RFI Hausa
Wasanni
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
Обов'язково відвідайте сайт подкасту та підтримайте його автора: www.rfi.fr
Де слухати?
Подкасти в застосунку Replaio Radio Уже незабаромПодкасти незабаром з'являться в застосунку. Встановіть уже зараз і першими побачте зовсім новий погляд на подкасти
Епізоди
Messi ya yi bankwana da tawagar Argentina bayan doka wasanni 208 12.10.2026 9:56
Shirin "Duniyar Wasanni" tare da Khamis Saleh a wannan mako, zai dubu ne kan bankwanan da Lionel Messi ya yi da tawagar Argentina. A farkon watan Oktoban nan da muke ciki ne kyaftin ɗin tawagar ƙasar Argentina Lionel Messi, yayi bankwana da tawagar bayan kwashe tsawon shekaru 21 tana wakiltar ƙasar a wasannin matakin ƙasa da ƙasa. Messi ya fara bugawa Argentina wasanni ne a ranar 17 ga watan Agust...
Yadda ƴan wasa ke dawowa gida don buga wasannin sada zumunci a lokacin hutu 05.10.2026 9:55
Shirin a wannan mako ya yi duba ne kan yadda ƴan wasan da ke taka leda ke dawowa gida don buga wasannin sada zumunci a lokacin da suke hutu. A duk lokacin da aka kammala wasannin lig-lig a kan tafi hutu a kowace shekara musamman a nahiyar Turai da lig ɗin su ya fi jan hankali, wanda hakan kuma ke buɗe wani babi na wasanni a yankuna daban-daban da ƴan wasan ke fitowa domin nuna bajintarsu a zahiri...
An kammala gasar tseren Keke ta ƙasa karo na 6 a Jamhuriyyar Nijar 28.09.2026 9:48
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda aka gudanar da gasar tseren keke a jihar Maradi da ke Jamhuriyar Nijar. Wannan ne dai karo na 6 da ake gudanar da gasar da ta haɗa masu wannan wasa daga jihohi 8 na ƙasar, da nufin samun gwarazan shekara sannan kuma a zaɓa ƴan wasan da za su rinƙa wakiltar ƙasar a gasanni daban daban kama daga nahiyar Afirka dama matakin duniya idan dam...
Duniyar Wasanni: Wace waina ake toyawa a gasar Frimiya Lig ta Ingila 21.09.2026 10:01
Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda al’amura ke gudana a gasar Firimiya lig ta Ingila. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh
Ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a matakin Unguwanni sun fara cinikayyar ƴan wasa 07.09.2026 10:00
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda ake cinikayyar ƴan wasa a matakin ƙananan ƙungiyoyin Unguwanni. A yanzu dai ƙananan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da ke buga wasanni a matakin Unguwanni a jihar Kaduna, tuni suka rungumi tsarin cinikayyar ƴan wasa domin ƙarawa ƙungiyoyinsu ƙarfi. Wasu daga cikin masu horas da irin waɗannan ƙungiyoyi sun ce wannan tsarin cinikayya ya taimaka w...
Shugabanni hukumar NFF sun yi murabus bayan kiraye-kirayen ƴan Najeriya 31.08.2026 9:59
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan murabus ɗin da shugaban hukumar kwallon ƙafa ta Najeriya NFF Alhaji Ibrahim Gusau da wasu daga cikin mambobin kwamitin zartarwarsa suka yi, bayan matsin lambar da suka fuskanta kan koma bayan da tawagogin ƙasar suka samu a manyan gasanni na duniya, ciki har da gaza samun gurbin da tawagar mata ta ƙasar ta yi a gasar lashe kofin duniya da za a...
An fara yunƙurin rushe kwamitin ƙoli na hukumar NFF a Najeriya 24.08.2026 10:21
Shirin Duniyar Wasanni na yau ya mayar da hankali kan dambarwar da ta kunno kai a sashen wasanni na Najeriya bayan da hukumar wasannin ƙasar ta baiwa mambobin kwamitin ƙolin NFF wa’adin sa’o’i 24 tun a juma’ar da ta gabata kan su ajje aiki. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.
Manyan kalubalen da tawagogin ƙwallon ƙafar Najeriya ke fuskanta a harakar wasanni 17.08.2026 10:03
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Shamsiyya Haruna ya yi duba ne kan irin koma bayan da ake gani na faruwa a tsakanin tawagogin kwallon kafar Najeriya, kama daga bangaren mata mata da maza, har ma da yan wasa masu tasowa. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
Yadda ba a samun sabbin ƙasashen da ke lashe Gasar Kofin Duniya 27.07.2026 10:01
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda ba a samun sabbin ƙasashen da ke lashe gasar kofin duniya. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Spain ta lashe kofin duniya karo na biyu a tarihi 20.07.2026 10:00
Shirin Duniyar wasanni a wannan makon tare da Khamis Saleh ya yi duba ne a gameda nasarar da tawagar Spain ta yi kan takwararta ta Argentina a gasar cin kofin duniya karo na 23 Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........
Sharhin yadda wasannin kwata final na gasar cin kofin duniya suka gudana 13.07.2026 9:56
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali kan wasannin gab da na kusa da ƙarshe na gasar cin kofin duniya da aka kammala tsakanin ƙasashe 8 wanda kuma kawo yanzu ya rage ƙasashe 4 a wannan tafiya wadda ta faro da ƙasashe 48. A wasannin dai Faransa ta yi waje da Morocco yayinda Spain ta yi waje da Belgium kana Ingila ta yi waje da Norway yayinda Argentina mai kar...
Tawagogin ƙasashen Afirka 7da aka yi waje dasu bayan sun tsallaka zagayen ƴan 32 06.07.2026 10:00
Bayan nasarar da tawagogin ƙasashen Afrika 9 suka yi na kaiwa zagayen ƴan 32 a gasar lashe kofin duniya, wani lamari da ya sanya nahiyar ta kafa tarihin samun yawan wakilai a wannan zagaye, sai dai kuma ana iya cewa murna ta koma ciki domin dai tuni aka yi waje da 7 daga cikin 9. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........
Irin rawar da ƙasashen Afirka suka taka a gasar Kofin Duniya ta 2026 29.06.2026 10:00
Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda irin rawar da ƙasashen Afrika suka taka a wasannin rukuni a gasar lashe kofin duniya. A ƙarshen mako ne dai aka kammala wasanni rukuni, abinda ke nuna cewar an buga wasanni 72 daga cikin 104 da za a yi a wannan gasa. Sakamakon waɗannan wasani da aka yi ya nuna cewar anyi waje da tawagogin ƙasashe 16 daga cikin 48 dake fafatawa a gasar, inda ƙasashe 32...
Muhimman abubuwan da suka faru a Gasar lashe Kofin Duniya kawo yanzu 22.06.2026 10:00
Shirin a wannan mako zai yi duba ne kan wasu muhimman abubuwan da suka faru a gasar lashe kofin duniya ciki har da karawar da Cote d’Ivoire ta sha kashi a hannun Jamus. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.
Dalilan da ya sa ƴan Afirka suka juyawa tawagar Afirka ta Kudu baya 15.06.2026 9:59
Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako tare da Khamis Saleh ya yi duba kan irin wainar da ake toyawa a gasar nema cin kofin duniya da ƙasashen Canada da Mexico da kuma Amurka ke karbar bakunci. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shiri........
Shiri na musamman kan shirye-shiryen fara gasar lashe kofin duniya 08.06.2026 10:00
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan gasar lashe kofin duniya da za a fara a wannan makon. Ita dai wannan gasa ta lashe kofin duniya da aka faro a shekarar 1930, Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ce ke shiryata duk bayan shekara 4, sai dai a shekarun 1942 da kuma 1946 an samu tsaikon gudanar da gasar sakamakin yaƙin duniya na biyu. Bayan kammala gasar da ƙasar Qatar ta karɓi b...
PSG ta lashe Gasar zakarun ta Turai a karo na biyu 01.06.2026 10:00
Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako tare da Khamis Saleh ya yi duba kan yadda aka gudanar da wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai tsakanin ƙungiyar PSG da kuma Arsenal, inda PSG ɗin ta samu nasarar lashe gasar a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka ta shi 1-1. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Sharhi kan nasarar lashe gasar Premier League da Arsenal ta yi a bana 25.05.2026 10:00
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya yi duba ne kan nasarar lashe gasar Firimiyar Ingila da Arsenal ta yi a kakar wasan bana, bayan kwashe tsawon shekaru 22 batare da tayi tozali da kofin ba. A Lahadin nan ne aka miƙawa Arsenal kofin bayan buga wasanta na ƙarshe a gasar a wannan kaka tsakaninta da Cystal Palace, inda aka tashi 2-1. Tun kafin wasan na jiya ne dai aka nasarar da Arsenal a matsa...
Yadda aka lashe mafi akasarin gasannin lik-lik na nahiyar Turai 18.05.2026 9:53
Shirin Duniyar Wassani a wannan lokacin yayi duba ne kan yadda aka lashe mafi akasarin gasannin lik-lik na nahiyar Turai, in banda gasar Firimiyar Ingila. Barcelona ta lashe gasar La liga a Spain, a Inter Milan ta lashe gasar Serie A na Italiya, ita kuwa Bayern Munich ta ɗauke kofin Bundesliga na ƙasar Jamus, yayin da PSG ta lashe gasar League 1 ta Faransa. A yanzu haka dai gasar Firimiyar Ingila...
Yadda aka gudanar da gasar Super 4 ta a Najeriya 11.05.2026 9:59
A ranar juma’ar data gabata ne dai aka kammala gasar gasar Super 4, wacce aka fafata tsakacin ƙungiyoyi 4 da suka haɗa da Sporting Lagos da Inter Lagos da Ranchers Bees ta Kaduna sai kuma Doma United, da suka zama zagaru a rukunoninsu na gasar NNL, gasa ta biyu mafi daraja a Najeriya. An gudanar da gasar ne a yanayin yadda ake gudanar da gasar lik-lik, inda kowa ya kara da kowa ganin cewa kowaccen...
Matsalolin da suka dabaibaye ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars 04.05.2026 9:59
A wannan mako shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali ne kan halin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars ke ciki, wanda ya haddasawa ƙungiyar gagarumin koma baya. Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars, ta kasance guda cikin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar ƙwararru da ake ji da su a shekarun baya daga yankin Arewacin Najeriya, wadda ta shafe tsawon shekaru tana gwa...
NPFL: Saura mako 3 a ƙarƙare amma har yanzu ba a san zakaran bana ba 27.04.2026 10:00
Shirin awannan mako ya leƙa gasar Firirmiyar Najeriya ne wadda ke gab da ƙarƙarewa, amma kuma haryanzu ba a san maci tuwon ba. Yanzu haka dai an kammala wasannin mako na 35 a gasar Firimiyar Najeriya, wadda ya rage mako 3 kacal a kammala gasar a kakar wasa ta bana, amma sai dai haryanzu ƴar manuniya bata nuna ƙungiyar da za ɗauki gasar ba tsakanin ta saman teburi harzuwa wadda take a mataki na huɗ...
Sharhi kan wasannin dab dana kusa dana ƙarshe a gasar zakarun Turai 20.04.2026 10:00
A makon daya gabata ne aka kammala wasannin zagayen dab dana kusa da na ƙarshe na gasar zakarun Turai, inda Bayern Munich ta cire Real Madrid, Atletico Madrid ita kuma ta doke Barcelona, Arsenal ta fidda Sporting CP, yayinda PSG ita kuma ta samu galaba kan Liverpool. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...............
Matakan da CAF ke dauka don warware dambarwar da ke tsakanin Morocco da Senegal 13.04.2026 10:00
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Khamis Saley ya yi duba akan dambarwar da da ta taso dangane hukuncin karɓe nasarar Senegal ta lashe kofin Afrika na baya bayan da hukumar CAF tayi tare da maida nasarar ga ƙasar Morocco Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Hasashe game da rawar da ƙasashen Afirka za su taka a gasar lashe Kofin Duniya 06.04.2026 10:00
Shirin a wannan lokaci tare da Khamis Saleh ya yi duba ne kan yadda aka kammala samun tawagogin ƙasashen da za su fafata a gasar lashe kofin duniya da ke tafe a watan Yuni mai zuwa. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
Схожі подкасти
Replaio не є видавцем подкастів; назви шоу, обкладинки та аудіо належать їхнім авторам і поширюються через публічні RSS-канали