DW
Taba Ka Lashe
Shirin al´adu, addinai da kuma zamantakewa tsakanin al´ummomi dabam-dabam a duniya. Taba Ka Lashe shiri ne da ke duba batutuwan da suka shafi al'adu da zamantakewa tsakanin al'ummomi da mabiya addinai dabam-dabam a duniya da zummar kyautata zamantakewarsu, zaman lafiya da kuma fahimtar juna tsakani. Muna gabatar muku da shirin ta rediyo a kowane mako, kuna kuma iya sauraronsa a shafinmu na Internet da kuma ta kafar Podcast.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Taba Ka Lashe: 30.07.2025 05.08.2025 10:00
Shan shayi al'ada ce mai tushe da ta yadu a tsakanin al'umomi mabanbanta a fadin duniya.
Taba Ka Lashe: 23.07.2025 29.07.2025 9:50
Rawar sarakunan gargajiya wajen magance matsalolin tsaro a jihar Zamfara da ke Najeriya.
Taba Ka Lashe: 02.07.2025 08.07.2025 9:55
Ko kun san tarin kalubalen da kwararrun ma'aikata ke sha kafin su samu takardar izinin shiga Jamus wato Visa, duk da cewa kasar na matukar bukatarsu? Shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya yi nazari a kai.
Taba Ka Lashe: 25.06.2025 01.07.2025 9:51
Ko kun san yadda Kabilar Tangale a jihar Gombe ke kare abincinsu na gargajiya? Shirin Taba Ka Lashe ya jiyo muku yadda suke yin abincin da ma adana shi.
Taba Ka Lashe 10.06.2025 10.06.2025 9:57
Shirin ya duba rayuwar fitacciyar zabiya Mariama Rabiou mai waka da Hausa da Zabamanci da Allah ya yi wa cikawa a Gaya ta Nijar.
Taba Ka Lashe 28.05.2025 03.06.2025 9:57
Sana'ar wanzanci, sana'a ce tun ta iyaye da kakanni a kasar Hausa, shin ko akwai banbamcin da aka samu a sana'ar a da da yanzu? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan wannan sana'a ta wanzanci.
Taba Ka Lashe: 14.05.2025 20.05.2025 9:54
Tsarin raye-raye da wake-wake tsakanin mutane bisa al'ada
Taba Ka Lashe: 07.05.2025 13.05.2025 9:46
Ko kun san irin al'ummar da ke zaune a yankin Obalande na jihar Legos da ke Tarayyar Najeriya? Shirinmu na Taba Ka Lashe ya lalubo muku wannan amsa.
Taba Ka Lashe: 16.04.2025 22.04.2025 9:41
Shirin ya duba yankin Zuru na jihar Kebbi da ke Najeriya kan al'adar aure na Gwalmou mai tsawon tarihi
Taba Ka Lashe 14.04.2025 08.04.2025 9:50
Shirin ya duba rijiyar Shehu Usman Dan Fodiyo mai dadadden tarihi da ke cikin tsakiyar birnin Sokoto, wacce ba ta taba ganin kafewarta ba.
Taba Ka Lashe 01.04.2025 01.04.2025 10:13
Miliyoyin jama'ar da suka yi imani da Allah da manzanninsa, na rayuwa a Jamus da yawan su ya haura miliyan shida. Kuma kasancewar su marasa rinjaye, bai hana da dama daga cikin su tafiyar da addininsu a cikin tsanaki ba ciki kuwa har da ibadunsu a cikin watan Azumin ramadana.
Taba Ka Lashe 19.03.2025 19.03.2025 9:58
Shirin ya duba yadda Hausawa mazauna kasar Senegal kei cudanya da 'yan asalin kasar duk da cewa suna daraja al'adunsu da ke da matikar muhimmanci a gare su.
Taba Ka Lashe 11.03.2025 11.03.2025 9:30
Shirin ya duba bikin fina-finai da wakokin adabi na Afirka FESPACO da ya saba gudana a birnin Ouagadougou na Burkina Faso.
Taba Ka Lashe: 26.02.2025 04.03.2025 9:34
A kasar Hausa a kan daura aure da yawa gabanin watan azumin Ramadan, sai dai a kan yi korafi a kan wannan al'ada ta auren dab da azumi. Shirin Taba Ka Lashe, ya yi nazari a kai.
Taba Ka Lashe 25.02.2025 25.02.2025 9:52
Shirin ya duba yadda mace ta yi nasarar zama dagaci a tsakanin kabilar Abzun da ke jihar Agadez saboda gaskiyarta da rikon amanarta.
Taba Ka Lashe 18.02.2025 18.02.2025 9:49
Shirin ya duba matakin gwamnatoci na sahale wa kafa Jami'oi masu zaman kansu bisa sharuda da ka'idoji domin bayar da ci-gaban ilimi a Najeriya.
Taba Ka Lashe: 05.02.2025 11.02.2025 10:05
Ko kun san wani abun busa da aka fi amfani da shi a gidajen sarauta wato "kakaki", ku biyo mu cikin Shirin Taba Ka Lashe.
Taba Ka Lashe: 15.01.2025 21.01.2025 9:59
Shekaru aru-aru maroka da mawakan baka na bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen bunkasa al'adu da martaba kimar al'umma a daular Hausa.
Taba Ka Lashe: 01.01.2025 07.01.2025 9:45
Ko kun san cewa har yanzu ana gudanar da al-adar nan ta sayen baki a Kasar Hausa idan an yi aure? Shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya yi nazari a kai.
Taba Ka Lashe: 04.12.2024 10.12.2024 9:45
Tsarin karatun Allo na neman ilimin da gwamnatin jihar Borno a Najeriya ke kokarin kyautatawa
Taba Ka Lashe 03.12.2024 03.12.2024 9:48
Shirin na al'adu ya duba tasirin gidan tarihi na Arewa (Arewa House) da ke Kaduna da ya tattara tarihin Marigayi Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da al'adu da sana'o'in yankin Arewacin Najeriya.
Taba Ka Lashe 20.11.2024 26.11.2024 10:00
Shirin ya duba al'adar kacici-kacici ko wasa kwakwalwa da malam Bahaushe ke amfani da ita wajen ilimantawa.
Taba Ka Lashe: 07.11.2024 12.11.2024 9:58
Shirin ya mayar da hankali ne kan masarautar Wurkun da ke karamar hukumar Karim Lamido a Jihar Taraba da ke tarayyar Najeriya,
Taba Ka Lashe 06.11.2024 06.11.2024 9:31
Shirin ya duba al'adar Masquerade, ko Basaje kamar yadda ake fassarawa, da ta kafu a yankin Kabilar Igbo a Najeriya.
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.