RFI Hausa
Mu Zagaya Duniya
Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.
Glöm inte att besöka poddens webbplats och stötta skaparen: www.rfi.fr
Var kan du lyssna?
Poddar i appen Replaio Radio Kommer snartPoddar kommer snart till appen. Installera nu och bli först med att uppleva ett helt nytt sätt att lyssna på poddar
Avsnitt
Shugaban Faransa ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza a matsayin abin kunya ga duniya 26.09.2026 20:20
A yau shirin ya yi waiwaye kan bankado yadda wasu fitattun yan siyasa a Najeriya suka wawure makudan kudade tare da mallakar kadarori a Amurka, sai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da ta fara gwajin allurar Ervebo don daƙile cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, da kuma fassarar kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron a babban taron MDD da ya bayyana halin da ake ciki a zirin Gaza na Palasdin...
Ana ci gaba da tsokaci kan mutuwar mutane a hannun Civil Defence na jihar Neja 19.09.2026 20:40
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon ya tabo batun mutuwar matasa sama da 30 a jihar Neja da ke Najeriya a hannun hukumar tsaro ta Civil Defence. Haka nan Gwamantin Guinea ta aike da gargaɗi a hukumance ga kafofin yaɗa labaran Faransa game da yadda suke kiran sunan shugaban ƙasar, sai kuma Majalisar Ɗinkin Duniya da ta buƙaci masu bincike na ƙasa da ƙasa su karaɗe ilahirin Zirin Gaza, domin tat...
Dangote ya buɗewa al'uma ƙofar shiga a dama dasu a harkokin matatar mai 12.09.2026 20:39
Shirin mu zagaya Duniya na wannan ya ba da hankali ne akan yadda Attajirin Afirka Aliko Dangote ya buɗe ƙofar sayar da hannayen jari ga jama'ar Najeriya, sai kuma matakin da mahukuntan Nijar suka ɗauka na umartar masu ababen hawa dasu je Yamai babban birnin ƙasar domin duba lafiyar ababen hawansu, sai batun ladan da Shigaban Amurka Donald Trump ya sanya ladan Dala dubu biyar-biyar ga Amurkawa idan...
Yunkurin juyin mulki a Nijar ya ci gaba da ɗaukar hankali a faɗin duniya. 05.09.2026 20:52
A wannan makon shirin Mu Zagaya Duniya ya yi waiwayen kan sukar kalaman shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya yi na cewa arewacin kasar ya fi amfana da manufofinsa, sai batun juyin yunkurin juyin mulkin Nijar da ya dauki hankali, sai rahoton MDD da ya gano katsalandan din kasashen waje ne ke rura wutar rikicin Sudan, sai luguden wutar da aka yi musaya tsakanin Amurka da Iran da ya janyo asarar...
Adadin mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwan Nepal na ci gaba da ƙaruwa 29.08.2026 20:29
Shirin ''Mu Zagaya Duniya" tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako, ya taɓo muhimman batutuwan da suka faru a makon da muke bankwana da shi, inda ya taɓo yadda ƴanbindiga suka yi awun gaba da mutum sama da 600 a wani kauye da ke kan iyakar Najeriya da Benin a can jihar Neja. Adadin mutanen da mumunar ambaliyar ruwa ta kashe a Nepal ya haura zuwa 470. A ɓangaren wasanni kuwa, shirin ya yi waiwaye ka...
Mu zagaya Duniya: Fara yaƙin neman zaɓe da musayar yawu tsakanin Tinubu da Atiku 22.08.2026 20:17
Shirin ''Mu Zagaya Duniya" tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako kamar yadda aka saba ya taɓo muhimman batutuwan da suka faru a makon da muke bankwana da shi a Najeriya da sauran ƙasashen Afrika da ma duniya baki ɗaya. Cikin batutuwan da shirin ya taɓo akwai yakin neman zaben Najeriya, inda aka jiyo tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar na shan alwashin dawo da tallafin man fetur, da ku...
Waiwaye game da muhimman labarai da suka faru a wannan makon 15.08.2026 20:33
A Colombia, wata girgizar ƙasa mai karfin maki 7.4 da ta afkawa ƙasar da ke kudancin Amurka tare da hallaka akalla mutane sama da 100, yayin da wasu da dama suka jikkata,a cikin shirin da ke waiwaye game da muhimman abubuwan da suka faru a makon da mu kayi ban kwana,wato Mu zagaya Duniya za ku ji irin wainar da aka tuya a wasu ƙasashe..............
Saudiya, Pakistan da Turkiya sun sanar da kulla yarjejeniyar tsaro 08.08.2026 20:57
Ƙasashen Saudiya,Pakistan da kuma Turkiya sun sanar da kulla yarjejeniyar tsaro a tsakanin su yau juma’a a birnin Djeddah a wani yanayi da ake kara samun tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya. Yarjejeniyar da aka raɗa wa suna yarjeniyar Makka, ko baya ga harakar tsaro ta kuma tanadi faɗaɗa alakar da ke tsakanin ƙasashen a fanoni daban-daban.
Mu Zagaya Duniya: Zafin alaƙa tsakanin Najeriya da Afrika ta kudu 01.08.2026 19:29
Shirin "Mu Zagaya Duniya" tare da Oumarou Sani kamar kowanne mako ya taɓo muhimman labaran da suka faru a sassa daban daban na Najeriya ciki har da zafin alaƙa tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu, kana dambarwar ma'aikatar Bogi a Najeriya sai kuma batun cika shekaru 3 da faro mulkin Soji a Najeriya sannan batun ficewar Chadi daga kotun ICC. Zamu soma shirin daga Najeriya inda batun kirkirar ma’aik...
Mu zagaya Duniya: Kotu ta yiwa ƴan ta'adda ɗaurin rai da rai a Najeriya 25.07.2026 20:42
Shirin Mu zagaya duniya tare da Oumarou Sani ya mayar da hankali kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke bankwana da shi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin wanda ya taɓo dukkanin batutuwa kama da tsaro da tattalin arziƙi, siyasar ƙasashe dama rikice-rikice.
Ceto ɗalibai da malamansu a Oyo na cikin labarai da suka ja hankali a makon jiya 18.07.2026 20:51
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Oumar Sani ya yi bitar wasu daga cikin manyan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka yi bankwana da shi ciki har da nasarar kuɓutar da dalibai tare da malamansu 40 a jihar Oyo da ke Najeriya bayan sun shafe kwanaki 50 a hannun wadanda su kayi garkuwa dasu.
Faɗa ya sake ɓarkewa tsakanin Amurka da Iran bayan rugujewar yarjejeniya 11.07.2026 20:36
Shirin a wannan makon zai leka Gabas ta Tsakiya inda rikici ya sake barkewa tsakanin Amurka da Iran abin da ya kawo karshen yarjejeniyar fahimtar juna ta watanni uku da suka cimma a tsakaninsu. Bayan nan, shirin zai taɓo wasu mahimman lammuran da suka wakana a sassan yammacin nahiyar Afirka, musamman Najeriya, Nijar da Kamaru.
Bitar muhimman labarun da suka faru a mako daga Rfi hausa 04.07.2026 19:19
Ƙungiyar kare hakin bil Adam Amnesty International ta zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu da gaza kare ƴan Najeriya daga matsalolin ta’addanci da na tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya.........
Ana ci gaba da laluben dubban mutanen da suka ɓata a girgizar kasa a Venezuela 27.06.2026 20:36
Shirin na wannan mako zai soma ne daga Venezuela inda a yammacin ranar laraba girgiza ƙasa mai karfin maki 7 a ma’aunin celcius ta afkawa arewa maso yammacin ƙasar abin da ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali da alhini sakamakon rasa rayuka da dukiyoyi. Alkaluman hukumomi sun ce sama da mutum 900 ne suka rasayukansu kawo yanzu yayin da sama da 4,000 suka jikkata bayaga sama da 50,000 da suka yi ɓa...
Shirin yayi bita kan harin da aka kai filin jirgin saman Yamai da ma wasu labarai 20.06.2026 20:58
Shirin na wannan mako ya mayar da hankali kan bitar muhimman labaran da suka faru a sassan duniya cikin makon da muke bankwana da shi. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Oumarou Sanni.
Shirin ya fara da yadda aka buɗe bikin gasar cin kofin duniya a ƙasar Mexico 13.06.2026 20:13
Ranar Alhamis 11 ga wannan watan aka yi bikin buɗe gasar cin kofin duniya karo na 23, gasar da itace karo na farko da ƙasashe 3, Amurka da Canada da kuma Mexico su ka karbi baƙunci, sai dai kuma an gudanar da zanga-zanga a wasu sassa na birnin ƙasar. Ƙasashe 48 ne ke fafata domin samun zakaran bana kuma yan wasa 1,248 da alkalan wasa 52 za su jagoranci wasanni 104 da za'a kwashe kwanaki 39 ana y...
Yadda malaman makaranta suka gudanar da zanga-zanga kan rashin tsaro a Najeriya 06.06.2026 20:47
Shirin na wannan mako ya waiwaya halin da duniya ke ciki a fannin tsaro, rikice-rikice da kuma Diflomasiyya
Mahajjata kusan miliyan biyu sun gudanar da aikin Hajjin bana 30.05.2026 20:57
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Oumarou Sani, kamaar yadda aka saba ya yi bitar wasu daga cikin muhimman lamurran da suka wakana a makon da muka yi wa bankwana. Daga cikin muhimman batutuwan kuma akwai, yadda Musulmi kusan miliyan biyu suka samu nasarar gudanar da aikin Hajjin bana. Shirin ya kuma leƙa Yankin Gabas ta Tsakiya domin jin halin da ake ciki, musamman kan ƙoƙarin kawo...
RFI Hausa ta cika shekaru 19 da fara watsa labarai cikin harsshen Hausa 23.05.2026 20:26
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya fara ne da labarin cikar wannan tasha ta RFI Hausa shekaru 19 da kafuwa. Ranar alhamis 21 ga wannan watan gidan Rediyonku na RFI sashen Hausa ya cika shekara daya- daya har 19 da soma yada shirye-shiryensa . A shekara 2007 ne kwarrariyar ƴar Jarida Lanni Smith ta kirkiri sashen Hausa na RFI da aka yi wa matsuguni a birnin Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya. Kuma...
Yadda harin dakarun Najeriya ya kashe ɗimbin mutane a kasuwar Zurmi 16.05.2026 21:04
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' yana bita ne na mahimman labaran al'amura da suka wakana a makon da ya gabata. a wannan makon shirin ya soma ne daga Najeriya inda a farkon makon da ya wuce wani harin da dakarun Najeriya suka kai ta sama a kasuwar Tumfa ta karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamafara ya hallaka akalla mutum dari 100 tare da jikkata wasu da dama. Wannan harin da ke zaman mafi muni da dakarun...
Wasu daga cikin muhimman labaru a cikin makon daya gabata 09.05.2026 18:46
A wannan mako shirin zai mayar da hankali akan batun zabukan fidda gwani na Jam'iyar APC mai mulki a Najeriya da kuma rikicin cikin gida a sauran jam'iyun ƙasar suka ɗauki hankulan al'uma.
Yadda haɗakar ƙungiyoyi suka ƙaddamar da farmaki a sassan Mali 02.05.2026 20:45
Shirin ya soma daga ƙasar Mali inda a ranar 25 ga watan Afrilun da mu kayi ban kwana haɗakar mayakan Abzinawa na FLA da na ƙungiya masu ikirarin jihadi ta JNIM suka ƙaddamar da mugayen hare-hare a garuruwa huɗu na ƙasar da suka haɗa da Sevare, Kidal, Gao da kuma Kati. A garin Kati da ke zaman babban sansanin sojin ƙasar ƴan bindigar sun yi amfani da motoci shake da bama-bamai da manyan bindigogi...
Shirin mu zagaya duniya ya tattaro manyan labaran da suka faru a wannan mako 25.04.2026 20:32
Shirin mu zagaya duniya na wannan mako ya duba manyan labaran da suka faru cikin wannan mako, a sassan duniya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Oumarou Sani.
Makomar masu shiga tsakani,kan neman ƙulla yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran 18.04.2026 20:01
Mecece makomar ƙoƙari da masu shiga tsakanin, musamman Pakistan ke yi a kan neman ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran duba da tsaurin wasu ko da dama daga cikin sharuɗɗan da ɓangarorin biyu suka gabatarwa juna? Nura Ado Suleiman ke yi muku barka da sake haɗuwa cikin shirin Duniyarmu a Yau
Bitar Labaran mako: Iran ta amince da buɗe mashigin Hormuz ga jiragen kasuwanci 18.04.2026 19:50
Shirin Mu zagaya duniya tare da Oumarou Sani, kamar yadda ya ke zuwar muku a kowannen mako, a wannan karon ma ya yi bita ne kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke ban kwana da shi. Cikin jerin labaran da ke ƙunshe a wannan shiri, akwai yadda Iran ta amince da buɗe mashigin Hormuz bayan ƙulla yarjejeniyar tsagaita wutar kwanaki 10 tsakanin Isra'ila da Lebanon. Wannan da sauran manyan lab...
Liknande poddar
Replaio är ingen poddutgivare; programnamn, omslag och ljud tillhör sina upphovspersoner och distribueras via offentliga RSS-flöden