DW
Taba Ka Lashe
Shirin al´adu, addinai da kuma zamantakewa tsakanin al´ummomi dabam-dabam a duniya. Taba Ka Lashe shiri ne da ke duba batutuwan da suka shafi al'adu da zamantakewa tsakanin al'ummomi da mabiya addinai dabam-dabam a duniya da zummar kyautata zamantakewarsu, zaman lafiya da kuma fahimtar juna tsakani. Muna gabatar muku da shirin ta rediyo a kowane mako, kuna kuma iya sauraronsa a shafinmu na Internet da kuma ta kafar Podcast.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Kultur: (24+25.06.2026) Sukur Kingdom - MP3-Stereo 30.06.2026 9:38
Mai marataba sarkin Sukur ke nan Luka Gizik, yake bayyana irin jimawar da masarautarsa da ke tsaunukan na Mandara a jihar Adamawan Najeriya ta yi.
Taba Ka Lashe 16.06.2026 16.06.2026 9:55
Shirin ya duba zamantakewa da cudanyar Kiristoci da Musulmi a jihar Filato da ta bambanta da ta sauran wurare a Najeriya,
Taba Ka Lashe 02.06.2026 02.06.2026 9:41
A Nijar, watanda, al'adar hada kudi don sayen dabba (Saniya) lokacin bukukuwan salla ta kama hanyar bacewa a kasar Hausa.
Taba Ka Lashe: 13.05.2025 19.05.2026 10:30
Maazou Dan Alalo yana ɗaya daga cikin shahararrun mawakan Jamhuriyar Nijar.
Taba Ka Lashe 12.05.2026 12.05.2026 10:12
Wannan shirin ya dubi yadda wakokin bege na addinin Islama ke kara samun karbuwa tsakanin matasa a kasashen nahiyar Afirka, duk kuwa da yawan sabanin fahimta da ake da su.
Taba Ka Lashe: 08.04.2026 14.04.2026 9:53
Wai shin kun san cewa a yankin Agadez na Jamhuriyar Nijar, akwai wata sarauta da ake kira ANASTAFIDAT da ke da karfin fada a ji baya ga saurautar sarkin Abzun?
Taba Ka Lashe: 25.03.2026 31.03.2026 10:24
Nishadi ga samari da 'yan mata a shekarun baya a yankuna irin na Katsina, Maradi, Madawa har zuwa Tahoua da wasu sauran sassa.
Taba Ka Lashe: 11.03.2026 17.03.2026 9:52
Buda baki ko Shan ruwa ko iftar a azumin watan Ramadan tsakanin Musulmi da Kirista ya kama hanyar zama al'ada a Kaduna da ke Najeriya
Taba Ka Lashe 06.03.2026 06.03.2026 9:54
Shirin ya duba kabilar Dogon na kasar Mali da ta yi fice a yankin yammacin Afirka musamman a Kudu maso gabashin kasar Mali.
Taba Ka Lashe: 25.02.202 03.03.2026 10:18
Dauri rayuwa ta zamantakewar al'ummar Hausa Fulani da ma wasu kabilun ta kasance cike da alkunya da kuima kamun kai ta yadda matar aure ke kauracewa fadar sunan danta ko mujinta.
Taba Ka Lashe 18.02.2026 18.02.2026 9:41
Shirin ya yi nazari kan suna a tsakanin kabilu da kuma radin suna ko kuma zanen suna a kasashe daban-daban na Afirka.
Taba Ka Lashe: 11.02.2026 17.02.2026 9:41
Suna dai linzami ne, kuma 'dan adam ya fara amfani da suna tun fil azal domin fayyace asali ko al'ada ko kuma jinsin da mutum ya fito.
Taba Ka Lashe 20.01.2026 20.01.2026 9:48
Shirin ya duba zalakar tsohon firaministan Najeriya Sir. Abubakar Tafawa Balewa wajen sarrafa magana a harshen Ingilishi.
Taba Ka Lashe: 07.01.2026 13.01.2026 9:55
Ko kun san ana alakanta wasu fina-finan Indiya da kokarin yin fancale ga addini, musamman ma a Pakistan da ke makwabtaka da su? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan wannan dambarwa.
Taba Ka Lashe 16.12.2025 16.12.2025 9:51
Shirin ya duba al'adun kabilar Pyemawa a Najeriya da suka rayu a cikin duwatsu da koguna tun shekaru 300 da suka shude.
Taba Ka Lashe 02.12.2025 02.12.2025 9:45
Shirin ya duba komabaya da al’adar wasannin karkara a lokacin kaka yayin tattara amfanin gona ke fuskanta a Zinder na Jamhuriyar Nijar.
Taba Ka Lashe 25.11.2025 25.11.2025 9:37
Shirin ya duba yadda Kabilar Shuwa da wasu makiyaya ne suka kaura zuwa jihar Kano sakamakon matsalar tsaro ta Boko Haram.
Taba Ka Lashe: 12.11.2025 18.11.2025 9:49
Bayan shekaru ashirin na aiki da kuma jinkiri marasa adadi, a karshen an bude babban gidan tarihi na Masar ga jama'a.
Taba Ka Lashe: 06.11.2025 13.11.2025 9:46
Mawakan baka na Hausa na kwaikwayon fitattu daga cikinsu, wadanda suka yi shura suka kuma shude daga bisani. Wacce irin barazana zamani ke yi, ga wakokin baka na al'adar Kasar Hausa? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari a kai.
Taba Ka Lashe 30.09.2025 30.09.2025 10:16
Tambari kayan kida ne na kaɗe-kaɗe da ke kunshe da ganga wanda aka shimfiɗa fata ɗaya ko fiye da haka. Ana buga shi da makidi a wasu wuraran ma da hannu a cikin masarautu. Wannan shi ne abinda shirn wannan lokaci ya kunsa.
Taba Ka Lashe: 17.09.2025 23.09.2025 9:52
Abuja hedikwatar Najeriya birni ne da ke bunkasa cikin sauri, sai dai ‘yan asalin wannan wuri ci gaban da aka samu ya tura su gefe guda.
Taba Ka Lashe: 20.08.2025 26.08.2025 9:23
Bikin kakar sabuwar doya na daya daga cikin biki mafi girma na kabilar Ibo wadanda suka fito daga yankin kudu maso gabashin Najeriya
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.