DW
Taba Ka Lashe
Shirin al´adu, addinai da kuma zamantakewa tsakanin al´ummomi dabam-dabam a duniya. Taba Ka Lashe shiri ne da ke duba batutuwan da suka shafi al'adu da zamantakewa tsakanin al'ummomi da mabiya addinai dabam-dabam a duniya da zummar kyautata zamantakewarsu, zaman lafiya da kuma fahimtar juna tsakani. Muna gabatar muku da shirin ta rediyo a kowane mako, kuna kuma iya sauraronsa a shafinmu na Internet da kuma ta kafar Podcast.
Where to listen?
Podcasts in the app Replaio Radio Coming soonPodcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts
Episodes
Taba Ka Lashe: 27.12.2023 27.12.2023 9:42
Shirin ya duba bikin Hausa Kirista da aka saba gudanarwa a duk ranar 26 ga watan disambar kowace shekara sakamakon kirisimeti. Za mu ji yadda bikin ya samo asali a cikin bukukuwan al'adun Hausawa da ma yadda aka gudanar da shi.
Taba Ka Lashe: 15.11.2023 21.11.2023 9:56
Shin kun san tarihin Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja mazan fama a shirin harkokin wasan kwaikwayo a arewacin Najeriya?
Taba Ka Lashe: 08.11.2023 13.11.2023 9:52
Ko kun san cewa marigayi Shehu Usman dan Fodiyo ya rubuta tarin litattafan ilimi, shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya yi nazari a kai.
Taba Ka Lashe: 25.10.2023 31.10.2023 9:52
Kabilar Dagomba guda ce daga cikin kabilun da ke da matukar tasiri a arewacin Ghana kuma ta yi biki nadi a birnin Kolon na Jamus.
Taba Ka Lashe: 04.10.2023 10.10.2023 9:56
Yadda al'umma a yankin Hausawa suke fadin sunayen yaransu na farko sabanin yadda aka sani a baya.
Taba Ka Lashe:26.09.2023 26.09.2023 9:04
Shirin ya duba muhimmancin tagwaye a lokacin aure a jihar Gaya ta Jamhuriyar Nijar, inda ake gayyatar 'yan biyu da ke a cikin gari da kewaye domin kawo gudurmuwa a wajen bikin 'yan biyu.
Taba Ka Lashe:19.09.2023 19.09.2023 9:51
Shirin ya nufi masarautar Abzinawa ta yankin Zinder da ke Jamhuriyar Nijar don duba tarihi da kuma al'adun masarautar har ma da irin rawar da take takawa wajen sasanta rikice-rikice tsakanin al'umma.
Taba Ka Lashe: (06.09.2023) 12.09.2023 9:46
Shirin na wannan lokaci, ya halarci bikin nunin fasahar zane-zane da fenti da rubuce-rubucen ayoyi ko surori da alamomi na tsayuwa ko wakafi ko kuma kowasula irinsa na farko da makarantar al-Kur'ani da take koyar da wannan darasi ta shirya a Kano.
Taba Ka Lashe: Al'adun Igbo 05.09.2023 9:48
'Yan kabilan Igbo sun kasance a yankin kudu maso gabashin Najeriya kuma suna al'adu masu yawa.
Taba Ka Lashe: 24.08.2023 29.08.2023 9:45
Shirin ya duba yadda Mata 'yan kabilar Kanuri ke ci gaba da rike al'adar nan ta cire takalmansu domin girmama maza
Taba Ka Lashe: 02.08.2023 08.08.2023 10:03
Shirin ya yi nazari kan yadda ske yin watsi da al'adun Hausawa na iyayen da kakanni a yayin bikin aure a Najeriya.
Taba Ka Lashe 18.07.2023 9:45
Jihar Tahoua da ke Jamhuriyar Nijar ta yi rashin wata fittaciyar mawakiya.
Taba Ka Lashe 27.06.2023 27.06.2023 9:32
Shirin ya duba yadda zumunci ya samu koma baya a kasar Hausa sabanin shekarun da suka gabata ba. A wancan lokaci, rike zumunci ya haifar da zaman lafiya da so da kauna da fahimtar juna da tausayin juna. Amma yanzu an iso wata gaba da al'amarin ya lalace. Me ya haifar da hakan? Ina mafita?
Taba Ka Lashe: 31.05.2023 06.06.2023 29:48
Shin ko kuna da masaniya kan wata al'ada da ake yi wa lakabi da "Tarkama"? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan wannan al'ada.
Taba Ka Lashe: 17.05.2023 23.05.2023 9:56
Shirin ya yi nazari kan wasu daga cikin al'adun Tubawa.
Taba Ka Lashe: 10.05.2023 16.05.2023 9:32
Masarautar Kano ta nada sabbin hakimai a kokarinta na kyautata al'ada da riko da tsarin da magabata suka dora ta a kai. Ko ya ya ake nadin sarautar hakimci a kano? Ko ya ya masarautun arewacin Najeriya ke aron sarauta a tsakaninsu.?
Taba Ka Lashe: 03.05.2023 09.05.2023 9:41
Shirin ya yi nazari kan yadda ake gudanar da bukukuwa da ma hawan salla a jihar Katsina da ke Najeriya
MMT/ Kultur(05-04-23)Niger Ramadan Tashe - MP3-Stereo 11.04.2023 9:37
Taba Ka Lashe: Tashe lokacin Azumi
Taba Ka Lashe 14.03.2023 9:45
Gidan tarihi na Kanta Museum dake garin Argugu a jihar Kebbi da ke Najeriya na kara samun karbuwa da tagomashi.
Taba Ka Lashe: 01.03.2023 07.03.2023 9:42
Ko kun san tabarbarewar tarbiyya da watsi da al'adu kan kawo lalacewar matasa su shiga wasu miyagin dabi'u da kuma ka iya shafar zamantakewar al'umma? Dangane da haka ma'aikatar kula da al'adu ta Jamhuriyar Nijar ta dauki matakin dakile wannan matsala. Shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya yi nazari kan matakan.
Taba Ka Lashe: Wasu kabilru sun hade domin fahimtar juna 21.02.2023 10:08
Wasu kabilu kimanin takwas a karamar hukumar Toro da ke jihar Bauchi a Najeriya sun hade wuri guda tare da dabbaka al'ada daya.
Taba Ka Lashe: 24.01.2023 30.01.2023 9:43
Ko kun san al'adar mutanen Zuru da ke jihar Kebbin Najeriya? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari.
Taba Ka Lashe 17.01.2023 24.01.2023 9:48
Yadda al'adar Fulani ta auren gida ta fara sauyawa sannu a hanakli a Najeriya.
Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.