RFI Hausa
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare
Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalin’ariziki, al’adu da dai sauransu…
Μην παραλείψεις να επισκεφτείς τη σελίδα του podcast και να στηρίξεις τον δημιουργό: www.rfi.fr
Δημιουργός
RFI Hausa
Κατηγορία
Ιστοσελίδα του podcast
Τελευταίο επεισόδιο
29 Σεπ 2026
Πού να ακούσεις;
Podcast στην εφαρμογή Replaio Radio Έρχεται σύντομαΤα podcast έρχονται σύντομα στην εφαρμογή. Εγκατάστησέ την τώρα και δες πρώτος μια εντελώς νέα προσέγγιση στα podcast
Επεισόδια
Ra'ayoyin masu sauraro kan ƙarancin makamashi a wasu ƙasashen yammacin Afrika 29.09.2026 9:42
Yayin da kusan a kowane mako ana iya a wayi gari da sabon farashin man fetur a Najeriya, a Jamhuriyar Nijar ana fama da ƙaranci da kuma tsadarsa ne a wasu jihohin ƙasar, yayin da ake fama da gagarumar matsalar ƙarancin gaz da ake amfani da shi domin girki. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta 18.09.2026 10:59
Yau juma'a kamar yadda aka saba, sashen Hausa na RFI na bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan dake ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga siyasa, tattalin arziƙi, tsaro, zamantakewa da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan ƴan aikin jarida dake fuskantar tarnaƙi a Afrika 16.09.2026 10:15
Ƴancin aikin jarida na ci gaba da fuskantar tarnaƙi a wasu ƙasashen Afirka, saboda yayin da wasu ke fuskantar tursasawa a Najeriya, a Jamhuriyar Nijar kuwa ana tsare da Moussa Tchangari kusan shekaru biyu ba tare da shara’a ba, yayin da a hannu ɗaya, wani ɗanjaridar wato Moussa Kaka ya ɓata yau kwanaki 16 kenan. A can kuwa Mali ko shekaran jiya litinin ma an yanke wa wani ɗanjaridar hukuncin ɗauri...
Ra'ayoyin masu sauraro kan hauhawar farashin man fetur a Najeriya 15.09.2026 9:49
Hauhawar farashin man fetur na ci gaba da haifar da tarin matsaloli ga al’ummar Najeriya, inda a jihohi irinsu Sokoto, Kebbi da Zamfara, farashin lita ya doshi Naira dubu ɗaya da 500 a halin yanzu kuma kusan hakan farashin yake a mafi yawan jihohin arewacimn ƙasar. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai yau, musamman game da yadda ake samun hauhawar farashin akai-a...
Ranar yaƙi da jahilci ta duniya a bana ya duba yadda za a inganta ilimin manya 08.09.2026 10:09
Ranar takwas ga watan Satumban kowacce shekara, rana ce da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware, tun a shekarar 1960 a matsayin ranar yaƙi da jahilci, inda ake mayar da hankali wajen faɗakar da jama'ar a sassan duniya mahimmancin ilimi da samar da tsari ko dabarun koyar da mutanen da basu samu dama ba. A mafi yawan ƙasashe dai an sha aiwatar da tsarin yaƙi da jahilci da ke bai wa dattijai ko masu many...
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta 28.08.2026 11:04
Kamar yadda aka saba ko wace rana irin ta yau Juma’a, muna baku damar tofa albarkacin bakin ku kan wasu abubuwa da ke ci muku tuwo a ƙwarya kama daga siyasa da tattalin arziƙi da zamantakewa da dai sauransu. To yau ba ta sauya zani ba, sai ku latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan kalaman tinzira jama'a da wasu ƴan siyasa suke 27.08.2026 10:59
A Najeriya ana ci gaba da mayar da martani mai zafi sakamakon kalaman da shugaban ƙaramar hukumar Kuje da ke birnin Abuja Mista Samuel Shekwolo ya furta, kan cewa duk wanda baya goyon bayan jam’iyya mai mulki ta APC ya fice daga karamar hukumar. Yayin da ake tunkarar zabe a Najeriya, sannu a hankali kalaman tunzuri da yiwa jama’a barazana a karuwa a tsakanin yan siyasa musamman daga bangaren jam’i...
Ra'ayoyin masu sauraro kan sace masallata 600 a jihar Neja 25.08.2026 9:44
A Najeriya al’umma na cike da zullumi a jihar Neja musamman bayan ƴan ta’adda sun saki wani bidiyo a kafafen sada zumunta wanda ke nuna mutane kusan 600, galibinsu mata da yara da kuma dattijai, waɗanda suka bayyana a matsayin masallatan da suka sace a gari na Borgu a Juma’ar da ta gabata. Mahukunta sun ce suna ƙoƙarin ceto su, amma hankula ba su kwanta ba gannin an saba ruwa ƙasa na shanyewa. Lat...
Ra'ayoyi kan yadda rashin bin ƙa'idojin gini ya haifar da ambaliya a Abuja da Kano 18.08.2026 10:30
A Najeriya duk da gargaɗin da hukumar yanayi ta NIMET ta riƙa yi a lokuta da dama game da ambaliyar da wasu sassan ƙasar zasu fuskanta a damunar bana, wajen ganin an ɗauki matakan daƙile illar da hakan zai haifar. Tuni aka ga wannan ambaliya a birane da dama ciki har da Abuja fadar gwamnatin ƙasar, birnin da ruwa ya shanye sassa da dama da ke matsayin ambaliya mafi muni da aka gani, wanda ake alaƙ...
Ra'ayoyin masu sauraro kan yadda zaɓen gwamnan Osun ya gudana Najeriya 17.08.2026 10:18
A Najeriya, Gwamna mai ci kuma ɗan takarar jam’iyar Accord Ademola Deleke ya lashe zaɓen jihar Osun da aka gudanar a ranar Asabar da ƙuri’u sama da dubu 511, yayin da ɗan takarar jam’iya APC mai mulkin ƙasar Bola Oyebamiji yazo na biyu da ƙuri’u dubu 444,815. Kafin ranar zaɓen dai an fuskanci dambarwar siyasa da rikice-rikice da suka yi sanadin mutuwar mutane sama da 40. Latsa alamar sauti don sau...
Ra'ayoyin masu saurare kan yadda gwamnonin Najeriya suka yi buris da kudaden UBEC 13.08.2026 10:00
A Najeriya, Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Kasa ta roƙi gwamnonin jihohi da su yi wa Allah su gaggauta karɓar sama da Naira biliyan 332 na kuɗaɗen tallafin daidaita tsarin ilimi. Shugabar Hukumar Aisha Garba wanda ta yi wannan kira, ta ce bayaga Naira biliyan 65 da aka ware akwai kuma wasu Naira biliyan 267 da aka ware domin inganta makarantun firamare a ƙananan hukumomin faɗin ƙasar. Ku dann...
Ra'ayoyin masu sauraro kan yunƙurin haɗa kan ƴan adawa a Najeriya don fiida ɗan takara ɗaya 12.08.2026 9:59
A Najeriya, ƙungiyar G –100 ta gamayyar wasu fitattun ƴan ƙasar kimanin 100 ta jagorancin wani sabon yunkurin ganin lallai sai jam’iyyun adawa sun yi haɗin guiwa domin fitar da ɗantakara ɗaya tilo da zai fafata da shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekara mai zuwa. Ku danna alamar sauraro dimin jin cikakken shirin tare da Oumar Sanni.
Ra'ayoyin masu sauraro kan haramtawa yara amfani da kafafen sadarwa a wasu ƙasashe 22.07.2026 10:04
Ana ci gaba da samun ƙarin ƙasashe a sassan Duniya da ke ɗaukar matakin taƙaitawa ko kuma haramta wa yara amfani da shafukan sada zumunta don basu kariya daga illolinsu. A halin yanzu dai fiye da ƙasashe 20 ne ciki har da India, da China da Faransa da Ingila, suka ɗauki wannan mataki, tun bayan da Australia ta zama ƙasa ta farko da ta bayar da misalin hana yara ‘yan ƙasa da shekaru 16 shiga shafuk...
Ra'ayoyin masu sauraro kan lashe kofin duniya da Spain ta yi 20.07.2026 10:51
Tawagar ƙasar Spain ta lashe gasar kofin duniya karo na biyu a tarihi, bayan ta doke Argentina da ke kare kambun a wasan ƙarshe da suka gudanar a daren jiya. Ita kuma Ingila ta ƙare a matsayi na 3 ne inda ta lashe kyautar tagulla da ke zama kyauta ta farko da ta lashe a kofin duniya cikin shekaru 60, ya yin da Faransa ta ƙare a matsayi na 4. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta 17.07.2026 10:09
Yau juma'a, rana ce da sashen Hausa na RFI ke bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga tsaro, tattalin arziƙi, siyasa, zamantakewa, da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwan mabanbanta 10.07.2026 10:58
Kamar yadda aka saba, yau rana ce da sashen Hausa na RFI ke bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga tsaro, siyasa, tattalin arziƙi da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan buƙatar majalisa na a dakatar da afuwa ga ƴan ta'adda 09.07.2026 10:38
Majalisar dattijan Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar da ta dakatar da shirin yin afuwa ko kuma sauya ɗabi’un tubabbun ƴan ta’adda a wani yunƙuri na dawo da su cikin al’umma, wanda ta ce ba ya taimakawa ƙoƙarin da ƙasar ke yi wajen yaƙi da ta’addancin da ya yi mata katutu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyi kan ziyarar da wakilan Vatican suka kai wa Sarkin Musulmin Najeriya 08.07.2026 10:52
Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Muhammadu Sa’ad Abubakar na uku, ya ce mutunta addinan juna, daina furta kalaman ƙiyayya ko tsatsauran ra’ayi, abubuwa ne da za su iya taimakawa ta fannin kyautata zamantakewa a tsakanin al’umma. Wannan dai gargaɗi ne da ke ƙunshe a sanarwar da aka fitar bayan ganawar da aka yi a babban masallacin birnin Abuja tsakanin mai alfarma Sarkin Musulmin da kuma tawaga...
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta 03.07.2026 9:19
Yau juma'a, kamar yadda aka saba, rana ce da sashen Hausa na RFI ke bai wa masu sauraro damar faɗin albarkacin bakin su kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga tsaro, tattalin arziƙi, siyasa, da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
Ra'ayoyin masu sauraro kan ambaliyar da ta afkawa ƙasashen gaɓar ruwan teku a Afrika 02.07.2026 9:59
Birane da dama da ke gaɓar ruwan tekun ƙasashen Yammacin Afrika sun fuskanci ambaliyar ruwa wadda ta haddasa asarar rayuka da kuma salwatar dukiyoyi masu tarin yawa. Birnin Accra na ƙasar Ghana da Abidjan Ivory Coast, a can ne aka samu asarar rayuka, yayin ambaliyar ta haddasa ɓarna ga gidaje da kadarori a biranen Lagos, Cotonou, Lome da sauransu. Lura da abin da ya faru a waɗannan birane da kuma...
Ra'ayoyin masu sauraro kan ci gaba da zanga-zangar ƙyamar baƙi a Afrika ta Kudu 01.07.2026 9:30
Bayan cikar wa’adin ranar 30 ga watan jiya da suka bai wa ƴan-ci rani don ficewa daga ƙasar, daga ƙarshe dai masu adawa da zaman baƙi a Afirka ta Kudu sun ƙaddamar da zanga-zangar neman ala dole sai sun fice daga ƙasar. Masu tarzomar dai na kallon ƴan asalin ƙasashen ƙetare a matsayin waɗanda suka mamaye gurabobin aiki, lamarin da ya jefe ɗimbin Ƴan Afirka ta Kudu cikin yanayin zaman kashe wando....
Ra'ayoyin masu sauraro kan tsadar mai duk da faɗuwar farashinsa a duniya 30.06.2026 10:16
Duk da cewa an samu faɗuwar farashin ɗanyan man fetur a kasuwar duniya sakamakon sulhun tsakanin Amurka da Iran, amma har yanzu ana ci gaba da fama da tsadar wannan makamashi a mafi yawan ƙasashen duniya. A Najeriya tuni Hukumar kare masu amfani da kayan masarufi ta ƙasar ta yi gargaɗin cewa ko dai dillalan mai su karya farashi ko kuma ta ɗauki matakan ladaftarwa a kansu. Latsa alamar sauti don sa...
Ra'ayoyin masu sauraro kan rawar ƙasashen Afrika a Gasar Kofin Duniya 29.06.2026 9:36
Ƙasashen Afrika 9 daga cikin 10 da ke halartar gasar cin kofin duniya ne suka samu nasarar tsallakawa zuwa zagayen ƙasashen 32 na wannan gasa da ke gudana a ƙasashen Amurka da Canada da kuma Mexico. Wannan dai shi ke matsayin babban tagomashi da nahiyar ta Afrika ta taɓa samu a irin wannan gasa ta cin kofin duniya. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta 26.06.2026 10:49
Yau juma'a kamar yadda aka saba, rana ce da sashen Hausa na RFI ke bai wa masu sauraro damar faɗin albarkacin bakinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga siyasa, tsaro, tattalin arziƙi, zamantakewa da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
Ra'ayoyin masu sauraro kan yadda matsalar tsaro ke kawo tarnaƙi ga manoma 24.06.2026 11:02
Yayin da damina ta fara kankama a Tarayyar Najeriya, wani abu da ake fargaba shi ne yadda matsalar tsaro ke iya haddasa tarnaki ga aikin gona hatta ma a wannan shekara. Kusan a kowace rana za a samu labarin cewa an kai hare-hare kan manoma da kan yi sanadiyyar kisa, yin garkuwa domin neman kuɗin fansa, yayin da a wasu lokuta ake tilasta wa manoman biyan haraji kafin ba su damar shiga gonakinsu. La...
Παρόμοια podcast
Το Replaio δεν είναι εκδότης podcast - τα ονόματα των εκπομπών, τα εξώφυλλα και ο ήχος ανήκουν στους δημιουργούς τους και διανέμονται μέσω δημόσιων ροών RSS