RFI Hausa
Al'adun Gargajiya
Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.
N'hésitez pas à visiter le site du podcast et à soutenir son créateur : www.rfi.fr
Où écouter ?
Les podcasts dans l'appli Replaio Radio Bientôt disponibleLes podcasts arrivent très bientôt dans l'appli. Installe-la dès maintenant et découvre en avant-première une toute nouvelle façon de vivre les podcasts
Épisodes
Yadda aka gudanar da bikin makiyaya na Cure Salee a Jamhuriyar Nijar 21.10.2025 9:38
Shirin a wannan mako ya yi tattaki ne, zuwa ƙauyen Ingal da ke Yankin Agadez a jamhuriyyar Nijar, domin waiwayar gagarumin bikin makiyaya da ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee' wanda aka saba yi duk shekara. Bikin makiyayan na Cure Salee ya gudana ne a tsakanin ranakun 4 zuwa 6 ga watan da muke ciki na Oktoba. Manufar bikin ita ce yadda za a ƙarfafa haɗin kai tsakanin makiyaya d...
Yadda sana'ar kaɗi ke gab da gushewa tsakanin al'ummar Hausawa 14.10.2025 10:03
Shirin al'adunmu na gado tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya mayar da hankali ne kan gushewar sana'ar kaɗi a ƙasar Hausa duk da kasancewarta guda cikin sana'o'in Hausawan suka gada kaka da kakanni. Galibi sana'o'in Hausawa na tafiya ne da tsarin rayuwa da zamantakewar jama'a, cikin wannan kuwa har da sana'ar kaɗi wadda galibi dattawa Mata suka fi ƙwarewa akai, kodayake wannan sana'a na gab...
Banbanci tsakanin maita da tsafi a mahangar al'adu da addini 07.10.2025 10:03
Shirin Al'adunmu na Gado tare da Nura Ado Suleiman a wannan mako, ya mayar da hankali kan manufar Maita da kambun baka a mahangar al'adu da kuma addini, a wani yanayi da ake yiwa wannan abubuwa biyu mabanbantan kallo. Duk da cewa wasu na yiwa waɗannan abubuwa biyu kallon abu guda, amma a wasu na kallon abubuwan biyu a matsayin mabanbanta kasancewar guda akan sameshi ne haka suddan yayinda ɗayan ku...
Yadda aka bar baya da ƙura a girmamawar da ka yiwa Rarara da digirin Dakta 23.09.2025 10:02
Shirin Al’adunmu na Gargajiya tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya sake waiwayar fagen Waƙa guda daga cikin fannoni masu tasiri a Adabin Harshen Hausa la’akari da gudunmawar waƙoƙin da kuma mawaƙan da ke rera su wajen bunƙasa harshen. Tun cikin makon jiya masana da sauran jama’ar gari ke tofa albarkacin bakunansu akan karramawar da wata Jami’a mai suna European-American University ta yi wa...
Sannu a hankali sana'ar ƙira na shuɗewa a jihar Agadez ta Jamhuriyar Nijar 16.09.2025 9:48
Shirin Al'adunmu na Gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda sannu a hankali sana'ar kira ke shudwa musamman ta ƴan Kabilar Abzinawa da ke jihar Agadez a jamhuriyar Nijar. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Issa.
Bikin cika shekaru 10 da fara Ranar Hausa ta Duniya - kashi na biyu 02.09.2025 9:59
Shirin Al’adunmu na Gado a wannan makon ya ɗora ne akan Bikin ranar Hausa ta Duniya, bikin da yake mayar da hankali wajen bunƙasawa da faɗaɗa harshe da kuma al’adun Hausawa a fadin Duniya. A watan Agustan shekarar 2015 aka fara gudanar da wannan biki na ranar Hausa ta Duniya a Najeriya da sauran ƙasashen da ke da al’ummar Hausawa, bikin da sannu a hankali ya riƙa samun karɓuwa gami da faɗaɗa har z...
Podcasts similaires
Replaio n'est pas éditeur de podcasts ; les noms des émissions, les visuels et l'audio appartiennent à leurs auteurs et sont diffusés via des flux RSS publics