RFI Hausa
Wasanni
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Tawagogin ƙasashen Afirka 7da aka yi waje dasu bayan sun tsallaka zagayen ƴan 32 06.07.2026 10:00
Bayan nasarar da tawagogin ƙasashen Afrika 9 suka yi na kaiwa zagayen ƴan 32 a gasar lashe kofin duniya, wani lamari da ya sanya nahiyar ta kafa tarihin samun yawan wakilai a wannan zagaye, sai dai kuma ana iya cewa murna ta koma ciki domin dai tuni aka yi waje da 7 daga cikin 9. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........
Irin rawar da ƙasashen Afirka suka taka a gasar Kofin Duniya ta 2026 29.06.2026 10:00
Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda irin rawar da ƙasashen Afrika suka taka a wasannin rukuni a gasar lashe kofin duniya. A ƙarshen mako ne dai aka kammala wasanni rukuni, abinda ke nuna cewar an buga wasanni 72 daga cikin 104 da za a yi a wannan gasa. Sakamakon waɗannan wasani da aka yi ya nuna cewar anyi waje da tawagogin ƙasashe 16 daga cikin 48 dake fafatawa a gasar, inda ƙasashe 32...
Muhimman abubuwan da suka faru a Gasar lashe Kofin Duniya kawo yanzu 22.06.2026 10:00
Shirin a wannan mako zai yi duba ne kan wasu muhimman abubuwan da suka faru a gasar lashe kofin duniya ciki har da karawar da Cote d’Ivoire ta sha kashi a hannun Jamus. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.
Dalilan da ya sa ƴan Afirka suka juyawa tawagar Afirka ta Kudu baya 15.06.2026 9:59
Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako tare da Khamis Saleh ya yi duba kan irin wainar da ake toyawa a gasar nema cin kofin duniya da ƙasashen Canada da Mexico da kuma Amurka ke karbar bakunci. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shiri........
Shiri na musamman kan shirye-shiryen fara gasar lashe kofin duniya 08.06.2026 10:00
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan gasar lashe kofin duniya da za a fara a wannan makon. Ita dai wannan gasa ta lashe kofin duniya da aka faro a shekarar 1930, Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ce ke shiryata duk bayan shekara 4, sai dai a shekarun 1942 da kuma 1946 an samu tsaikon gudanar da gasar sakamakin yaƙin duniya na biyu. Bayan kammala gasar da ƙasar Qatar ta karɓi b...
PSG ta lashe Gasar zakarun ta Turai a karo na biyu 01.06.2026 10:00
Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako tare da Khamis Saleh ya yi duba kan yadda aka gudanar da wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai tsakanin ƙungiyar PSG da kuma Arsenal, inda PSG ɗin ta samu nasarar lashe gasar a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka ta shi 1-1. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Sharhi kan nasarar lashe gasar Premier League da Arsenal ta yi a bana 25.05.2026 10:00
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya yi duba ne kan nasarar lashe gasar Firimiyar Ingila da Arsenal ta yi a kakar wasan bana, bayan kwashe tsawon shekaru 22 batare da tayi tozali da kofin ba. A Lahadin nan ne aka miƙawa Arsenal kofin bayan buga wasanta na ƙarshe a gasar a wannan kaka tsakaninta da Cystal Palace, inda aka tashi 2-1. Tun kafin wasan na jiya ne dai aka nasarar da Arsenal a matsa...
Yadda aka lashe mafi akasarin gasannin lik-lik na nahiyar Turai 18.05.2026 9:53
Shirin Duniyar Wassani a wannan lokacin yayi duba ne kan yadda aka lashe mafi akasarin gasannin lik-lik na nahiyar Turai, in banda gasar Firimiyar Ingila. Barcelona ta lashe gasar La liga a Spain, a Inter Milan ta lashe gasar Serie A na Italiya, ita kuwa Bayern Munich ta ɗauke kofin Bundesliga na ƙasar Jamus, yayin da PSG ta lashe gasar League 1 ta Faransa. A yanzu haka dai gasar Firimiyar Ingila...
Yadda aka gudanar da gasar Super 4 ta a Najeriya 11.05.2026 9:59
A ranar juma’ar data gabata ne dai aka kammala gasar gasar Super 4, wacce aka fafata tsakacin ƙungiyoyi 4 da suka haɗa da Sporting Lagos da Inter Lagos da Ranchers Bees ta Kaduna sai kuma Doma United, da suka zama zagaru a rukunoninsu na gasar NNL, gasa ta biyu mafi daraja a Najeriya. An gudanar da gasar ne a yanayin yadda ake gudanar da gasar lik-lik, inda kowa ya kara da kowa ganin cewa kowaccen...
Matsalolin da suka dabaibaye ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars 04.05.2026 9:59
A wannan mako shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali ne kan halin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars ke ciki, wanda ya haddasawa ƙungiyar gagarumin koma baya. Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars, ta kasance guda cikin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar ƙwararru da ake ji da su a shekarun baya daga yankin Arewacin Najeriya, wadda ta shafe tsawon shekaru tana gwa...
NPFL: Saura mako 3 a ƙarƙare amma har yanzu ba a san zakaran bana ba 27.04.2026 10:00
Shirin awannan mako ya leƙa gasar Firirmiyar Najeriya ne wadda ke gab da ƙarƙarewa, amma kuma haryanzu ba a san maci tuwon ba. Yanzu haka dai an kammala wasannin mako na 35 a gasar Firimiyar Najeriya, wadda ya rage mako 3 kacal a kammala gasar a kakar wasa ta bana, amma sai dai haryanzu ƴar manuniya bata nuna ƙungiyar da za ɗauki gasar ba tsakanin ta saman teburi harzuwa wadda take a mataki na huɗ...
Sharhi kan wasannin dab dana kusa dana ƙarshe a gasar zakarun Turai 20.04.2026 10:00
A makon daya gabata ne aka kammala wasannin zagayen dab dana kusa da na ƙarshe na gasar zakarun Turai, inda Bayern Munich ta cire Real Madrid, Atletico Madrid ita kuma ta doke Barcelona, Arsenal ta fidda Sporting CP, yayinda PSG ita kuma ta samu galaba kan Liverpool. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...............
Matakan da CAF ke dauka don warware dambarwar da ke tsakanin Morocco da Senegal 13.04.2026 10:00
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Khamis Saley ya yi duba akan dambarwar da da ta taso dangane hukuncin karɓe nasarar Senegal ta lashe kofin Afrika na baya bayan da hukumar CAF tayi tare da maida nasarar ga ƙasar Morocco Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Hasashe game da rawar da ƙasashen Afirka za su taka a gasar lashe Kofin Duniya 06.04.2026 10:00
Shirin a wannan lokaci tare da Khamis Saleh ya yi duba ne kan yadda aka kammala samun tawagogin ƙasashen da za su fafata a gasar lashe kofin duniya da ke tafe a watan Yuni mai zuwa. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
Amurka ta gargaɗi masu aniyar maƙalewa idan suka je kallon gasar cin kofin duniya 09.03.2026 10:00
Shirin Duniyar Wassani a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda Amurka ta fara gargaɗin ƴan Ghana da ke da aniyar maƙalewa idan suka je ƙasar don kallon gasar cin kofin duniya da ƙasashen Amurka da Canada da kuma Mexico za su karɓi baƙunci a watan Yuni mai zuwa. Ganin irin matakan da dama gwamnatin Amurka ke ɗauka kan shigar baki ƙasar tuni ofishin Jakadancin ƙasar da ke Ghana ya fara gargaɗin masu...
FIFA za ta jagoranci koyar da ƙwallon ƙafa a makarantun Nijar 02.03.2026 9:57
Shirin “Duniyar Wasanni” tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zai yi duba ne kan yadda aka sanya tsarin koyar da wasan kwallon ƙafa a makarantun Boko na Jamhuriyar Nijar. A wannan makon mun yi dubi ne kan shirin koyar da wasan kwallon ƙafa da za a sirka a tsarin koyarwa a makarantun Boko a Jamhuriyar Nijar, a ƙoƙarin da ake yi na haɓɓaka harkar, ganin yanda take a baya sosai a jadawalin ƙasashe d...
Yadda ta wakana a gasar tseren dawaki da ta gudana a garin Daura na jihar Katsina 23.02.2026 9:59
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali ne kan gasar tseren dawaki da aka gudanar a garin Daura da ke jihar Katsina da ke a arewacin Najeriya. A farkon watan Faburairun wannan shekarar ne aka kammala babbar gasar tseren dawaki ta ƙasa da ƙasa da ƙungiyar sukuwar dawaki ta Najeriya ke shiryawa. Wannan ne dai karo na uku da ake gudanar da irin wannan sukuwa a ci...
Taƙaddamar da ta dabaibaye gina filin wasa a jihar Kebbi ta Najeriya 16.02.2026 10:00
Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako, ya mayar da hankali ne kan taƙaddamar da ta dabaibaye gina filin wasa a jihar Kebbi ta arewacin Najeriya. Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Khamis Saleh...
Gasar tseren dawakai da aka gudanar a jihar Jigawan Najeriya 26.01.2026 9:59
Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan gasar tseren dawaki da aka gudanar a jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya.
Senegal ta lashe gasar AFCON karo na biyu bayan nasarar da ta samu kan Morocco 19.01.2026 9:55
A jiya Lahadi ne dai aka buga wasan ƙarshe a gasar lashe kofin nahiyar Afrika ta AFCON karo na 35 da ƙasar Morocco ta karɓi baƙunci, inda Senegal ta samu nasara da ci 1 da nema kan Morocco, bayan da ɗan wasanta Pape Alassene Gueye ya jefa kwallo jim kaɗan bayan ƙarin lokacin. Wasan ƙarshen ya kasance mai cike da cecekuce sakamakon tsaiko minti 20 da aka samu, sanadiyar bugun daga kai sai mai tsaro...
Super Eagles ta nuna bajinta a wasan ta da Aljeriya a gasar AFCON 12.01.2026 9:57
Shirin Duniyar Wasanni na wanan mako tare da Khamis Saley ya yi dubi kan nasarar da tawagar Najeriya ta samu a wasan dab da na kusa da na ƙarshe a gasar AFCON da ake gudanarwa a kasar Morocco. Shiga alamar sauti domin sauran cikakken shirin.....
Yadda aka doka wasu daga cikin wasanni ƴan zagayen 16 a gasar AFCON 05.01.2026 9:59
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Khamis Saleh ya yi duba kan yadda aka dawo da buga wasanni a zagayen ƴan 16 a gasar AFCON da ke gudana a Morocco a karshen mako. a Danna alamar sauti domin sauraron cikakken shirin......
An kammala gasar kokowa ta ƙasa mafi girma a Jamhuriyyar Nijar 29.12.2025 10:00
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda aka kammala gasar kokuwar gargajiya ta ƙasa a Jamhuriyar Nijar. Jiya Lahadi ne aka kammala gasar kokowar gargajiya ta ƙasa a Jamhuriyar Nijar da aka gudanar a garin Tawa, wacce ita ce karo ta 46, inda mai masaukin baki ta lashe takobin bayan ƴan kokowarta biyu sun kai wasan ƙarshe a wannan gasa. Bayan karawa ta min...
Yadda aka yi bikin buɗe gasar cin kofin Afrika ta AFCON a Morocco 22.12.2025 9:59
Shirin "Duniyar Wasanni" tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zay yi duba ne kan yadda aka faro gasar lashe kofin nahiyar Afrika da ƙasar Morocco ke karɓar baƙunci. A daren jiya lahadi ne dai aka buɗe gasar lashe ƙofin nahigar Afrika ta AFCON karo na 35 da ƙasar Morocco ke karɓar baƙunci. An dai buga wasanni tsakanin Morocco da Comoros, inda Moroccon ta samu nasasara da ci 2 da nema, wani abu da k...
Similar podcasts
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.