RFI Hausa
Kasuwanci
Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.
Koniecznie odwiedź stronę podcastu i wesprzyj twórcę: www.rfi.fr
Gdzie słuchać?
Podcasty w aplikacji Replaio Radio Już wkrótcePodcasty trafią do aplikacji już wkrótce. Zainstaluj teraz i jako pierwszy zobacz nowe podejście do podcastów
Odcinki
Rashin rassan bankuna ya tilastawa al'ummar karkara rungumar POS a Najeriya 08.07.2026 9:57
Shirin kasuwa akai miki dole dake bibiyar harkokin kasuwanci da tattalin arziki na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ci gabar fasahar zamani da aka samu a fannonin haɗar-haɗur ƙudi a Najeriya, ke shafar al’ummomi a yankunan ƙarƙara.
Ana samun ƙaruwar cin bashin kuɗin kiran waya tsakanin jama'ar Najeriya 01.07.2026 10:15
Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan Najeriya suka rungumi ɗaukar bashin kiran waya, wanda wani rahoto ya ce, a bara kaɗai anci bashin kiran waya da ƙudinsu ya kai Naira Tiriliyan 4 da biliyan 61. Wasu bayanai da cibiyar fintech firms Optasia mai tattara alƙaluman shige da ficen kuɗaɗen layukan sadarwa ta fitar a baya-bayan nan, ya...
Yadda tattalin arzikin Ghana ke haɓɓaka sannu a hankali 17.06.2026 9:45
Yau shirin ya mayar da hankali ne dangane yadda tattalin arzikin ƙasar Ghana ke ci gaba da ɓunƙasa sannu a hankali. Ku danna alamar sauraro domin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.
Koken ƴan Najeriya kan yadda bankuna ke zare musu kuɗi daga asusun ajiyarsu 20.05.2026 10:32
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan yadda ƴan Najeriya, ke nuna fushinsu dangane da zargin cire musu kuɗi ba bisa ka’ida ba daga asusun bankunansu. Miliyoyin 'yan Najeriya da yanzu haka ke fuskantar hauhawan farashin kayayyaki da kuɗin sufuri, da kuma rashin tabbas ga makomarsu a fannin tattalin arziki, caje-caje da dama da bankuna ke yi a asusun ajiyars...
Yadda ƴan kasuwa a Najeriya suka jingine harakokinsu saboda tsadar sufuri 13.05.2026 10:30
Shirin Kasuwa akai miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......
Yadda tsadar sufuri ya tilastawa 'yan kasuwa jingine sana'o'insu a Najeriya 13.05.2026 10:30
A yau shirin ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Sannu a hankali, irin hada-hadar da aka saba gani tsakanin mafi yawan kasuwannin Nigeria na neman zama abun tarihi, sakamakon yadda ‘yan kasuwa masu tarin yawa suka jingine harkokinsu na kasuwanci saboda tsad...
Damarmaki da kuma ƙalubalen da manoman Albasa a arewacin Kamaru ke fuskanta 29.04.2026 9:59
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon, ya duba ƙalubale da kuma damammaki a ɓangaren noman albasa a arewacin Kamaru. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.
Matakan da bankin CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗi a Najeriya 22.04.2026 10:04
Shirin Kasuwa akai miki doke na wannan mako ya yi duba ne kan matakan da babban bankin Najeriya CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗaɗe, domin rage hauhawan farashin kayayyaki a kasuwanni da kuma daga darajar kuɗin ƙasar wato Naira, ta hanyar rage kuɗaɗe da ke yawo a hannun jama’a. Babban Bankin Nigeria, ya fito da bakin alƙalamin adadin kuɗaɗen da ke bankuna da waɗanda ake hada-hada d...
Yadda matsalolin tsaro ke kassara kasuwanci a arewacin Najeriya 08.04.2026 10:00
Shirin na wannan makon ya mayar da hankali ne kan irin fargabar da 'yan kasuwar arewacin Najeriya da ke fatauncin kayayyaki zuwa wasu sassan jihohi ke ciki, sakamakon ayyukan bata gari da ke tare hanya wanda a wasu lokuta kan kai ga rasa rayuka. Abune da aka saba gani, ‘yan kasuwar dake hada Hada tsakankin jihohi daga wannan kasuwa zuwa waccan ko tsakanin kasuwannin kauyuka. To sai dai Kuma irin w...
Yadda matasa ke fatan cin gajiyar yarjejeniyar tattalin arziki tsakanin Nijar da Algeria 01.04.2026 9:56
Matasa a Agadez da ke arewacin Jamhuriyar Nijar na cike da fatan cin moriyar sabuwar dangatakar da aka kyautata tsakanin kasar da makwabciyarsu Aljeriya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.
Koma bayan da kasuwancin duniya ya fuskanta sakamakon rikicin Gabas Ta Tsakiya 18.03.2026 10:18
Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" tare da Ahmed Abba a wannan mako ya ɗora ne kan inda ya tsaya a makon jiya, game da gagarumin koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arziki da duniya ke fuskanta masamman a bangaren makamashi, sakamakon yaƙin da kawancen Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran, da kuma martinin jamhuriyar musuluncin kan Isra’ila da muradun Amurka a kasashen labarawa suka janyo. A...
Yadda yaƙin Iran ya haifar da koma baya ga tattalin arzikin Duniya 11.03.2026 9:56
A yau shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan mako tare da Ahmad Abba ya mayar da hankali ne a kan yadda Yaƙin da kawancen Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran, da hare-haren mayar da martini na jamhuriyar musuluncin kan yahudun Isra’ila da muradun Amurka a kasashen labarawa suka janyo gagarumar koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arzikin duniya masamman a bangaren makamashi. Ku latsa...
Yadda aka gudanar da taron tattalin arzikin a Akwa Ibom 04.03.2026 9:53
Shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan taron taron tattalin arziki da ya gudana a farkon watan Fabarairun da ya gabata a jihar Akwa Ibom da ke kudancin Najeriya. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
Najeriya da China sun yi bukin cika shekaru 55 da hulɗar diflomasiyya 18.02.2026 17:27
Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan tasirin tattalin arziki dangane da alaƙar China da Najeriya da a makon jiya aka yi bikin cika shekaru 55 da faro hulɗar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu. Najeriya da China sun sake jaddada karfafa dangantakar diflomasiyya da ke tsakaninsu yayin da kasashen biyu ke bikin cika shekaru 55 da fara huldar di...
Yadda buɗe iyakokin Najeriya da Nijar zai taimaka wajen haɓaka kasuwanci 11.02.2026 10:00
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan wani sabon yunkuri na kara inganta alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar inda hukumar kwastom a jamhuriyar Nijar tayi tattaki zuwa Najeriya don tattaunawa hanyoyin da za’a bi don saukaka hada-hadar kayayyaki tsakanin kasashen biyu. Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam na Najeriya Adewale Adeniyi, ya sake jaddada an...
Yadda gwamnatin jihar Yobe ta duƙufa wajan gina kasuwannin zamani 04.02.2026 9:54
Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan gina kasuwanni na zamani da Gwamnatin Jihar Yobe ta sake ginawa a wasu sassan jihar domin karfafa harkokin kasuwanci da suka fuskanci koma baya, saboda matsaloli na Boko Haram. Shiga alamar sauti domin sauraron karin bayani.......
Yadda aka ƙulla yarjejeniyar kasuwanci mafi girma a duniya tsakanin India da EU 28.01.2026 10:01
Yau shirin ya mayar da hankali ne dangane gagarumar yarjejeniyar cinikayya mafi girma da ba’a taba ganin irinta ba, da aka cimma tsakanin ƙungiyar Tarayyar Turain ƙasar India. Yarjejeniyar da aka cimma yayin ziyarar da shugabannin Turai suka kai New Delhi na ƙasar India, za ta bada damar kasuwanci mara shinge tsakanin ƙasashe mambobin EU 27 da kuma ƙasar da ta fi yawan jama'a a duniya, waɗanda suk...
Mahangar masana kan kiran IMF da bankin Duniya ga Najeriya don sauƙaƙa tsadar rayuwa 21.01.2026 10:07
Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole"na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan sabbin kiraye-kirayen da Bankin Duniya da kuma Asusun bada Lamuni na Duniya (IMF) suka yi ga gwamnatin Najeriya wajen ganin ta ɗauki matakab da suka kamata don ƙara rage hauhawar farashin kayayyaki domin al’umma ta amfana a zahiri da kuma ci gaban tattalin arziki ƙasar. Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Ƙ...
Yadda Najeriya ta yi iƙirarin rarar tiriliyan 12 a watanni 6 farkon 2025 14.01.2026 10:23
Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya mayar da hankali kan ikirarin gwamnatn Najeriya na samun rarar kuɗi da ya kai tiriliyan 12 kuma kashi 21 daga ciki ta same su ne daga bangarorin da ba na man fetur ba a cikinn watanni 6 na farkon shekarar 2025. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Tasirin kama shugaba Maduro na Venezuela ga tattalin arzikin duniya 07.01.2026 10:30
Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya tattauna da masana da sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin man fetir dangane da tasirin kama shugaban ƙasar Venezuela Nicolas Maduro da Amurka ta yi zai yi ga tattalin arzikin duniya.
Hangen masana tattalin arziƙi kan sabon harajin gwamnatin Najeriya 24.12.2025 10:07
Shirin "Duniya Akai Miki Dole" tare da Faruk Muhammad Yabo a wannan mako ya yi duba ne kan sabbin harajin da gwamnatin Najeriya ke shirin karɓa a hannun jama'ar ƙasar, a wani yanayi da ƙasar ke fatan tattara wani ɓangare na kuɗaɗen tafiyar da harkokinta. Shirin a wannan mako ci gaba ne na makon da ya gabata dangane da wannan dokar haraji wadda al'ummar Najeriya ke ci gaba da suka akanta. A cikin s...
Abubuwan da sabon tsarin harajin Najeriya ya ƙunsa 17.12.2025 10:07
A wannan mako shirin zai tattauna ne kan sabuwar dokar harajin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanya wa hannu, wadda kamar yadda na ambata ba da jimawa, za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan gobe na shekara mai zuwa. Tun a watan Yunin da ya gabata shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar harajin da ake sa ran za ta sauya fasalin tsarin karɓa da tattara kuɗaɗen shiga ga gwamnati daga...
Al'ummar Nijar sun rungumi tsarin hada hadar kuɗi ta manhajar waya 10.12.2025 10:04
Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda a shekarun baya bayan nan, hada hadar kuɗi ke neman yin ƙaura daga bankuna zuwa manhajojin wayar salula da ake kira da Mobile Money a Turance, da ake amfani da tsarin wajen aikewa da kuɗi ko karɓarsu a ciki da wajen ƙasar ta Nijar. Samun damar aika kuɗaɗe ta hanyar amfani da manhajojin wayar hannu ba tare da yankar ku...
Yan Najeriya na yawaba Hasetins kan kafa kamfanin ma'adanai mafi girma a Afirka 03.12.2025 10:06
Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan gina katafaren kamfanin tono da kuma sarrafa ƙarafu da duwatsu masu daraja da wani matashi ya ƙaddamar a jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya, irinsa mafi girma a Afirka, wanda zai laƙume dalar Amurka miliyan 400.
Podobne podcasty
Replaio nie jest wydawcą podcastów; nazwy audycji, okładki i audio należą do ich autorów i są rozpowszechniane przez publiczne kanały RSS