RFI Hausa

Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

News HA ↓ Episoade: 39

Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma da ke sauraren Shirye shiryen RFI Hausa daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalin’ariziki, al’adu da dai sauransu…

Vizitează neapărat site-ul podcastului și susține-i creatorul: www.rfi.fr

Autor

RFI Hausa

Categorie

News

Site-ul podcastului

www.rfi.fr

Cel mai nou episod

29 sept. 2026

Unde asculți?

Podcasturi în aplicație Replaio Radio În curând

Podcasturile ajung în curând în aplicație. Instaleaz-o acum și fii primul care descoperă o abordare complet nouă a podcasturilor

Descarcă din Google Play Instalează gratuit Android aproape 10 mil. descărcări · nota 4,8 iOS în curând

Episoade

Ra'ayoyin masu sauraro kan ƙaryata zargin kisan Kiristoci da MDD ta yi 23.06.2026

Tawagar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tura zuwa Najeriya don gudanar da bincike a game da zargin kisa, yin garkuwa da mutane da kuma tilasta wa wasu barin muhallansu saboda dalilai na addini, ta ce wannan ba gaskiya ba ne. Jagorar tawagar Farfesa Nazila Ghanea, a ƙarshen ziyarar gani da ido ta kai a ƙasar, ta ce mutane na yin waɗannan zarge-zarge ne saboda gazawar gwamnati wajen ba su kariya da ku...

Ra'ayoyin masu sauraro kan taƙaddamar ƴan siyasa a kotunan Najeriya 18.06.2026

Yayin da ake shirin gudanar da zaɓuka cikin watan Fabarairun shekaru mai zuwa a Najeriya, wani abu da ke faruwa shi ne taƙaddamar ƴan siyasa a gaban kotunan ƙasar. Kusan a kowane mako, za a ji cewa kotu ta yanke hukunci kan jam’iyyun siyasa, lamarin da ke iya nisantar da su daga tsayawa takara a waɗannan zaɓuka. Wannan ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku akai. Latsa alamar sauti...

Ra'ayoyin masu sauraro kan ganawar shugabannin Nijar da Benin 03.06.2026

Nijar da Jamhuriyar Benin sun amince da yin aiki a tare don yaƙi da ta’addanci da ke addabar ƙasashen biyu na Yammacin Afirka, yayin da a hannu ɗaya suka kafa wani kwamitin da zai bayar da shawarwari cikin kwanaki 15  a game da yadda za a sake buɗe iyakokin ƙasashen da ke rufe yau kusan shekaru uku.    An dai cimma wannan matsaya ce a ziyarar da shugaban Benin Romuald Wadagni ya kai a birnin Yamai...

Saƙon gaisuwar sallah daga masu bibiyar shafin RFI 27.05.2026

A yau take Sallah Babba! Ranar da ɗaukacin Musulmi a faɗin duniya ke murnar zagayowar Sallar layya. Wannan biki na zuwa ne a daidai lokacin da lamura suka yi tsauri, musamman ta ɓangaren tattalin arziƙi. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.

Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta 21.05.2026

Kamar yadda aka saba a kowace ranar alhamis, shirin Rayuwata na bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan maudu'an da shirin ya tattauna a wannan mako. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

Ra'ayoyin masu sauraro kan yarjejeniyar Nijar da kamfanin ƙasar China 20.05.2026

Bayan share kusan shekara ɗaya ana taƙaddama tsakanin gwamnatin Nijar da kamfanin mai na CNPCN na ƙasar China, ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniya da ke bai wa Nijar damar ƙarin jari da kuma faɗa-a-ji a harkar man fetur. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

Ra'ayoyin masu sauraro kan giɓin kuɗaɗe da WHO ke fuskanta 19.05.2026

Yanzu haka ƙasashe masu tasowa na ci gaba da ƙoƙarin cike giɓin da aka samu bayan da Donald Trump ya janyewa tallafin da Amurka ke bai wa Hukumar Lafiya don yaƙi da wasu curutuka a duniya. A jawabinsa gaban Taron Hukumar Lafiya WHO da ke a birnin Geneva, shugaban Ghana John Dramani Mahama ya ce ya kamata Afirka ta samar da tsarin kula da lafiyar al’ummarta a maimakon barin lamarin a hannun hukumar...

Ra'ayoyin masu sauraro kan ƙara yawan jihohi a Nijar 14.05.2026

Gwamnatin Nijar ta fitar da wani daftari da ke ƙara adadin jihohi zuwa 19 ta hanyar ƙirƙiro sabbin 11 a maimakon 8 da ake da su a kasar yau kusan shekaru 30 kenan. Gwamnatin ta ce za ta ƙirƙiri sabbin jihohi da kuma gundumomi ne domin samar da ci gaba da ta hanyar ƙara matso da jama’a zuwa kusa da hukuma. Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti d...

Ra'ayoyin masu sauraro kan taron Afrika da Faransa da aka kammala a Kenya 13.05.2026

A taron Afirka da Faransa da aka kammala jiya talata a ƙasar Kenya, Faransa ta sanar da shirin saka jarin Euro bilyan 23 don ƙarfafa kasuwanci tsakanin ɓangarorin biyu. Shugaba Emmanuel Macron ne ya sanar da haka, yana mai cewa daga yanzu ɓangarorin biyu za su gudanar da mu’amala ce irin ta ba ni gishiri in ba ka manda a maimakon bai Afirka tallafi kamar yadda ake yi a baya. Latsa alamar sauti don...

Ra'ayoyin masu sauraro kan batutuwa mabanbanta 08.05.2026

Yau juma'a sashen Hausa na RFI na bai wa masu sauraro damar bayyana ra'ayoyinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya, kama daga fannin siyasa, tattalin arziƙi, tsaro, da dai sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabanbanta...

Nijar ta bayar da umarnin garƙame masallatai bayan kammala sallar farilla 05.05.2026

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayar da umarnin garƙame masallatai, da zarar an kammala sallolin farilla, tare da tabbatar da cewa an hana jama’a kwana a wuraren ibada ciki har da makarantun Islamiyya. Tuni ministan cikin gida ya sanar da gwamnoni, shugabannin ƙananan hukumomi da sarakunan gargajiya matakin a hukumance, saboda dalilai na tsaro. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

Ra'ayoyin masu sauraro kan ranar ƴancin aikin jarida ta duniya 04.05.2026

Rahoton shekara-shekara da ƙungiyar kare ƴan jarida ta Reporters Without Borders ta fitar, na nuni da cewa an samu gagarumin koma-baya ta fannin ƴancin aikin yaɗa labarai a cikin ƙasashe 100 daga cikin 180 na duniya. RSF ta fitar da rahoton ne a jajibirin ranar ƴancin aikin jarida da ake gudanarwa ranar 3 ga watan Mayun kowace shekara. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

Ra'aoyin Masu Saurare na ranar Jumma'a 1 ga watan Mayun 2026 01.05.2026

A kowace ranar Jumma'a filin ra'ayoyin 'Masu Sauraro kan bada damar tsokaci kan bututuwa da ke ci wa mai sauraro tuwo a kwarya. Ku latsa alamar sautin domin jin wasu daga cikin ra'ayoyin da wasu masu sauraro suka aiko mana.

Ra'ayoyin masu sauraro kan dokar zaɓen Najeriya ta 2026 30.04.2026

A Najeriya, yayin da ƙasar ke ci gaba da ɗaura ɗamarar tunkarar zaɓukan gama-gari a shekara mai zuwa, yanzu haka ana ci gaba da mahawara dangane da abubuwan da ke ƙunshe a dokar zaɓe ta 2026 wadda a ƙarƙashinta ne komai zai gudana. Dokar dai na ƙunshe da sauye-sauye da dama saɓanin waɗanda aka sha jarrabawa a zaɓukan da suka gabata. Saboda haka za mu so jin ra’ayoyinku a game da alfahu ko rashin a...

Ascultă podcastul Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare în Replaio

Radio și podcasturi într-o singură aplicație - gratuit și fără înregistrare. Instaleaz-o azi și nu rata lansarea

Descarcă din Google Play

Replaio nu este editorul podcasturilor; numele emisiunilor, coperțile și materialul audio aparțin autorilor lor și sunt distribuite prin fluxuri RSS publice