RFI Hausa

Ilimi Hasken Rayuwa

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’Adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.

Glöm inte att besöka poddens webbplats och stötta skaparen: www.rfi.fr

Skapare

RFI Hausa

Kategori

Education

Poddens webbplats

www.rfi.fr

Senaste avsnittet

17 nov 2026

Var kan du lyssna?

Poddar i appen Replaio Radio Kommer snart

Poddar kommer snart till appen. Installera nu och bli först med att uppleva ett helt nytt sätt att lyssna på poddar

Ladda ned på Google Play Installera gratis Android 10 mn+ nedladdningar · betyg 4,7+ iOS snart

Avsnitt

Yadda ƙungiyoyi masu zaman kansu ke baiwa ilimi tallafi a arewacin Najeriya 17.11.2026

Shirin wannan mako ya duba yadda ake cigaba da ƙoƙartawa ne wajen samar da tallafin karatu ta hannun ƙungiyoyi da kuma Gidauniyar da ake kafawa a wurare daban daban a yankin Arewacin Najeriya. Ga misali a waccan makon da ya gabata, gidauniyar Muktariyya da ke jihar Kano ta yaye ɗalibai kusan dubu 2000, waɗanda aka ilimantar a fannonin na’ura mai ƙwaƙalwa da kuma aikin Jarida bayan da suka kammala...

Yadda ake cigaba da samun tallafin karatu daga ƙungiyoyi a arewacin Najeriya 17.11.2026

Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan mako ya duba yadda ake cigaba da ƙoƙartawa ne wajen samar da tallafin karatu ta hannun ƙungiyoyi da kuma Gidauniyar da ake kafawa a wurare daban daban a yankin Arewacin Najeriya. Ga misali a waccan makon da ya gabata, gidauniyar Muktariyya da ke jihar Kano ta yaye ɗalibai kusan dubu 2000, waɗanda aka ilimantar a fannonin na’ura mai ƙwaƙalwa da kuma aikin Jari...

Yadda maye gurbin makaranta da yawon talla ke kassara rayuwar mata a Najeriya 10.11.2026

Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali, ya yi duba ne kan makomar da yarinya mace ke da ita idan aka hanata taɓa alƙalami, aka kuma bata kwanon tallace-tallace a yankunan karkara, yayin da a dai dai wannan lokaci da ake fuskantar matsin tattalin arziki, fargabar tsaro da wasu tsoffin al'adun gargajiya na ci gaba da raba 'yan mata samun damar shiga aju...

Yaɗuwar fasahar AI a harkar koyo da koyarwa 03.11.2026

A wannan makon, shirin namu ya yi duba ne ga guguwar fasahar zamani ta Artificial Intelligence ko kuma AI, da kuma yadda take sauya fasalin yadda ake koyo da koyarwa a makarantunmu. Ko wace makoma ce ke jiran azuzuwanmu na gaba a daidai lokacin da dalibai suka rungumi amfani da manhajoji irin su ChatGPT da Google Gemini? Gudunmowa ko kuma illar da fasahar AI ke da ita ga dalibai na ci gaba da dauk...

Matakin sallamar shugabannin makarantu sama da ɗari 4 a Nijar ya haifar da cece-kuce 27.10.2026

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya maida hankali ne kan matakin sallamar shugabannin makarantu sama da ɗari 4 da gwamnatin Nijar tayi, bayan da ɗaliban makarantun da suke jagoranta na firamari da kuma sakandare suka gaza samun makin da ake buƙata, lamarin da ya sanya ɗiga ayar tambaya kan ko wannan mataki zai haifar da ɗa mai ido ga ɓangaren ilimin ƙasar. Ku latsa alamar sauti don saura...

Yadda ƙarancin malamai ke barazana ga harkar ilimi a yankin Afrika 20.10.2026

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon zai kai ku kai tsaye zuwa cikin azuzuwan karatu na yankin Afirka ta Kudu da Sahara, yayin da rahoton baya-bayan nan na hukumar UNESCO ya girgiza duniya, inda ya bayyana cewa ana buƙatar ƙarin malamai miliyan Hamsin nan da shekara ta 2030 domin ceto ilimin duniya. Amma abin mamaki da kuma ban tsoro shi ne; kusan miliyan 15 na waɗannan malamai, a nan yankin...

Yadda ambaliyar ta kassara makarantu da dama a arewacin Najeriya 13.10.2026

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya duba halin da makarantu ke ciki ne a Tarayyar Najeriya sakamakon fuskantar matsalar ambaliyar ruwa a sassa daban daban na ƙasar.

Najeriya: saɓanin alƙaluma kan jihar da ɗalibanta ke kan gaba a cin jarabawar NECO 06.10.2026

A yau shirin zai leƙa Najeriya, inda aka samu saɓani ta fuskar alƙaluma a fannin ilimi, bayan fitar da sakamakon jarabawar ƙasa ta NECO na shekarar 2026, gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa jihar ce ta zo ta ɗaya a fadin ƙasar. Sai dai, wani bincike mai zurfi da jaridar Premium Times ta yi, ya musanta wannan iƙirari, inda ta ajiye jihar a matsayi na 31. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

Jigawa ta gabatar da tsarin rage barace-baracen Almajirai a jihar 29.09.2026

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan daɗaɗɗen batun nan na yaran da basa zuwa makaranta a Najeriya matsalar da har kawo yanzu ta ƙi ci taki cinyewa. Wani Rahoton UNICEF ya bayyana jihohin Kano da Jigawa da kuma Katsina a matsayin jihohin da ke da rinjayen yaren da basa zuwa Makaranta, inda a jumlace ƙasar ta yammacin Afrika ke da yara fiye da mi...

Gwamnatin Kano na shirin tilasta koyar da ilimin Kwamfuta a makarantun Firamare da Sakandare 22.09.2026

Shirin Ilimi Hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda majalisar dokoki jihar Kano ta bukaci a mayar da ilimin Kyamfuta dole a matakin makarantun Firamare da Sakandare. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

Gwamanatin Najeriya na shirin Horas da malamai sama da miliyan guda 15.09.2026

A yau shirin ya mayar da hankali ne kan matakin gwamnatin Najeriya kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka da ke shirin horas da malaman makaranta sama da miliyan guda. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

Gudunmowa ko kuma illar da shafukan sada zumunta ke yiwa al'adun Bahaushe 01.09.2026

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya duba irin yadda guguwar kafafen yada labarai da shafukan Internet ke barazana ga al'adun Hausawa da salon rayuwarsu. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

Yadda matasa suka ƙera jirgi maras matuƙi mai cin Kilomita 30 a Kano 18.08.2026

Shirin a wannan makon ya leka Kanon Najeriya, inda aka gano wani sabon tarihin bunkasar kimiyya da fasaha da matasan yankin ke jagoranta. Wannan gagarumar bajinta dai wani matashi Abubakar Waiya, wanda ya daɗe yana fafutukar kera na'urorin shawagi ne ya ƙera jirgi maras matuƙi domin taimakawa ɓangaren tsaro da kuma boma. Jirgin da ya kera a yanzu yana da ikon tashi da kansa har na tsawon kilomita...

Makomar ilimin yara a Kano na cikin halin rashin tabbas 14.07.2026

Shirin na wannan makon cigaba ne kan wanda muka gabatar a makon jiya, wanda ya gano yadda yara a wasu yankunan jihar Kano basa zuwa makaranta saboda yawon tallace-tallace domin tara kudin kayan ɗaki. Yayin da su kuma mazan suke diban yashi da fasa Dutse, da sunan wai su taso suna da sana'ar dogaro da kai. Yankunan da wannan lamari yafi kamari sun hada da Challawa, Kafin Maiyaki, Madobi, Gora, da K...

Yadda makomar ilimin yaran karkara a Najeriya ke cikin rashin tabbas 08.07.2026

A wannan makon, shirin ya nufi yankunan karkara, inda inda gine-ginen makarantu ke ci gaba da kasancewa a matsayin kango, kasancewar babu dalibai. A wasu wuraren kuma, azuzuwan sun zama fanko, yayin da matasa da yara suka ƙaurace wa shiga, ‘yan mata na fita birni yin tallace-tallace, su kuma samari na dambatawa da aikin ƙwadagon fasa duwatsu da ɗiban yashi. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sa...

Taron ƙaddamar da littafin tarihi na wani fitaccen matashi a Kanon Najeriya 30.06.2026

Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan taron ƙaddamar da sabon littafin tarihin nan mai suna 'Mu San Magabata', wanda fitaccen matashin marubuci Kabiru Ahmad Kwalli ya rubuta da aka gudanar a jihar Kanon Najeriya. Taron ya haɗa masana, sarakuna, da ɗandazon al'umma domin duba yadda za a ceto tarihin ƙasar Hausa da ke shirin bacewa. Wannan littafi, kamar yadda masana da dama suka bayyana,...

Yadda aka gudanar da taron manyan masana na duniya a birnin Lagos 23.06.2026

A wannan makon, shirin ya mayar da hankali ne kan babban taron ƙungiyar Lagos Studies Association karo na goma da aka kammala a ƙarshen mako, wanda ya saba haɗa masana, malaman jami'o'i, da masu bincike daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje domin tattauna halin da ilimi yake ciki a nahiyar Afirka cikin wannan ƙarni. Wannan taro, wanda aka kafa shi shekaru goma da suka gabata a birnin...

Yadda talauci ke hana ɗalibai cikar burinsu 09.06.2026

Shirin Ilimi hasken rayuwa na wanna Mako ya mayar da hankali ne kan yadda matsin tattalin arziki ke tilstawa ɗalibai haƙura da cikar burinsu na karatu, don kawai neman abin kaiwa baka, a kowacce rana. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsioyya Haruna.

Shirin kawar da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta na samun nasara a Jigawa 02.06.2026

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan makon ya sake waiwayar matsalar nan ce ta yawaitar yaran da ba za zuwa makaranta a arewacin Najeriya, batun da a fannin ilimi ke ci wa al’ummar yankin tuwo a ƙwarya.  Masu iya magana dai na cewa ‘mai rai ba ya rasa motsi’ domin kuwa duk da girman da wannan matsala ta yi a Najeriya musamman ma yankin arewacin ƙasar, akwai waɗanda suka tashi tsaye wajen ganin sun...

Ɗimbin matasa na haƙura da karatun boko saboda rashin tabbas kan samun aiki 19.05.2026

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda matasa a baya-bayan na ke haƙura da ilimin boko saboda shakku kan yiwuwar samun aikin yi. Matsalar rashin aikin yi bayan shafe tsawon shekaru ana karatu tare da kashe maƙuden kuɗaɗe ya sanya matasa da dama musamman waɗanda ba ƴaƴan wasu ba ajje tunanin karatu tare da mayar da hankali a kasuwanci da koyo...

An yafe wa ɗaliban da ke son shiga kwalejin ilimi rubuta JAMB a Najeriya 12.05.2026

A yau muna ɗauke da wani labari mai daɗi ga ɗaliban da ke sha’awar zama malamai da kuma masu son shiga Kwalejin Ilimi a faɗin Najeriya. Gwamnatin ta fitar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin sauƙaƙa wa ɗalibai hanyar neman ilimi da kuma ƙarfafa musu gwiwa ta fuskar kuɗi. Ministan Ilimi Tunji Alausa, ya sanar da cewa ɗaliban da ke son shiga Kwalejin Ilimi yanzu ba sai sun rubuta jarrabawar UTME ba....

Tasirin fasahar zamani wajen bunƙasuwar aikin jarida 05.05.2026

Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan bikin ranar ƴancin ƴan Jaridu ta duniya da ke gudana a kowacce ranar 3 ga watan Mayu, bikin da ke zuwa a wannan karon cikin wani yanayi da aikin na Jarida ke ganin koma baya. Akwai dai ƙorafe-ƙorafe daga sassa daban-daban kan yadda aikin  na Jarida ke fuskantar barazana kodayake masu ruwa da tsaki a wannan...

Yadda makarantun tsangaya suka fara gauraya karatun addini da na Boko don tafiya da zamani 28.04.2026

Shirin Ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda makarantun tsangaya da na Islamiyya suka fara gauraya karatun addini da na zamani a ƙoƙarin da suke yi na tafiya da zamani da kuma amun tallafi daga gwamnatoci da manyan ƙungiyoyi na duniya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2 22.04.2026

Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tamba...

Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2 21.04.2026

Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tamba...

Lyssna på podden Ilimi Hasken Rayuwa i Replaio

Radio och poddar i en och samma app - gratis och utan konto. Installera redan idag och missa inte premiären

Ladda ned på Google Play

Replaio är ingen poddutgivare; programnamn, omslag och ljud tillhör sina upphovspersoner och distribueras via offentliga RSS-flöden