RFI Hausa

Bakonmu a Yau

News HA ↓ Episoade: 82

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Vizitează neapărat site-ul podcastului și susține-i creatorul: www.rfi.fr

Autor

RFI Hausa

Categorie

News

Site-ul podcastului

www.rfi.fr

Cel mai nou episod

20 nov. 2026

Unde asculți?

Podcasturi în aplicație Replaio Radio În curând

Podcasturile ajung în curând în aplicație. Instaleaz-o acum și fii primul care descoperă o abordare complet nouă a podcasturilor

Descarcă din Google Play Instalează gratuit Android 10 mil.+ descărcări · nota 4,7+ iOS în curând

Episoade

Hon Sama’ila Mohammed kan saida hannun jarin matatar man Dangote 09.09.2026

A ranar Litinin da ta gabata, matatar man fetur ta Ɗangote ta dasa ɗambar shirinta na shiga kasuwar hada-hadar hannayen jari, waɗanda shugaban rukunin kamfanonin na Ɗangote, Alhaji Aliko, ya ce ana iya mallakar aƙalla guda 10 da ƙasa da Naira dubu 6. Kan wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da Honorable Sama’ila Mohammed, masanin tattalin arziƙi a Najeriya, wanda ya yi tsokaci kan tasiri da kuma y...

Tattaunawa da Datective Auwal Bala kan baiwa MOPOL damar yaƙi da ta'addanci 08.09.2026

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta sanar da tsaurara matakan yaƙi da ta’addanci da ya addabi ƙasar ta hanyar shigar da ƴan sandan kwantar da tarzoma cikin aikin fatattakar ƴan ta’adda. Da yake jawabi yayin wani rangadi da ya kai barikokin ƴan sanda a jihar Lagos, babban sufeton ƴan sandan ƙasar Tunji Disu ya ce, daga yanzu za’a sanya jami’an cikin aikin gadan-gadan. Game da wannan batu Rukayya Abba K...

Dr Salissou Ibrahim Yahaya kan amincewa da yi wa taswirar duniya gyara 07.09.2026

Majalisar Ɗinkin Ɗuniya ta amince da ƙudirin da ke bayar da damar yi wa taswirar duniya gyara, bayan da ƙasashen Afirka suka gabatar da ƙorafin cewa wadda ake amfani da ita a yau na ɗauke da kura-kurai tare da tauye faɗin nahiyar na haƙiƙan. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Dr Salissou Ibrahim Yahaya, malami kuma masani kimiyar taswirar duniya a Jami’ar Damagaram da ke Jamhuriyaer Nijar, wan...

Martani kan iƙirarin shugaban Najeriya game da ciyar da arewacin ƙasar gaba fiye da kowanne yanki 03.09.2026

A Najeriya iƙirarin da shugaba Bola Tinubu ya yi cewa yankin arewacin ƙasar ce ta fi cin gajiyar manufofinsa na  sauye-sauyen tattalin arziƙi ya janyo suka daga  masu ruwa da tsaki, inda ƙungiyar al’ummar Arewacin ƙasar da wasu ƙungiyoyin yankin suka caccaki kalaman, su na mai cewa a maimakon cigaba, manufofin shugaban sun mayar da yankin arewa cibiyar talauci. Akan haka ne Michael Kuduson ya tatt...

Dr Ibrahim Modibbo kan tattaunawar samar da ɗan takara ɗaya da zai kara da Tinubu 01.09.2026

Wakilan Jam’iyyun adawa a Najeriya sun gana a jiya Litinin, inda suka tattauna kan yiwuwar ƙulla yarjejeniyar haɗa ƙarfi wajen mara wa ɗan takara guda baya a zaɓen shugabancin ƙasar da ke tafe a 2027. Wannan taro ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin G-100, ƙungiyar wasu fitattun ƴan Najeriya da ke ƙoƙarin haɗa gamayyar jam’iyyun adawa. Don jin ƙarin bayani kan abinda aka cimma, Nura Ado Suleiman ya...

Dr Kabiru Adamu kan boren sojoji a Jamhuriyar Nijar 31.08.2026

Ƙura ta lafa a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar bayan da wasu sojoji  suka kai hari filin jirgin sama da fadar shugaban ƙasar, a wani bore da suka fara tun cikin daren Juma’a zuwa wayewar safiyar Asabar, lamarin da ya haifar da musayar wuta da fashe-fashe na tsawon sa'o'i. Rahotanni na cewa dakarun hayar Rasha sun taimaka wajen daƙile boren na ƙananan sojoji da suka kaucewa fagen daga domin fa...

Muhd Makiga kan maƙudan kuɗin fansar da ƴan ta'adda ke samu a Najeriya 28.08.2026

A Najeriya masana da wasu ƴan ƙasar na ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan rahoton cibiyar binciken tsaro ta SBM Intelligence, da ya nuna cewar ƴan ta’adda sun karɓi kuɗaɗen fansar da yawansu ya kai Dala miliyan 5.8, daidai da kusan naira biliyan 8 cikin shekara guda. Rahoton, ya ce ƴan ta’addan sun ƙarbi kuɗaɗen ne a tsakanin watan Yulin shekarar bara ta 2025, da kuma Yunin bana, kuma mayaƙan Boko H...

Isa Sunusi kan yadda ƴan siyasa suka fara kalaman tinzira al'umma 27.08.2026

Yayin da aka kada gangar siyasar Najeriya, ana zargin wasu ƴan siyasar da kalaman tinzira tashin hankali, abinda ke barazana ga zaman lafiyar jama'a. Bayan Sanatan jihar Osun da ya buƙaci a kashe magoya bayan jam'iyyar adawa, an jiyo shugaban karamar hukumar Kuje dake Abuja na kira ga wadanda basa goyan bayan APC da su fice daga yankin. Tuni wannan ya fara jefa fargaba a tsakanin jama'a. Bashir Ib...

Kasuwar hada-hadar hannayen jarin Najeriya ta zama mafi ƙarfi a duniya 10.07.2026

Cikin makon nan, kasuwar hada-hadar hannayen jarin Najeriya, ta kafa tarihin zama mafi ƙarfi gami da bunƙasa a faɗin Duniya, bayan zarta mai riƙe da kambun a baya bayan nan, wato takwararta ta Korea ta Kudu.   Rahoton kamfanin Bloomberg ya nuna cewa, zuwa yanzu Kasuwar ta Najeriya ta samu tagomashi ne da kaso 67 cikin 100, yayin da ta Korea ta Kudu ke da kaso 66. Domin jin ƙarin bayanin kan dalila...

Najeriya na neman goyon bayan China wajen yaƙi da ta'addaci - Bello Dambazau 09.07.2026

Najeriya na tattaunawa da China wajen ganin ta samu goyon bayan da ya dace a fasahar zamani da kuma makamai domin shawo kan matsalolin tsaro da suka addibi ƙasar. Sabon jakadan Najeriya a ƙasar China Janar Abdurrahman Bello Dambazau mai ritaya ya bayyana haka a tattaunawar da suka kayi da Bashir Ibrahim Idris. Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar.

Dakta Sani Gambo kan taron ƙasashen ƙungiyar AES da Rasha 08.07.2026

A wannan Laraba ake fara taron tuntuɓa tsakanin ƙasashen ƙungiyar AES wato Mali, Nijar da Burkina Faso da kuma  ƙasar Rasha a gefe guda a Yamai fadar gwamnatin  Nijar, inda ake sa ran za su tattauna batutuwan da suka shafi tsaro, tattalin arziki da kuma makamashi. Wannan ne karo na biyu da ake gudanar taron bayan makamancinsa da aka yi a birnin Moscow na Rasha a watan Afrilun 2025, kuma ya na zuwa...

Ɗambarwar Naira Triliyan 8 ta girgiza gwamnatin Bola Tinubu 06.07.2026

A Najeriya, daidai lokacin da ake neman sanin matsayin shugaba Bola Tinubu dangane da zargin kafawa da kuma tafiyar da wata ma’aikatar jabu a ƙarƙshin gwamnatin tarayya, sai kuma ga wasu bayanai daga Asusun Lamuni na Duniya IMF da ke cewa gwamnatin ta kashe sama da Naira triliyan 8 waɗanda sam kasafin kuɗin ƙasar bai san da su ba. Shiga alamar sauti  don sauraron cikakkiyar hira da Abdoulklarim Ib...

Isa Sanusi kan rahoton Amnesty da ke zargin gwamnatin Najeriya gaza kare al'umma 03.07.2026

Ƙungiyar Amnesty International a Najeriya ta zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu da gaza kare ƴan Najeriya daga matsaloli na ta’addanci da na tattalin arziki da ake fama da shi. Ruƙayya Abba Kabara ta tattauna da daraktan Amnesty a Najeriya, Malam Isa Sanusi kan rahoton nasu. Latsa alamar sauti don sauraren sa....

Dakta Isa Abdullahi akan soke lasisin wasu ƙananan bankuna da aka yi a Najeriya 02.07.2026

Babban Bankin Najeriya na CBN ya sanar da soke lasisin wasu ƙananan bankuna 46 saboda saɓawa ƙa'idar aiki. Waɗannan bankuna sun haɗa da guda 12 a Kano da wasu takwas a Lagos, baya ga wasu ɗaiɗaikun jihohi. Domin sanin tasirin wannan mataki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Isa Abdullahi, masanin tattalin arziki, kuma ga yadda zantawar su ta gudana a kai. 

Muhammad Sani Sufyan kan watsin Kotu da buƙatar Trump game da ƴancin zama ɗan ƙasa 01.07.2026

Kotun Ƙolin Amurka ta yi watsi da buƙatar  shugaba Donald Trump ta soke dokar da ke bai wa waɗanda aka haifa a ƙasar ƴancin zama ƴan ƙasa kai-tsaye. Kotun ta tananata cewa, duk wanda aka haifa a Amurka na da ƴancin mallakar shaidar zama ɗan ƙasa. Trump ya ruga kotun kolin ne bayan rashin nasara a ƙananan kotunan ƙasar. Kan haka, Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna da Muhammad Sani Sufyan, mazaunin...

Rakiya Sa'idu akan cika wa'adin korar baƙi a Afirka ta Kudu 30.06.2026

An shiga wani yanayi na fargaba da tsananin tashin hankali a Afirka ta Kudu, yayin da yau wa’adin ranar 30 ga watan nan na Yuni ke cika, game da zanga-zangar da wasu ƙungiyoyin ƙyamar baki suka shirya don tilasta wa baƙin da ba su da takardu barin ƙasar.   Ko da yake hukumar ’yansandan ƙasar ta ce ta tura ɗimbin jami'an tsaro zuwa yankunan da ake sa ran za su fuskanci tashin hankali, kamar su Pret...

Soumaila Amadou akan rikicin diflomasiyyar Faransa da Burkina Faso 29.06.2026

Mahukunta a Faransa, sun ce yanzu haka suna kan yin nazari domin ɗaukar matakin da ya dace bayan da Burkina Faso ta sanar da katse duk wata hulɗar diflomasiyya da  ƙasar, inda ta zargi Faransa da taimaka wa masu tayar da ƙayar baya da ke neman wargaza sha’anin tsaro da na zamantakewar al’ummarta. A game da wannan batu ne Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Malam Soumaila Amadou, wanda ke bin di...

CP Muhammed Indabawa kan samar da ƴan sandan jihohi a Najeriya 26.06.2026

A Najeriya ra’ayoyi sun sha bambam a tsakanin al’umma dangane da shirin bai wa jihohi damar kafa rundunar ƴansanda don inganta sha’anin tsaro a ƙasar. Tuni dai Majalisun Tarayyar Ƙasar biyu suka amince da daftarin dokar da ke bayar da damar ɗaukar wannan mataki, kamar dai yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta buƙata. Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da tsohon Kwamishinan Ƴansanda CP Muhammed Ind...

Baba Usman Ngelzerma,kan tsangwamar da Fulani ke fuskanta a kudancin Najeriya 24.06.2026

Fulani makiyaya a Najeriya sun koka dangane da irin tsangwama da kuma barazanar da suke fuskanta a kudancin ƙasar, sakamakon matsalar tsaro da kuma garkuwa da mutane da ake fama da shi. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban ƙungiyar Miyetti Allah, Baba Usman Ngelzerma. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakkiyar tattaunawar.

Dakta Abdulhakeem Garba kan cikar Birtaniya shekaru 10 da ficewa daga EU 23.06.2026

Yau ake cika shekaru 10 da ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar ƙasashen Turai domin cin gashin kan ta wajen gudanar da harkokin mulki da kuma kasuwancin ta ba tare da sanya hannun ƙungiyar EU ba. Bayan share shekaru ana tattaunawa, Birtaniya ta fita a hukumance a ranar 31 ga Janairun 2020. Wannan mataki na Birtaniya ya canza taswirar siyasa, tattalin arziki, da dangantakar kasuwanci ta duniya ba...

Alhassane Intchinicar kan sharuɗɗan da Nijar ta kafa kafin buɗe iyaka da Benin 22.06.2026

An fara tattaunawa tsakanin Benin da kuma Jamhuriyar Nijar da nufin sake buɗe iyakar ƙasashen biyu, sai dai mahukuntan birnin Yamai sun gindaya sharuɗɗa biyu kafin sake buɗe iyakar. Ministan cikin gida kuma jagoran tawagar Nijar a tattaunawar, ya ce na farko dole ne a ƙulla yarjejeniyar tsaro wadda a ƙarƙashinta ba ɗaya daga cikin ƙasashen biyu da za ta bari a yi amfani da ita domin kai wa ɗaya ha...

Gobe za a gudanar da zaɓen gwamna a jihar Ekiti ta kudancin Najeriya 19.06.2026

Gobe ne hukumar zaɓe a Najeriya ke gudanar da zaɓen gwamnan Ekiti da ke yankin kudanci, inda ƴan takara 13 za su fafata. Ana kallon wannan zaɓen a matsayin zakaran gwajin dafi ga sabon shugaban hukumar zaɓen Farfesa Joash Amiputan. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da mai magana da yawun hukumar Hajiya Zainab Abubakar. Latsa alamar sauti don sauraren yadda zantawarsu ta gudana...

Amnesty ta ci gaba da matsa wa gwamnatin Najeriya lamba kan ceto ɗalibai 18.06.2026

Ƙungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Amnesty International ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta dauki matakai na gaggawa don kare dalibai da kuma ceto wadanda har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutane. Ƙungiyar ta jaddada cewa gazawar hukumomi wajen kawo ƙarshen hare-hare da sace-sacen dalibai na nuna cewa rayuwar yara na cikin matsananciyar barazana. Ƙungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya dauki ma...

Akwai takaici yadda wasu ke son haddasa gaba tsakanin ƙabilu a Plateau-Joyce Ramnap 17.06.2026

Gwamnatin Jihar Filato da ke Najeriya ta bayyana matuƙar damuwar ta dangane da yadda ta ce wasu na amfani da hukuncin wata kotu dangane da baiwa wasu Hausawa takardar zama ƴan ƙasa domin haifar da tashin hankali a tsakanin al'ummar da suka kwashe shekaru da dama su na zaman lafiya da juna. Gwamnatin ta ja kunnen al'umma inda ta ce waɗanda ba su gamsu da hukuncin ba na da hurumin ɗaukaka ƙara kamar...

Dakta Abubakar Sadiq kan matakin rushe wasu jam'iyyu siyasa a Najeriya 16.06.2026

Wata babbar kotu a Najeriya, ta bai wa hukumar zaɓe ta INEC umarnin soke wasu jam'iyyun adawa har guda biyar, saboda saɓawa dokokin zaɓen shekarar 2023 na ƙasa samun kashi 25 na ƙuri'un da aka kaɗa. Jam'iyyun sun haɗa da ADC da AA da APP da ZLP da Acoord Party. Tuni wannan hukunci ya haifar da mahawara da kuma zargin yunƙrin haa 'yan adawa shiga zaɓe mai zuwa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da D...

Ascultă podcastul Bakonmu a Yau în Replaio

Radio și podcasturi într-o singură aplicație - gratuit și fără înregistrare. Instaleaz-o azi și nu rata lansarea

Descarcă din Google Play

Replaio nu este editorul podcasturilor; numele emisiunilor, coperțile și materialul audio aparțin autorilor lor și sunt distribuite prin fluxuri RSS publice