RFI Hausa

Dandalin Fasahar Fina-finai

News HA ↓ 24 episodes

Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayar wa ma su sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya  bai wa wasu ta fanin shirya fim ko tsara wasan kwaikwayo. Wanda ke zo maku a duk ranar Asabar da safe, tare da maimaici a ranar Lahadi da yamma.

Author

RFI Hausa

Category

News

Podcast website

www.rfi.fr

Latest episode

Jul 11, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 5M+ downloads · 4.8 rating iOS soon

Episodes

Manyan labaran da suka wakana a wannan mako a duniyar fina-finai 11.07.2026

A cikin shirin na wannan rana zamu zagaya da ku masana’antun shirya fina-finai don tsamo muku manyan labaran da suka wakana a wannan mako. Akwai mu da yadda aka fitar da jerin fina-finan da suka fi jan hankalin ƴan kallo a watanni 6 na wannan shekara daga ƙasar India. Muna tafe da yadda muhawara ta barke a shafukan sada zumunta, kan yadda jarumai daga jihar Plateau suka mamaye Kanywood, yayin da a...

Tattaunawa ta musamman da mashiryin Fina-finai Abdul Amart 20.06.2026

A cikin shirin na wannan mako za ku ji mu ɗauke da tattaunawa ta musamman da mashiryin Fina-finai Abdul Amart. Muna tafe da batu kan fina-finan da aka fi tafka muhawara akan su cikin mako da muke bankwana da shi. Akwai mu da tattaunawa da Dauda Kahutu Rarara, wanda ya ballo sabuwar Dambarwa da mawaƙi Davido, da kuma yadda yake ganin wakokinsa na siyasa ka iya tasiri a zabe mai zuwa.

Karancin ingantaccen labarin fina-finai, lamarin da ke karya darajar su a Najeriya 16.11.2024

A cikin shirin na wannan mako a bangaren mu na Kannywood zamu duba yadda karancin ingantaccen labarin fina-finai, lamarin da ke karya darajar fina-finan. Za ku ji mu tafe da dambarwar da ta kunno kai tsakanin fitaccen mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara, da hukumar tace fina-finai ta jijar Kano.

Korafe-korafen makallata fina-finan Hausa 13.07.2024

A cikin shirin na wannan mako, zamu sake yin waiwaye kan korafe-korafen makallata fina-finan Hausa, kan yadda mashirya fina-finai suka fi mayar da hankali kan soyayya, tare da fatali da sauran fannonin rayuwa. Za mu tsallaka Jamhuriyar Nijar, inda zamu duba yadda zamani yayi tafiyar ruwa da wake-waken ‘yan mata da ke tashe a baya. Muna tafe da tattaunawa da Hadiza Gire, guda daga cikin matan da su...

Ko ana 'kan ta waye' a masana'antar Kannywood? 06.02.2022

Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' ya yi nazari ne a kan al'amarin nan da ake kira 'kan-ta-waye'. Shirin ya yi  bayani a kan menene 'kan-ta-waye', sannan ya tattauna da baki, wadanda suka fadada bayanin don fahimtar mai sauraro.

Rayuwar mata masu shirya fina-finai a Nollywood a Najeriya 30.01.2022

A cikin wannan shirin na dandalin fasahar Fina-finai,Hawa Kabir ta samun tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Duniyar fina-finai dangane da makomar mata musaman a gidajen mazan su,ko wandada ke da niyar yin aure.

Halin da masana'antar Fim ta shiga a makon da ya kare 09.01.2022

Kamar yadda aka saba kowane mako shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai tare da Hauwa Kabeer ya tattauna akan wasu daga cikin muhimman al'amuran da ke wakana a masana'antar fina-fina da ke arewaci da kuma kudancin Najeriya.

Abinda ya wakana cikin kungiyar MOPAN a baya bayan nan 19.12.2021

Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon tare da Hauwa Kabeer, ya leka kungiyar MOPAN ne domin jin wainar da ake toyawa.

An kamala zaben wakilan kungiyar yan Fim a jihar Kaduna 12.12.2021

A cikin shirin duniyar fina-finai,Hawa Kabir ta samu tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harakar fim yan lokuta bayan kamala zaben wakilan MOPAN a jihar Kaduna. Makomar duniyar Fim,hanyoyin kawo karshen baraka a wannan duniya na daga cikin manyan batutuwa da Hawa ta samu tattaunawa da bakin na ta.

Fitaccen makawaki ya sha alwashin daukar nauyin tallafawa mata da sana'o'i 05.12.2021

Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon tare da Hauwa Kabeer ya tattauna da wani fitaccen mawakin Hausa da ya sha alwashin daukar nauyin tallafawa mata da sana'o'i.

An fara daukar shirin 'Gidan Badamasi' zango na 4 21.11.2021

Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai ya leka inda ake daukar shirin barkwancin nan mai dogon zango, wato 'Gidan Badamasi', inda ya gana da jarumai da masu ruwa da tsaki a shirin, cikin su har da babban daraktan shirin, Falalu Dorayi.

Rayuwar Alhaji Umaru Danjuma Katsina da aka fi sani da Kasagi 07.11.2021

Kasagi wanda ya rubuta fitaccen littafin da aka yi wa suna ‘Kulba na Barna’ ya rasu ne sakamakon gajeruwar rashin rashin lafiya. Danjuma Katsina na daya daga cikin fitattun masu wasan kwaikwayon da suka yi suna daga shekarar 1980 tare da wasu abokan aikin sa a lokacin irin su Kasimu Yero da Tumbuleke da Malam Mamman da karkuzu Na Bodara da kuma Samanja Mazan Fama. Hawa Kabir a cikin shirin dandali...

Masu ruwa da tsaki kan rubutun adabi da fina-finai na alhinin rasa Kasagi 31.10.2021

Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon tare da Hauwa Kabir ya tattauna na masu ruwa da tsaki kan rubutun adabin Hausa da kuma fina finai kan rasuwar marigayi Umaru Danjuma Katsina da aka fi sani da Kasagi.

Taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa 2/2 24.10.2021

Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai tare da Hauwa Kabir ya cigaba da tattaunawa ne kan taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa na kungiyar WTC da ya gudana a garin Zaria, dake jihar Kaduna.

Taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa 03.10.2021

A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai, hauwa Kabir ta leka taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa na kungiyar WTC  da ya gudana a Zaria, jihar Kaduna. Shirin ya gana da shehunan malaman da suka halarci taron. 

Rayuwar yan wasan fina-finai a Tarrayar Najeriya 26.09.2021

A cikin shirin dandalin Fina-finai,Hawa Kabir ta jiyo ta bakin  masu shirya fim a Nollywood,wanda suka kuma yi mata bayyana dangane da rayuwar su da kuma irin wasannin da suke iya kasancewa a cikin su ga baki daya.

Gudunmawar Ahmad Aliyu Tage ga masana'antar Kannywood 19.09.2021

Shirin dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon ya tattauna kan rashin da masana'antar Kannywood tayi na wasu manyan jaruman ta, musamman Ahmad Aliyu Tage da ya rasu a makon da ya gabata.

Ta'aziyyar mawakin siyasa Isyaku Forest 12.09.2021

Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai' na wannan mako tare da Hauwa Kabir ya kawo mana ta'aziyyar mawakin siyasan nan, Isyaku Forest, wanda ya rasu kwanan nan. Hauwa Kabir ta tattauna da makusanta da aminansa, ciki har da shahararren mawakin siyasa, Rarara.

Dalilan da suka haifar da koma baya ga kasuwar fina-finan Hausa 05.09.2021

Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon ya tattauna da masu ruwa da tsaki kan dalilan da suka janyo faduwar kasuwa fina-finan Hausa.

Mutane na yi wa fim kallon hadarin kaji don ba su ke yi ba - Isa Bello Ja 29.08.2021

A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa kabir ta kawo abubuwa da dama a bangaren fina-finai, inda ta duba yadda yanzu masana'antar Kannywood ke gogayya da takwararta tav kudancin Najeriya. Ta kuma tattauna da shugaban jaruman Kannywood, Alhassan Kwale wanda ya ce Umma Shehu da Sadiya Haruna ba 'yan Kannywood bane.

Tattaunawa da Yaya Dankwambo na shirin gidan Badamasi 22.08.2021

Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon tare da Hauwa Kabeer ya tattauna da Muhammadu Nura Yakubu da a yanzu aka fi sani da sunan Yaya Dankwambo na shirin fim din Gidan Badamasi.

Tattaunawa da Tijjani Asase (Damisa) kan masana'antar Kannywood 15.08.2021

Shirin Dandalin Fasahar Fina Finai ya tattauna da Tijjani Asase da aka fi sani da Damisa kan lamurran da suka shafi masana'antar Kannywood.

Ana shirin ci gaban fim din Hausa na 'Malam Zalimu' 25.07.2021

A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa Kabir ta duba tattauna da Ado Ahmed Gidan Dabino a game da ci gaban shirin fim din Malam Zalimu. Bayan nan ta leka Nollywood ta kudancin Najeriya, inda ta kawo ta'aziyar rasuwar shahararren mawaki, Sound Sultan.

Masu shirya Fina finan Hausa sun koma cin moriyar Youtube 18.07.2021

A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa Kabir ta yi dubi da batun kasuwanci a masana'antar Kannywood, tare da duba yadda masu shirya fim din suka koma intanet, ta wajen cin moriyar dandalin Youtube, inda suke dora ayyukansu a kai.

Listen to the Dandalin Fasahar Fina-finai podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.