RFI Hausa
Mu Zagaya Duniya
Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.
Podcast'in sitesini ziyaret etmeyi ve yapımcısını desteklemeyi unutma: www.rfi.fr
Nereden dinlenir?
Uygulamada podcast'ler Replaio Radio Çok yakındaPodcast'ler çok yakında uygulamaya geliyor. Şimdi yükle ve podcast'lere yepyeni bir bakışı ilk gören sen ol
Bölümler
An cimma yarjejeniyar tsagaita wutar makwanni 2 tsakanin Amurka da Iran 11.04.2026 20:29
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' tare da Oumaru Sani, ya yi bitar wasu daga cikin muhimman labaru kan lamurran da suka wakana a makon da muka yi wa bankwana, daga cikinsu kuma akwai yarjejeniyar tsagaita wutar kwanaki 14 da aka cimma tsakanin Amurka da Iran, bayan da ƙasar Pakistan ta shiga tsakani.
Rikicin Gabas ta Tsakkiya: Dakarun Amurka sama da 2000 sun isa yankin 04.04.2026 20:55
Shirin mu na yau ya fara yadda zango a yankin Gabas ta Tsakiya inda rikicin Amurka da Isra’ila kan Iran ke cigaba da tsananta duk da tayin shiga tsakani da wasu kasashen Larabawa su ka faro karshen mako a Pakistan da zummar kawo karshen rikicin da tuni ya kasara tattalin arzikin duniya. A cikin ranakun ƙarshen mako kamfanin dilancin labaran Reuters ya bayyana cewa sojojin Amurkan dubu 2 da 500 su...
Wane hali ake ciki game da yaƙin Gabas ta tsakiya 28.03.2026 19:50
Shirin Mu zagaya Duniya na wannan rana ya mayar da hankali kan yakin Gabas ta tsakiya da halin da yanayin tsaro ke ciki a Najeriya da sauran manyan labaran da suka faru a sassan duniya cikin wannan mako. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Oumarou Sanni.
Yadda rikicin Iran ke faɗaɗa a yankin Gabas ta Tsakiya 07.03.2026 20:44
A Wanan makon shirin zai karkata alakarsa ne yankin Gabas ta Tsakiya inda sabon rikici ya barke tsakanin hadakar Amurka da Isra’ila da kuma Iran. A cikin shirin zamu yi duba dangane da yadda rikicin ke cigaba da faɗaɗa zuwa sauran kasashen yankin da ma tasirinsa kan bangarori daban-daban a wanan duniyar sai a gyara zama domin sauraron cikakakken shirin.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci Pakistan da Afghanistan su kai zuciya nesa 28.02.2026 19:31
Shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan mako tare da Oumarou Sani ya mayar da hankali kan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka bankwana da shi, masamman kan ƙazancewar rikici tsakanin Afghanistan da Pakistan, bayan da Pakistan ta ƙaddamar da harin Operation Ghazab lil-Haq a matsayin martani ga hare-haren da tace Taliban ta kai wa sojojinta, da kuma dambarwar Amurka da Iran kan yarjejeniya...
Sanya hannu kan dokar zaɓe da Tinubu ya yi ta bar baya da ƙura 21.02.2026 20:27
Shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan mako tare da Oumarou Sani kamar ya mayar da hankali kan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka bankwana da shi, masamman kan dambarwar da ta biyo bayan sa hannun da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yiwa dokar zaɓen ƙasar, da kuma mummunar gobarar da aka samu a kasuwar Singa da ke jihar Kano. Haka nan shirin ya yi bitar hukuncin ɗaurin rai da rai...
Harin Kwara da dambarwar Nukiliyar Iran na cikin manyan labaran makon da ya gabata 07.02.2026 20:23
Shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan mako tare da Oumar Sani kamar kullum ya mayar da hankali kan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka bankwana da shi, masamman harin da ya kashe sama da mutane 170 a jihar Kwara dake arewacin Najeriya.
Ƙungiyar IS ta dau alhakin harin da aka kai filin tashin da saukar jirage na Diori Hamani a Nijar 31.01.2026 20:40
A daren Laraba zuwa wayewar ranar Alhamis, filin jirgin saman Diori Hamani na Yamai da ke jamhuriyar Nijar ya fuskanci wani hari na ɗan lokaci daga wasu mayaka na ƙungiyar IS. Gwamnatin sojin Nijar, tare da taimakon sojojin Rasha,ta murkushe maharan. A yanzu haka,jiragen sama sun ci gaba da zirga-zirga, a cewar hukumar da ke kula da harkokin sufurin jiragen sama na ƙasar.
Kisan mutane 7 ƴan gida ɗaya ya tayar da hankalin jama'a a Kano 25.01.2026 19:16
Daga cikin abubuwan da Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan mako ya yi duba akai har da batun kisan Fatima Abubakar da ƴaƴanta 6 a Unguwar Ɗorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin......
Aƙalla mutane 5000 ake fargabar sun mutu a zanga-zangar Iran 17.01.2026 20:31
Mahukuntan Iran sun yi barzanar amfani da hukuncin kisa kan masu zanga-zangar wadda ta juye zuwa tarzoma inda ofishin babban mai shigar da ƙara na gwamnati ya ce akwai yiwuwar idan aka fara ɗaukar wannan mataki a samu sassaucin zanga-zangar. A nasa bangare shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar daukar mataki mai tsauri kan Iran muddun hukumomin ƙasar suka fara kashe masu zanga-zangar tsadar...
Benzer podcast'ler
Replaio bir podcast yayıncısı değildir; program adları, kapak görselleri ve ses içerikleri yazarlarına aittir ve herkese açık RSS beslemeleri aracılığıyla dağıtılır