RFI Hausa
Ilimi Hasken Rayuwa
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’Adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.
Wo hören?
Podcasts in der App Replaio Radio Bald verfügbarPodcasts kommen bald in die App. Installiere sie jetzt und erlebe als Erster einen ganz neuen Blick auf Podcasts
Folgen
Yadda makomar ilimin yaran karkara a Najeriya ke cikin rashin tabbas 08.07.2026 10:00
A wannan makon, shirin ya nufi yankunan karkara, inda inda gine-ginen makarantu ke ci gaba da kasancewa a matsayin kango, kasancewar babu dalibai. A wasu wuraren kuma, azuzuwan sun zama fanko, yayin da matasa da yara suka ƙaurace wa shiga, ‘yan mata na fita birni yin tallace-tallace, su kuma samari na dambatawa da aikin ƙwadagon fasa duwatsu da ɗiban yashi. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sa...
Taron ƙaddamar da littafin tarihi na wani fitaccen matashi a Kanon Najeriya 30.06.2026 10:02
Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan taron ƙaddamar da sabon littafin tarihin nan mai suna 'Mu San Magabata', wanda fitaccen matashin marubuci Kabiru Ahmad Kwalli ya rubuta da aka gudanar a jihar Kanon Najeriya. Taron ya haɗa masana, sarakuna, da ɗandazon al'umma domin duba yadda za a ceto tarihin ƙasar Hausa da ke shirin bacewa. Wannan littafi, kamar yadda masana da dama suka bayyana,...
Yadda aka gudanar da taron manyan masana na duniya a birnin Lagos 23.06.2026 10:00
A wannan makon, shirin ya mayar da hankali ne kan babban taron ƙungiyar Lagos Studies Association karo na goma da aka kammala a ƙarshen mako, wanda ya saba haɗa masana, malaman jami'o'i, da masu bincike daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje domin tattauna halin da ilimi yake ciki a nahiyar Afirka cikin wannan ƙarni. Wannan taro, wanda aka kafa shi shekaru goma da suka gabata a birnin...
Yadda talauci ke hana ɗalibai cikar burinsu 09.06.2026 10:04
Shirin Ilimi hasken rayuwa na wanna Mako ya mayar da hankali ne kan yadda matsin tattalin arziki ke tilstawa ɗalibai haƙura da cikar burinsu na karatu, don kawai neman abin kaiwa baka, a kowacce rana. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsioyya Haruna.
Shirin kawar da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta na samun nasara a Jigawa 02.06.2026 10:00
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan makon ya sake waiwayar matsalar nan ce ta yawaitar yaran da ba za zuwa makaranta a arewacin Najeriya, batun da a fannin ilimi ke ci wa al’ummar yankin tuwo a ƙwarya. Masu iya magana dai na cewa ‘mai rai ba ya rasa motsi’ domin kuwa duk da girman da wannan matsala ta yi a Najeriya musamman ma yankin arewacin ƙasar, akwai waɗanda suka tashi tsaye wajen ganin sun...
Ɗimbin matasa na haƙura da karatun boko saboda rashin tabbas kan samun aiki 19.05.2026 10:00
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda matasa a baya-bayan na ke haƙura da ilimin boko saboda shakku kan yiwuwar samun aikin yi. Matsalar rashin aikin yi bayan shafe tsawon shekaru ana karatu tare da kashe maƙuden kuɗaɗe ya sanya matasa da dama musamman waɗanda ba ƴaƴan wasu ba ajje tunanin karatu tare da mayar da hankali a kasuwanci da koyo...
An yafe wa ɗaliban da ke son shiga kwalejin ilimi rubuta JAMB a Najeriya 12.05.2026 9:58
A yau muna ɗauke da wani labari mai daɗi ga ɗaliban da ke sha’awar zama malamai da kuma masu son shiga Kwalejin Ilimi a faɗin Najeriya. Gwamnatin ta fitar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin sauƙaƙa wa ɗalibai hanyar neman ilimi da kuma ƙarfafa musu gwiwa ta fuskar kuɗi. Ministan Ilimi Tunji Alausa, ya sanar da cewa ɗaliban da ke son shiga Kwalejin Ilimi yanzu ba sai sun rubuta jarrabawar UTME ba....
Tasirin fasahar zamani wajen bunƙasuwar aikin jarida 05.05.2026 9:59
Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan bikin ranar ƴancin ƴan Jaridu ta duniya da ke gudana a kowacce ranar 3 ga watan Mayu, bikin da ke zuwa a wannan karon cikin wani yanayi da aikin na Jarida ke ganin koma baya. Akwai dai ƙorafe-ƙorafe daga sassa daban-daban kan yadda aikin na Jarida ke fuskantar barazana kodayake masu ruwa da tsaki a wannan...
Yadda makarantun tsangaya suka fara gauraya karatun addini da na Boko don tafiya da zamani 28.04.2026 9:55
Shirin Ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda makarantun tsangaya da na Islamiyya suka fara gauraya karatun addini da na zamani a ƙoƙarin da suke yi na tafiya da zamani da kuma amun tallafi daga gwamnatoci da manyan ƙungiyoyi na duniya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2 22.04.2026 10:00
Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tamba...
Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2 21.04.2026 10:00
Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke tamba...
Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu 14.04.2026 10:07
A arewacin Najeriya, shigar mata makarantun yaki da jahilci ya fara ne a matsayin wani yunkuri na inganta rayuwar iyali da kuma tarbiyyar yara, inda mata da dama sun fahimci cewa rashin ilimi na hana su taimaka wa yaransu wajen karatunsu na zamani da kuma kulawa da lafiyarsu. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.
Wani matashi ya yi nasarar ƙera jirgi marar matuƙi a jihar Kano 07.04.2026 10:14
Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon, ya yi dubi ne kan yadda wani matashi a jihar Kanon Najeriya ya ja hankalin jama’a, bayan ƙirƙirar jirgi maras matuƙi, daidai lokacin da matasan wannan ƙasa ke faɗi tashin yadda za su samo masu ɗaukar nauyin ayyukan fasahar da suke son cimmawa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruwa...........
Yadda wasannin na'ura kwamfita ke samun karɓuwa a tsakanin matasa 31.03.2026 9:46
Shirimmu na ilimi hasken rayuwa na wannan mako yayi karin bayani akan wasannin na’ura kwamfuta masu kama da gaske da aka fi sani da virtual reality a turance. Danna alamar sauti domin sauraron karin bayani........
Tasirin faɗowar wasu sinadarai daga sama a fagen kimiyya da fasaha 03.03.2026 9:57
Shirin "Ilimi Hasken Rayuwa" na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya yada zango ne a Jamhuriyar Nijar inda abaya-bayan nan aka rika samun fadowar wasu abubuwa daga sararin samaniya, lamarin da ke ci gaba da faruwa a sassan a kasar. A baya bayan ne dai wasu abubuwa suka fado daga sararin samaniya a kauyuka 5 daban daban a yankin Kornaka, da Dakwaro da suka hada da Dan Madi, Baushi, da sauransu,...
Ra'ayoyi sun banbanta kan amfani da fasahar AI wajen yin tiyata 24.02.2026 10:12
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako a wannan makon, ya mayar da hankali kan binciken da ya gano cewa shigar fasahar AI cikin fannin tiyata na haifar da wasu matsaloli masu kama da barazana ga rayuwar ɗan adam, kan haka ne ma muka zanta da masana a fannin kimiyya da kuma ɓangaren lafiya, inda muka jiyo ra’ayoyin mutane game da yadda wasu ke yarda AI ya duba lafiyarsu h...
Yadda satar jarabawa ke taka rawa wajen kassara ingancin ilimi a Najeriya 17.02.2026 10:00
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda satar jarabawa ke ƙoƙarin zama ruwan dare a makarantun sassan Najeriya, matsalar da ke ci gaba da illa ga ingancin ilimi a dukkan makarantu na ƙasar. Akwai zarge-zargen da ke nuna cewa wasu daga cikin jami'an hukumomin da ke kula da shirya jarabawa a matakai daban-daban na taimakawa wannan mummunar ɗabi...
Yadda masu larurar ji ke fama da ƙalubalen karatu a Najeriya 10.02.2026 9:59
Shirin na wannan mako ya ba da hankali ne akan yadda masu fama da larurar ji ke fama da ƙalubalen karatu a wasu sassan Najeriya.
Ana fuskantar koma bayan koyan harshen larabci a arewacin Najeriya 03.02.2026 9:52
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali ne kan dalilan da suka haddasa rashin koyon ingantaccen larabci tsakanin daliban sakandare a arewacin Najeriya, sabanin lokutan baya. A shekarun baya, alkaluma sun nuna cewa kusan kaso hamsin na larabcin da Dalibai ke koya suna samun sa ne a makarantun boko ba lallai sun sun halarci makarantun Arabiya, al’amarin...
Yadda satar jarabawa da cin hanci da rashawa ke kassara ɓangaren Ilimi a Kamaru 27.01.2026 9:59
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda wani bincike can a Jamhuriyyar Kamaru ya gano yadda satar Jarabawa da cin hanci da rashawa ke mummunan tasiri a ɓangare ilimin ƙasar. Matsalar ta cin hanci da rashawa kai tsaye ta yi mummunar illa ga yanayin ɗaukar malamai aiki da gina makarantu ko kuma samar da ci gaba a ɓangaren na Ilimi, yayinda a...
Makomar karatu a yankin arewacin Najeriya cike da barazanar ƴanbindiga 20.01.2026 9:58
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan makomar karatun ɗalibai a makarantun Najeriya musamman yankin arewaci mai fama da matsalolin tsaro, dai dai lokacin da aka koma sabon zangon karatu Iyaye na cike da fargaba kan tsaro a makarantu. Makwanni gabanin tafiya hutun zangon da ya gabata cikin watan Nuwamban bara ne, hare-haren ƴan bindiga suka tilas...
Kashi na biyu kan yadda sabuwar manhajar fassarawa da lissafa haraji ke amfani a Najeriya 06.01.2026 9:49
A kashi biyu na shirin ilimi hasken rayuwa, mun ɗora kan sabuwar manhajar fassarawa da da sauƙaƙa lissafin karɓar haraji. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Faruk Yabo.
Farfesa Aminu Bello ya samar da manhaja mai sauƙaƙa lissafin haraji a Najeriya 30.12.2025 9:59
Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya tattauna da Farfesa Aminu Bello Usman daga Birtaniya, ɗan jihar Kano da ke tarayyar Najeriya, wanda ya ƙirƙiri wata Manhaja da za ta taimaka wa mutane wajen sauƙaƙa musu lisaffin hada-hadar kuɗaɗe musamman ma na haraji. Wani abin ban sha’awa dangane da Manhajar da aka fi sani da Software a Turance, shi ne yadda wannan manhajar ta ƙunshi harsuna biyar. Danna...
Akwai bukatar samarwa masu buƙata ta musamman ayyukan yi domin dogaro da kai 23.12.2025 9:59
Mutane da suka tsinci kansu a cikin masu buƙata ta musamman sakamakon nau’ikan nakasar da suka fama da ita sun share shekaru suna fuskantar giɓi babba a muhimman fannonin rayuwa daban daban, ciki kuwa har da samun guraben ayyukan yi ko da kuwa a ce sun yi katarin tsallake shingen samun ilimi, matsalar da ta fi ƙamari a ƙasashe masu tasowa ciki har da na Nahiyar Afrika. Mutane da suka tsinci kansu...
Ähnliche Podcasts
Replaio ist kein Herausgeber von Podcasts; die Namen der Sendungen, Cover und Audioinhalte gehören ihren Autoren und werden über öffentliche RSS-Feeds verbreitet