labaran da suka faru a sassan duniya cikin makon da muke bankwana da shi. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Oumarou Sanni.

Shirin ya fara da yadda aka buɗe bikin gasar cin kofin duniya a ƙasar Mexico 13.06.2026

Ranar Alhamis 11 ga wannan watan  aka yi  bikin buɗe gasar cin kofin duniya karo na 23, gasar da itace karo na farko da ƙasashe 3, Amurka da Canada da kuma Mexico su ka karbi baƙunci, sai dai kuma an gudanar da zanga-zanga a wasu sassa na birnin ƙasar. Ƙasashe 48 ne ke fafata domin samun zakaran bana kuma yan wasa 1,248 da alkalan wasa 52 za su jagoranci wasanni 104 da za'a kwashe kwanaki 39 ana y...

Yadda malaman makaranta suka gudanar da zanga-zanga kan rashin tsaro a Najeriya 06.06.2026

Shirin na wannan mako ya waiwaya halin da duniya ke ciki a fannin tsaro, rikice-rikice da kuma Diflomasiyya

Mahajjata kusan miliyan biyu sun gudanar da aikin Hajjin bana 30.05.2026

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Oumarou Sani, kamaar yadda aka saba ya yi bitar wasu daga cikin muhimman lamurran da suka wakana a makon da muka yi wa bankwana. Daga cikin muhimman batutuwan kuma akwai, yadda Musulmi kusan miliyan biyu suka samu nasarar gudanar da aikin Hajjin bana. Shirin ya kuma leƙa Yankin Gabas ta Tsakiya domin jin halin da ake ciki, musamman kan ƙoƙarin kawo...

RFI Hausa ta cika shekaru 19 da fara watsa labarai cikin harsshen Hausa 23.05.2026

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya fara ne da labarin cikar wannan tasha ta RFI Hausa shekaru 19 da kafuwa.  Ranar alhamis 21 ga wannan watan gidan Rediyonku na RFI sashen Hausa ya cika shekara daya- daya har 19 da soma yada shirye-shiryensa . A shekara 2007 ne kwarrariyar ƴar Jarida Lanni Smith ta kirkiri sashen Hausa na RFI da aka yi wa matsuguni a birnin Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya. Kuma...

Yadda harin dakarun Najeriya ya kashe ɗimbin mutane a kasuwar Zurmi 16.05.2026

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' yana bita ne na mahimman labaran al'amura  da suka wakana a makon da ya gabata. a wannan makon shirin ya soma ne daga Najeriya inda a farkon makon da ya wuce wani harin da dakarun Najeriya suka kai ta sama a kasuwar Tumfa ta karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamafara ya hallaka akalla mutum dari 100 tare da jikkata wasu da dama. Wannan harin da ke zaman mafi muni da dakarun...

Wasu daga cikin muhimman labaru a cikin makon daya gabata 09.05.2026

A wannan mako shirin zai mayar da hankali akan batun zabukan fidda gwani na Jam'iyar APC mai mulki a Najeriya da kuma rikicin cikin gida a sauran jam'iyun ƙasar suka ɗauki hankulan al'uma.

Yadda haɗakar ƙungiyoyi suka ƙaddamar da farmaki a sassan Mali 02.05.2026

Shirin ya soma daga ƙasar Mali inda a ranar 25 ga watan Afrilun da mu kayi ban kwana haɗakar mayakan Abzinawa na FLA da na ƙungiya masu ikirarin jihadi ta  JNIM suka ƙaddamar da mugayen hare-hare a garuruwa huɗu na ƙasar da suka haɗa da Sevare, Kidal, Gao da kuma  Kati. A garin Kati da ke zaman babban sansanin sojin ƙasar ƴan bindigar sun yi amfani da motoci shake da bama-bamai da manyan bindigogi...

Shirin mu zagaya duniya ya tattaro manyan labaran da suka faru a wannan mako 25.04.2026

Shirin mu zagaya duniya na wannan mako ya duba manyan labaran da suka faru cikin wannan mako, a sassan duniya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Oumarou Sani.

Makomar masu shiga tsakani,kan neman ƙulla yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran 18.04.2026

Mecece makomar ƙoƙari da masu shiga tsakanin, musamman Pakistan ke yi a kan neman ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran duba da tsaurin wasu ko da dama daga cikin sharuɗɗan da ɓangarorin biyu suka gabatarwa juna? Nura Ado Suleiman ke  yi muku barka da sake haɗuwa cikin shirin Duniyarmu a Yau

Bitar Labaran mako: Iran ta amince da buɗe mashigin Hormuz ga jiragen kasuwanci 18.04.2026

Shirin Mu zagaya duniya tare da Oumarou Sani, kamar yadda ya ke zuwar muku a kowannen mako, a wannan karon ma ya yi bita ne kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke ban kwana da shi. Cikin jerin labaran da ke ƙunshe a wannan shiri, akwai yadda Iran ta amince da buɗe mashigin Hormuz bayan ƙulla yarjejeniyar tsagaita wutar kwanaki 10 tsakanin Isra'ila da Lebanon. Wannan da sauran manyan lab...

An cimma yarjejeniyar tsagaita wutar makwanni 2 tsakanin Amurka da Iran 11.04.2026

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' tare da Oumaru Sani, ya yi bitar wasu daga cikin muhimman labaru kan lamurran da suka wakana a makon da muka yi wa bankwana, daga cikinsu kuma akwai yarjejeniyar tsagaita wutar kwanaki 14 da aka cimma tsakanin Amurka da Iran, bayan da ƙasar Pakistan ta shiga tsakani.

Rikicin Gabas ta Tsakkiya: Dakarun Amurka sama da 2000 sun isa yankin 04.04.2026

Shirin mu na yau ya fara yadda zango a yankin Gabas ta Tsakiya inda rikicin Amurka da Isra’ila kan Iran ke cigaba da tsananta duk da tayin shiga tsakani da wasu kasashen Larabawa su ka faro karshen mako a Pakistan  da zummar kawo karshen rikicin da tuni ya kasara tattalin arzikin duniya. A cikin ranakun ƙarshen mako kamfanin dilancin labaran Reuters ya bayyana cewa sojojin Amurkan dubu 2 da 500 su...

Wane hali ake ciki game da yaƙin Gabas ta tsakiya 28.03.2026

Shirin Mu zagaya Duniya na wannan rana ya mayar da hankali kan yakin Gabas ta tsakiya da halin da yanayin tsaro ke ciki a Najeriya da sauran manyan labaran da suka faru a sassan duniya cikin wannan mako. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Oumarou Sanni.

Yadda rikicin Iran ke faɗaɗa a yankin Gabas ta Tsakiya 07.03.2026

A Wanan makon shirin zai karkata alakarsa ne yankin Gabas ta Tsakiya inda sabon rikici ya barke tsakanin hadakar Amurka da Isra’ila da kuma Iran. A cikin shirin zamu yi duba dangane da yadda rikicin  ke cigaba da faɗaɗa zuwa sauran kasashen yankin da ma  tasirinsa kan bangarori daban-daban a  wanan duniyar sai a gyara zama domin sauraron cikakakken shirin.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci Pakistan da Afghanistan su kai zuciya nesa 28.02.2026

Shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan mako tare da Oumarou Sani ya mayar da hankali kan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka bankwana da shi, masamman kan ƙazancewar rikici tsakanin Afghanistan da Pakistan, bayan da Pakistan ta ƙaddamar da harin Operation Ghazab lil-Haq a matsayin martani ga hare-haren da tace Taliban ta kai wa sojojinta, da kuma dambarwar Amurka da Iran kan yarjejeniya...

Sanya hannu kan dokar zaɓe da Tinubu ya yi ta bar baya da ƙura 21.02.2026

Shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan mako tare da Oumarou Sani kamar ya mayar da hankali kan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka bankwana da shi, masamman kan dambarwar da ta biyo bayan sa hannun da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yiwa dokar zaɓen ƙasar, da kuma mummunar gobarar da aka samu a kasuwar Singa da ke jihar Kano. Haka nan shirin ya yi bitar hukuncin ɗaurin rai da rai...

Harin Kwara da dambarwar Nukiliyar Iran na cikin manyan labaran makon da ya gabata 07.02.2026

Shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan mako tare da Oumar Sani kamar kullum ya mayar da hankali kan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka bankwana da shi, masamman harin da ya kashe sama da mutane 170 a jihar Kwara dake arewacin Najeriya. 

Ƙungiyar IS ta dau alhakin harin da aka kai filin tashin da saukar jirage na Diori Hamani a Nijar 31.01.2026

A daren Laraba zuwa wayewar ranar Alhamis, filin jirgin saman Diori Hamani na Yamai da ke jamhuriyar Nijar ya fuskanci wani hari na ɗan lokaci daga wasu mayaka na ƙungiyar IS. Gwamnatin sojin Nijar, tare da taimakon sojojin Rasha,ta murkushe maharan. A yanzu haka,jiragen sama sun ci gaba da zirga-zirga, a cewar hukumar da ke kula da harkokin sufurin jiragen sama na ƙasar.

Kisan mutane 7 ƴan gida ɗaya ya tayar da hankalin jama'a a Kano 25.01.2026

Daga cikin abubuwan da Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan  mako ya yi duba akai har da batun kisan Fatima Abubakar da ƴaƴanta 6 a Unguwar Ɗorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin......

Aƙalla mutane 5000 ake fargabar sun mutu a zanga-zangar Iran 17.01.2026

Mahukuntan Iran sun yi barzanar amfani da hukuncin kisa kan masu zanga-zangar wadda ta juye zuwa tarzoma inda ofishin babban mai shigar da ƙara na gwamnati ya ce akwai yiwuwar idan aka fara ɗaukar wannan mataki a samu sassaucin zanga-zangar. A nasa bangare shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar daukar mataki mai tsauri kan Iran muddun hukumomin ƙasar suka fara kashe masu  zanga-zangar tsadar...

Listen to the Mu Zagaya Duniya podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.