RFI Hausa
Lafiya Jari ce
Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.
Обов'язково відвідайте сайт подкасту та підтримайте його автора: www.rfi.fr
Де слухати?
Подкасти в застосунку Replaio Radio Уже незабаромПодкасти незабаром з'являться в застосунку. Встановіть уже зараз і першими побачте зовсім новий погляд на подкасти
Епізоди
Kalubalen da ake fuskanta wajan yaki da cutar babban tari ko tuberculosis 06.04.2026 10:01
Shirin Lafiya Jarice na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali gameda tarin matsaloli da gangamin yaki da babban tari ke cin karo dasu. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin........
Najeriya ta karɓi sabbin alluran rigakafin cutar HIV 30.03.2026 10:19
Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan sabbin alluran rigakafin cutar Sida ko kuma HIV Aids da Najeriya ta karɓa ƙarƙashin shirin yaƙi da wannan cuta mai haɗari. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shiri....
Haɗarin cizon mahaukacin kare da ke haddasa cutar zangai maras jin magani 23.03.2026 9:28
A wannan makon shirin na lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba kan matsalar cutar zangai ko cizon mahaukacin kare, cutar dake daɗa bazuwa a jamhuriyyar Nijar musaman a Jihar Maradi, jihar dake sahun gaba wajan masu fama da wannan matsala. Alƙaluman ofishin ministan lafiya na jamhuriyyar Nijar sun nuna cewa cikin mutane 10 da cutar ta kashe, 5 sun fito ne daga jihar Maraɗi, inda aka...
Jita-jitar dake alaƙanta kamuwa da cututtuka ta hanyar amfani da kayayyakin lantarki 16.03.2026 9:59
A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan jita-jitar da ke alaƙanta amfani da wasu kayakin lantarki a matsayin dalilan da ke sabbaba kamuwa da wasu nau’ikan cutuka ciki har da Cancer. A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan jita-jitar da ke alaƙanta amfani da wasu kayakin lantarki a matsayin dalilan da ke sabbaba kamuwa da wasu nau’ikan cutuka ciki h...
Cututtukan da ke barazana ga lafiyar jama'a a lokacin azumi 09.03.2026 10:08
Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali ne kan irin cututtuka da ke barazana ga lafiyar al'umma a lokacin azumin watan Ramadan, musamman ga masu azumi da ke fuskantar sauye-sauyen lafiyar jiki. Galibi a duk lokacin da aka faro azumi, mutane da dama musamman masu kwantattun cutuka kan taso musamman idan mutane basu ɗauka matakan da suka kamata ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron...
Zubar hazo a lokacin zafi ya haddasawa mutane da dama rashin lafiya a Kamaru 02.03.2026 10:06
A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan sauyawar yanayin da wani yanki na arewacin ƙasar Kamaru ya gamu da shi a watan Fabarairun da ya gabata wanda ba safai aka saba ganin faruwarsa ba, ta yadda ake ganin zubar hazo a wani yanayi da kuma ake fama da tsananin zafi, wanda ya haddasa cutuka, lamarin da ya sanya gamayyar masana lafiya dana yanayi jan hankali jama’a don su ɗauk...
Yadda yakamata jama'a su kula da cimakarsu a lokacin azumin Ramadan 23.02.2026 10:04
Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako zai mayar da hankali kan cimaka a lokacin azumin watan Ramadana, dama yadda wasu ke fuskantar matsaloli masu alaƙa ɓacin ciki sakamakon yanayin ciye-ciyen da akan yi ko dai a lokacin buɗa baki ko kuma sahur. Kamar yadda ya ke bisa al’ada a irin wannan lokaci na azumin watan Ramadan, musulmi kan ƙauracewa abinci da abin sha tun gabanin...
Najeriya ta ƙaddamar da dokar ta ɓaci a harkar kiwon lafiya 02.02.2026 10:09
A wannan makon shirin zai yi dubi ne kan dokar ta baci a harkan lafiya da gwamnatin Najeriya ta kaddamar inda ta sanar da karuwar cutuka masu alaka da gurbatacciyar iskar da jama’ar ƙasar ke shaka. Hukumar duba gari ta Najeriya ko kuma Environmental Health Council a Turance ita ta sanar da wannan dokar ta baci inda tace munin cutukan dake alaka da numfashi da kuma cutar kansa dake karuwa yasa dole...
An fara gangamin rigakafin cutar Typhoid irinsa na farko a Jamhuriyyar Nijar 19.01.2026 9:47
Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan gangamin rigakafin cutar Typhoid da mahukuntan Jamhuriyyar Nijar suka faro a faɗin ƙasar, irinsa na farko da aka taɓa gani a tarihi a wani yanayi da ake ganin ta’azzarar wannan cuta a ƙasar ta yankin Sahel. Wasu alƙaluman hukumar Lafiyar Jamhuriyyar Nijar a 2021 sun ce mutane dubu 30 suka kamu da cutar, a wancan lokaci wadda ta haddasa m...
Illolin da sauyin yanayi ke haifarwa ga lafiyar jama'a 12.01.2026 9:58
A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali ne kan illolin da sauyawar yanayi ke haifarwa ga lafiyar jama’a, musamman ganin yadda hunturu ya fara amma kuma kwatsam ya ɗauke cikin ƙanƙanin lokaci tare da shigowar zahi, lamarin da ya haddasa cutuka masu yawa a tsakanin jama’a.
Ɓullar annobar ƙyanda ta t'azzara a sassan Najeriya 05.01.2026 10:04
A wannan makon shirin tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan fitar wasu sabbin alƙaluman hukumar NCDC masu tayar da hankali matuƙa da ke nuna yawaitar ɓullar cutar ƙyanda ko kuma baƙon dauro dama ƙaruwar mutanen da take kashewa a sassan Najeriya. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.......
Illar ta'ammali da magungunan ƙara kuzari ko rage gajiya da jama'a ke yi 22.12.2025 9:59
Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan karon ya mayar da hankali kan yadda ɗabi’ar ta’ammali da wasu nau’ikan tsumin gargajiya da sunan samun kuzari ko kuma ƙarfin jiki ke ci gaba da ta'azzara tsakanin jama'a, wanda masana suka yi ittifaƙin na da matuƙar illa ga lafiyar jama’a. Tsumi na baya-bayan nan da ke samun karɓuwa tsakanin jama’a musamman masu ayyukan ƙarfi shi ne ‘’Wanki...
Dabarun yaƙi da ƙibar da ta wuce ƙima ko kuma Obesity tsakanin matasa 15.12.2025 9:57
Shirin Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir a wannan mako ya mayar da hankali kan wasu alƙaluman mujallar Lancet da ke nuna cewa nan da shekarar 2050 fiye da kashi 50 na yawan al’ummar Afrika musamman Afrika za su zama masu ƙibar da ta wuce ƙima ko kuma Obesity a turance. Alƙaluman na Lancet wanda aka tattara bayan gwaji a ƙasashe fiye da 50 ya nuna cewa matsloli masu alaƙa da cimaka da kuma rashin...
Replaio не є видавцем подкастів; назви шоу, обкладинки та аудіо належать їхнім авторам і поширюються через публічні RSS-канали