RFI Hausa

Bakonmu a Yau

News HA ↓ 47 episodi

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Visita il sito del podcast e sostieni chi lo crea: www.rfi.fr

Autore

RFI Hausa

Categoria

News

Sito del podcast

www.rfi.fr

Ultimo episodio

1 ott 2026

Dove ascoltare?

I podcast nell'app Replaio Radio In arrivo

I podcast stanno per arrivare nell'app. Installala ora e scopri per primo un modo tutto nuovo di vivere i podcast

Scaricala su Google Play Installala gratis Android quasi 10 mln di download · valutazione 4,8 iOS in arrivo

Episodi

Yau Najeriya ke bikin cika sheakru 66 da samun 'yancin kai 01.10.2026

A wannan rana ta 1 ga watan Oktoba Najeriya na bikin cika shekaru 66 da samun ƴancin kai, bayan share tsawon shekaru ƙarƙashin mulkin mallakar Turawan Ingila. Abubawa da dama ne suka faru a Najeriya a cikin waɗannan shekaru, da suka haɗa da na cigaba da kuma na asha, yayin da wasu ke ganin cewa ya kamata a ce ƙasar ta zarta inda take a yau ta kowanne fanni. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da s...

Ko janyewar dakarun Amurka sama da 4,000 a ƙasar Iraƙi nasara ce ga Iran? 30.09.2026

Amurka ta sanar da shirin janye sojojinta daga sansanoninsu na ƙarshe a Iraƙi zuwa ranar Laraba, matakin da Iran da ƙawayenta ke ɗauka a matsayin wata nasara, a ƙasar da sojojin Amurka 4,500 suka mutu cikin sama da shekaru 20 na yaƙi. Ana ganin wannan a matsayin wata nasara ga ƙasar Iraƙi da ƙawayenta, ganin yadda ficewar sojojin Amurkan ke cikin sharuddan da Iran ta gindaya kafin dakatar da yakin...

Tattaunawa da Malam Nazifi Alaramma kan shata iyakar Najeriya da Kamaru 29.09.2026

Shugaban hukumar kula da iyakokin Najeriya Adamu Adaji, ya ce ƙasar na dab da kammala aikin shata iyakarta da Kamaru, bayan kwashe kusan shekaru 24 da kotun duniya ta ICJ ta yanke hukuncin mallaka yankin Bakassi ga Kamaru. A yayin wata zantawa da yayi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Abuja, ya ce a yanzu abinda ya yi saura a aikin bai wuce kafa tubali 260 a ɓangaren jihar Adamawa ba...

Tattaunawa da Rabi'u Kwankwaso kan iƙirarin Atiku na dawo da tallafin man fetur 28.09.2026

A kwanakin baya ne tsohon shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugabancin ƙasar a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ADC mai adawa, Atiku Abubakar ya sha alwashin maido da tallafin mai idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasar, lamarin da ya  janyo tattaunawa a tsakanin ƴan Najeriya a yayin da a gefe guda ya kaɗa hantar gwamnati mai ci. Akan batun tallafin ne Michael Kuduson ya gana da dan takaran mataim...

Ambasada Suleiman Ɗahiru akan taron Majalisar Ɗinkin Duniya 24.09.2026

An shiga rana ta uku a ci gaba da gudanar da Babban Taron Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, wanda ke matsayin dama ga illahirn shugabannin ƙasashe don gabatar da jawabai kan batutuwan da suka shafi duniya. To sai dai tun a ranar farko da aka buɗe wannan zama, shugaban Amurka Donald Trump ya fito fili inda ya yi fatali da wasu batutuwa da suka shafi ƙasa da ƙasa. Abdoulkarim Ibrahim Shikal...

Alhaji Shehu Ashaka kan yadda lamura ke tafiya bayan buga kugen siyasa 23.09.2026

A Najeriya, yayin da jama’a ke ci gaba da kokawa dangane da rashin tsaro da kuma tsadar rayuwa, a nasu ɓangare kuwa ƴan siyasa waɗanda ke da alhakin tafiyar da lamurran jama’a da kuma samar da tsaro, sun duƙufa ne ta fannin yaƙin neman zaɓe.  Bashir Ibrahim Idris ya zanta da Alhaji Shehu Ashaka, ɗaya daga cikin dattijai a yankin Arewacin Najeriya, domin jin yadda yake kallon makomar alaƙa tsakanin...

Aissami Mahamadou kan dalilin Amurka na zuba jari a sashen Uranium ɗin Nijar 22.09.2026

Ana ci gaba da ɗiga ayar tambaya a game da dalilan da suka sa Amurka ta amince ta bai wa kamfanin Global Atomic Corporation na ƙasar Canada dala million 414 don gaggauta zuba jarin haƙo makamashin uranium a  jamhuriyar Nijar, duk da cewa alaƙa ta yi rauni tsakanin mahukuntan birnin Yamai da na Washington tun bayan kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya a ƙarƙashin Mohamed Bazoum. A game da wannan batu n...

Ƙungiyoyi sun yunƙura don tabbatar da adalci ga matasan da suka mutu a jihar Neja 21.09.2026

A Najeriya, ƙungiyoyi masu zaman kansu sun yunƙuro domin tabbatar da cewa an gudanar da bincike tare da hukunta masu hannu wajen mutuwar matasa aƙalla 37 lokacin da suke tsare a hannun jami’an tsaro n Civil Defense a jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar, lamarin da ya yi matuƙar tayar da hankula. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Comrade Abubakar Abdullahi, shugaban ƙungiyar Human Freedom Internat...

Muhd Ladan kan dakatar da samar da takardun kuɗin bai ɗaya da BRICS suka yi 18.09.2026

Ƙasashe mambobin Ƙungiyar BRICS da suka gudanar da taronsu na shekarar bana a ranakun 12 da kuma 13 ga wannan wata na Satumba, sun yanke shawarar dakatar da shirinsu na samar da takardar kuɗin bai ɗaya, domin kawo ƙarshen amfanin da Dalar Amurka a tsakaninsu. Domin jin dalilin ɗaukar wannan mataki da kuma sabuwar dabarar da suka runguma, Nura Ado Suleiman ya tattauna da mai magana da yawun ƙungiya...

Hamza Idris kan yadda ƴan Jarida a Najeriya da sassan Afrika ke fuskantar barazana 17.09.2026

Ƙungiyar Editocin kafafen yaɗa Labaran Najeriya ta koka kan ƙaruwar yadda jami’an tsaro ke cin zarafi da kuma take hakkin da ‘Yan Jarida, matsalolin da ka iya daƙile ‘yancin manema labarai. Cikin sanarwar da ta fitar bayan ganawa a Kano, ƙungiyar Editocin Najeriyar ta buƙaci kawo ƙarshen yadda ake fakewa da wasu dokoki ciki har da na hukunta laifukan da suka shafi Intanet, wajen yin barazana ga ay...

Dr Kabiru Adamu kan ƙara yawan makaman da Najeriya ta sayo daga ƙetare 16.09.2026

Wani rahoton hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS ya nuna cewar, yawan makaman da gwamnatin ƙasar ke sayowa daga ƙetare da zummar inganta tsaro a ƙasar ya ƙaru da kaso 104, inda ta kashe Naira biliyan 55 a cikin watanni shidda na farkon wannan shekara, idan aka kwatanta da abinda aka kashe wajen sayen makaman a shekarar bara. Tuni dai masana da sauran ƴan Najeriya suka fara bayyana ra’ayoyi mabanbant...

Souleyman Yahaya kan tasirin al'ummar Hausawa a ƙasar Togo 15.09.2026

Hausawa a ƙasar Togo kamar dai a sauran ƙasashe, sun gudanar da bukukuwan ranar Hausa ta duniya, inda suka yi amfani da wannan damar don tattauna al’adu da kuma tasirin wannan al’umma a cikin wannan ƙasar da ke Yamancin Afirka. Abdoulaye Issa ya zanta da Souleyman Yahaya, shugaban cibiyar yaɗa al’adu da kuma kare muradun Hausawa a Togo, wanda ya yi masa ƙarin bayani a game da yanayin zamantakewars...

Alhaji Ibrahim Muhammad kan yadda shirin samar da ɗan takarar adawa ɗaya a Najeriya ya rushe 14.09.2026

Hukumar Zaɓen Najeriya ta fitar da jerin sunayen mutane 18 da suka cancanci tsayawa takarar shugabancin ƙasar da mataimakansu, sai kuma wasu mutane dubu 4 da 860 da za su tsaya takarar neman kujerun Majalisun Tarayya a zaɓen da za a yi shekara mai zuwa. Wannan dai na nuni da cewa yunƙurin ƴan adawa na fitar da ɗantakarar ɗaya tilo don tunkarar jam’iyyar mai mulki ya ci tura. Abdoulkarim Ibrahim Sh...

An naɗa sabon kwamandan da zai jagoranci yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci a Najeriya 11.09.2026

A Najeriya an naɗa sabon kwamandan  da zai jagoranci yaƙin da ake da ƙungiyoyin ta’addancin na ISWAP da Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar, lamarin da ke nuni da cewa an maye gurbin wanda ke jagorantar wannan runduna ƙasa da shekaru biyu bayan naɗa shi kenan. Shin wanan sauyi ya dace da halin da  ake ciki na yaƙi da ta’addanci ko kuma dai kawai garambawul ne da aka saba yi? Akan haka ne Michae...

Kamilu Sani Fagge kan tsanantar rikici a Gabas ta tsakiya 10.09.2026

Rikicin Gabas ta Tsakiya da ya tsananta tsakanin Amurka da Iran na cigaba da faɗaɗa, inda a ‘yan kwanakin nan ya kai ga sake tayar da rikicin Yemen tsakanin gwamnatin ƙasar da Saudiya ke marawa baya, da kuma ‘Yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran, ɓangarorin da zuwa yanzu suka rasa mayaƙa fiye da 500. Baya ga datse mashigin ruwan Hormuz, a halin yanzu rikicin na Gabas ta Tsakiya ya shafi...

Hon Sama’ila Mohammed kan saida hannun jarin matatar man Dangote 09.09.2026

A ranar Litinin da ta gabata, matatar man fetur ta Ɗangote ta dasa ɗambar shirinta na shiga kasuwar hada-hadar hannayen jari, waɗanda shugaban rukunin kamfanonin na Ɗangote, Alhaji Aliko, ya ce ana iya mallakar aƙalla guda 10 da ƙasa da Naira dubu 6. Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Honorable Sama’ila Mohammed, masanin tattalin arziƙi a Najeriya, wanda ya yi tsokaci kan tasiri da kuma y...

Tattaunawa da Datective Auwal Bala kan baiwa MOPOL damar yaƙi da ta'addanci 08.09.2026

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta sanar da tsaurara matakan yaƙi da ta’addanci da ya addabi ƙasar ta hanyar shigar da ƴan sandan kwantar da tarzoma cikin aikin fatattakar ƴan ta’adda. Da yake jawabi yayin wani rangadi da ya kai barikokin ƴan sanda a jihar Lagos, babban sufeton ƴan sandan ƙasar Tunji Disu ya ce, daga yanzu za’a sanya jami’an cikin aikin gadan-gadan. Game da wannan batu Rukayya Abba K...

Dr Salissou Ibrahim Yahaya kan amincewa da yi wa taswirar duniya gyara 07.09.2026

Majalisar Ɗinkin Ɗuniya ta amince da ƙudirin da ke bayar da damar yi wa taswirar duniya gyara, bayan da ƙasashen Afirka suka gabatar da ƙorafin cewa wadda ake amfani da ita a yau na ɗauke da kura-kurai tare da tauye faɗin nahiyar na haƙiƙan. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Salissou Ibrahim Yahaya, malami kuma masani kimiyar taswirar duniya a Jami’ar Damagaram da ke Jamhuriyaer Nijar, wan...

Martani kan iƙirarin shugaban Najeriya game da ciyar da arewacin ƙasar gaba fiye da kowanne yanki 03.09.2026

A Najeriya iƙirarin da shugaba Bola Tinubu ya yi cewa yankin arewacin ƙasar ce ta fi cin gajiyar manufofinsa na  sauye-sauyen tattalin arziƙi ya janyo suka daga  masu ruwa da tsaki, inda ƙungiyar al’ummar Arewacin ƙasar da wasu ƙungiyoyin yankin suka caccaki kalaman, su na mai cewa a maimakon cigaba, manufofin shugaban sun mayar da yankin arewa cibiyar talauci. Akan haka ne Michael Kuduson ya tatt...

Dr Ibrahim Modibbo kan tattaunawar samar da ɗan takara ɗaya da zai kara da Tinubu 01.09.2026

Wakilan Jam’iyyun adawa a Najeriya sun gana a jiya Litinin, inda suka tattauna kan yiwuwar ƙulla yarjejeniyar haɗa ƙarfi wajen mara wa ɗan takara guda baya a zaɓen shugabancin ƙasar da ke tafe a 2027. Wannan taro ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin G-100, ƙungiyar wasu fitattun ƴan Najeriya da ke ƙoƙarin haɗa gamayyar jam’iyyun adawa. Don jin ƙarin bayani kan abinda aka cimma, Nura Ado Suleiman ya...

Dr Kabiru Adamu kan boren sojoji a Jamhuriyar Nijar 31.08.2026

Ƙura ta lafa a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar bayan da wasu sojoji  suka kai hari filin jirgin sama da fadar shugaban ƙasar, a wani bore da suka fara tun cikin daren Juma’a zuwa wayewar safiyar Asabar, lamarin da ya haifar da musayar wuta da fashe-fashe na tsawon sa'o'i. Rahotanni na cewa dakarun hayar Rasha sun taimaka wajen daƙile boren na ƙananan sojoji da suka kaucewa fagen daga domin fa...

Muhd Makiga kan maƙudan kuɗin fansar da ƴan ta'adda ke samu a Najeriya 28.08.2026

A Najeriya masana da wasu ƴan ƙasar na ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan rahoton cibiyar binciken tsaro ta SBM Intelligence, da ya nuna cewar ƴan ta’adda sun karɓi kuɗaɗen fansar da yawansu ya kai Dala miliyan 5.8, daidai da kusan naira biliyan 8 cikin shekara guda. Rahoton, ya ce ƴan ta’addan sun ƙarbi kuɗaɗen ne a tsakanin watan Yulin shekarar bara ta 2025, da kuma Yunin bana, kuma mayaƙan Boko H...

Isa Sunusi kan yadda ƴan siyasa suka fara kalaman tinzira al'umma 27.08.2026

Yayin da aka kada gangar siyasar Najeriya, ana zargin wasu ƴan siyasar da kalaman tinzira tashin hankali, abinda ke barazana ga zaman lafiyar jama'a. Bayan Sanatan jihar Osun da ya buƙaci a kashe magoya bayan jam'iyyar adawa, an jiyo shugaban karamar hukumar Kuje dake Abuja na kira ga wadanda basa goyan bayan APC da su fice daga yankin. Tuni wannan ya fara jefa fargaba a tsakanin jama'a. Bashir Ib...

Kasuwar hada-hadar hannayen jarin Najeriya ta zama mafi ƙarfi a duniya 10.07.2026

Cikin makon nan, kasuwar hada-hadar hannayen jarin Najeriya, ta kafa tarihin zama mafi ƙarfi gami da bunƙasa a faɗin Duniya, bayan zarta mai riƙe da kambun a baya bayan nan, wato takwararta ta Korea ta Kudu.   Rahoton kamfanin Bloomberg ya nuna cewa, zuwa yanzu Kasuwar ta Najeriya ta samu tagomashi ne da kaso 67 cikin 100, yayin da ta Korea ta Kudu ke da kaso 66. Domin jin ƙarin bayanin kan dalila...

Najeriya na neman goyon bayan China wajen yaƙi da ta'addaci - Bello Dambazau 09.07.2026

Najeriya na tattaunawa da China wajen ganin ta samu goyon bayan da ya dace a fasahar zamani da kuma makamai domin shawo kan matsalolin tsaro da suka addibi ƙasar. Sabon jakadan Najeriya a ƙasar China Janar Abdurrahman Bello Dambazau mai ritaya ya bayyana haka a tattaunawar da suka kayi da Bashir Ibrahim Idris. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar.

Ascolta il podcast Bakonmu a Yau su Replaio

Radio e podcast in un'unica app - gratis e senza registrazione. Installala oggi e non perderti il lancio

Scaricala su Google Play

Replaio non è un editore di podcast; i nomi dei programmi, le copertine e l'audio appartengono ai rispettivi autori e vengono distribuiti tramite feed RSS pubblici