RFI Hausa

Kasuwanci

Business HA ↓ 38 episodes

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

Be sure to visit the podcast's website and support the creator: www.rfi.fr

Author

RFI Hausa

Category

Business

Podcast website

www.rfi.fr

Latest episode

Nov 11, 2026

Where to listen?

Podcasts in the app Replaio Radio Coming soon

Podcasts are coming to the app soon. Install now and be the first to see a whole new take on podcasts

Get it on Google Play Install for free Android 10M+ downloads · 4.7+ rating iOS soon

Episodes

Tasirin ma'adanan ƙarƙashin ƙasa wajan bunkasa tattalin arzikin Najeriya 11.11.2026

Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan mako tare da Nura Ado Suleimane ya yi  waiwaye kan fannin haƙar ma’adanan a Najeriya domin tattaunawa da masu rusa da tsaki kan ayyukan haƙar ma’adanan dangane da dalilan yawaitar masu waɗannan ayyuka ba tare da lasisi ba, da kuma yadda za a magance matsalar a sauƙaƙe.  Latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin........

Yadda fasahar AI ke tasiri wajen sauya harkokin bankuna a duniya 21.10.2026

Shirin a wannan mako tare da Ahmed Abba zai mayar da hankali ne kan yadda na’ura da aka  ƙimsawa tunanin ɗan adam wato AI ke sauya harkokin banki a duniya. Artificial Intelligence, wato fasahar AI, na ƙara sauya yadda ake gudanar da harkokin tattalin arziki a duniya, ciki har da bankuna da hada-hadar kuɗi. Daga gano zamba cikin mu’amalolin kuɗi zuwa tantance masu neman rance, ba da amsoshi ga abok...

Borno na son farfado da tattalin arzikin waɗanda ricikin Boko Haram ya ɗaiɗaita 14.10.2026

Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin jihar Borno da samar da hanyoyin dogaro da kai ga al'ummar da rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita. Bayan kwashe shekaru da dama na rikicin Boko Haram  da kuma tasirinsa ga tattalin arziki, gwamnatin jihar Borno da ke ar...

Rahoton CBN ya ce ƙarfin sayayyar ƴan Najeriya ya ƙaru a watan Satumba 07.10.2026

Yau shirin zai mayar da hankali kan sabon rahoton Babban Bankin Nigeria, wanda ya fito da sabbin alkaluman ci gaban da aka samu a fannin damar iya sayen kayayyaki a kasuwanni a tsakanin al’ummar kasar da ya karu da maki 53 a watan Satumba daga maki 52.7 daga watan Agustan da ya gabata. Madallah! Lallai za’a yi cewa, tattalin arzikin Najeriya na farfadowa bisa alƙaluma, amma ga talakan ƙasar, har y...

Dalilin da ya sanya aka fara haramta sana'ar jari bola a wasu sassan Najeriya 30.09.2026

Sana’ar tattara wa da sayar da tsofaffin ƙarafa da sauran tarkace wadda aka fi sani da ‘Bola Jari’ na daga cikin sana’o’i da dubban mutane masamman matasa ke dogaro da su a Najeriya. Amma a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sana’ar ta fuskanci babban ƙalubale, musamman saboda zargin cewa wasu masu tattara ƙarafa na amfani da ita wajen sayar da kayayyakin da aka sace daga tituna, gadoji, layin do...

Matatar matatar Ɗangote ta ƙaddamar da sayar da hannayen jarinta a hukumance 16.09.2026

Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan ƙaddamar da shiga matatar Ɗangote kasuwannin hannayen jarin Najeriya, a wani biki da aka gudanar a babban shelkwatan kasuwannin hannayen jarin Najeriya da ke Marina a birnin Legas, inda shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko da kansa ya kaɗa ƙararrawar buɗe shigar matatar a hukumance. Matatar ta sanya hannun jari biliy...

Tasirin da saida hannun jarin matatar man Dangote ke da shi ga al'umma 09.09.2026

Shirin kasuwa akai miki dole na wannan lokacin, ya maida hankali ne kan yadda matatar Dangote ta shirya buɗe ƙofifinta ga al’umma domin su mallaki wani kaso a matatar mafi girma a Afirka, bayan da a karon farko ta sanar da shiga kasuwar hannayen jari. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba...........

Sharhi kan kalaman Alhaji Atiku na maido da tallafin mai a Najeriya 02.09.2026

Shirin ‘kasuwa akai miki dole’ a wannan mako tattauna ne kan wasu batutuwa da suka taso masu nasaba da siyasa da tattalin arziƙi a Najeriya, Inda muhawara ta kaure kan batun tallafin man fetur, bayan da  ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyyar adawa ta ADC Alhaji Atiku Abubakar ya yi alƙawarini maido da tallafin man idan aka zaɓe shi a 2027, to amma nan da nan gwamnatin Najeriyar ta mayar da ma...

Ghana ta zama ƙasa ta 6 a cikin jerin ƙasashen da ke samar da zinari a duniya 26.08.2026

Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda Ghana ta zama ta shida a cikin manyan ƙasashe da suka fi samar da zinare a duniya, bayan zarce Amurka a alƙaluman yawan zinare da ƙasar ta yammacin Afirka ta hako a shekarar 2025 da ta gaba. To, amma menene tasirin kasancewar ƙasar ta ɗaya daga cikin manyan masu samar da zinare a duniya ke nufi ga talakawan Ghana da kuma ta...

Me cigaban kasuwar hannayen jarin Najeriya ke nufi ga talakan ƙasar kashi na 2 19.08.2026

Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya dora kan shirin makon da ya gabata, wanda ya mayar da hankali kan ci gaba da kasuwar hannayen jarin Najeriya ta samu, wajen zama ta ɗaya a duniya, kamar yadda mujallar Bloomberg ta sanar a ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta 2026. To amma me cikin gaban kasuwar hannayen jarin ke nufi ga takan ƙasar?

Cigaban kasuwar hannayen jari na nufin rayuwa ta fara inganta ga talakan Najeriya? 12.08.2026

A ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta 2026, mujalar Bloomberg da ke bibiyar harkokin tattalin arzikin ƙasashen duniya, ta bayyana kasuwar hannayen jarin Najeriya a matsayin ta ɗaya a duniya a fannin dala, wajen yi wa ta Koriya ta Kudu fintinƙau. Masana tattalin arziki sun alakanta wannan gagarumin ci gaba da kasuwar ta samu da sauye-sauye masu tsauri da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi...

Ghana ta yiwa ƙasashen Afrika fintinkau a fannin ci gaban hada-hadar kuɗaɗe ta wayar hannu 05.08.2026

Shirin na wannan mako ya duba yadda Ƙasar Ghana ta zama jagaba a fannin hada_hadar kuɗi ta wayar hannu a Afirka, inda a wannan shekara kaɗai kamfanonin sadarwar wayar tafi da gidanka suka yi hada-hadar sama da Cidi biliyan 40. Ku danna lamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

Illar cushen kusan naira tiriliyan 1 a kasafin kuɗin Najeriya ga tattalin arziƙi 29.07.2026

Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako, ya mayar da hankali ne kan yadda aka gano cushen kusan Naira triliyan ɗaya cikin kasafin kuɗin Najeriya na wannan shekarar ta 2026, domin sayen motocin alfarma da kuma ayyukan tallafa wa jama'a. Wannan na ƙunshe ne cikin wani rahoton da wata  cibiyar da ke sa’ido kan yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗen kasafi a Najeriya wato Tracka. Cibiya...

Matakin matatar Ɗangote ya fusata ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya 22.07.2026

Shirin a wannan mako tare da Ahmed Abba  ya yi dubi ne kan matakin da ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya ta sanar na dakatar da sayen mai daga matatar Dangote, sakamakon matakin da matatar ta ɗauka na fara sayar musu da man da take tacewa da dala maimakon Naira. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

Rashin rassan bankuna ya tilastawa al'ummar karkara rungumar POS a Najeriya 08.07.2026

Shirin kasuwa akai miki dole dake bibiyar harkokin kasuwanci da tattalin arziki na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ci gabar fasahar zamani da aka samu a fannonin haɗar-haɗur ƙudi a Najeriya, ke shafar al’ummomi a yankunan ƙarƙara.

Ana samun ƙaruwar cin bashin kuɗin kiran waya tsakanin jama'ar Najeriya 01.07.2026

Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan Najeriya suka rungumi ɗaukar bashin kiran waya, wanda wani rahoto ya ce, a bara kaɗai anci bashin kiran waya da ƙudinsu ya kai Naira Tiriliyan 4 da biliyan 61. Wasu bayanai da cibiyar fintech firms Optasia mai tattara alƙaluman shige da ficen kuɗaɗen layukan sadarwa ta fitar a baya-bayan nan, ya...

Yadda tattalin arzikin Ghana ke haɓɓaka sannu a hankali 17.06.2026

Yau shirin ya mayar da hankali ne dangane yadda tattalin arzikin ƙasar Ghana ke ci gaba da ɓunƙasa sannu a hankali. Ku danna alamar sauraro domin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

Koken ƴan Najeriya kan yadda bankuna ke zare musu kuɗi daga asusun ajiyarsu 20.05.2026

Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan yadda ƴan Najeriya, ke nuna fushinsu dangane da zargin cire musu kuɗi ba bisa ka’ida ba daga asusun bankunansu. Miliyoyin 'yan Najeriya da yanzu haka ke fuskantar hauhawan farashin kayayyaki da kuɗin sufuri, da kuma rashin tabbas ga makomarsu a fannin tattalin arziki, caje-caje da dama da bankuna ke yi a asusun ajiyars...

Yadda ƴan kasuwa a Najeriya suka jingine harakokinsu saboda tsadar sufuri 13.05.2026

Shirin Kasuwa akai miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

Yadda tsadar sufuri ya tilastawa 'yan kasuwa jingine sana'o'insu a Najeriya 13.05.2026

A yau shirin ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Sannu a hankali, irin hada-hadar da aka saba gani tsakanin mafi yawan kasuwannin Nigeria na neman zama abun tarihi, sakamakon yadda ‘yan kasuwa masu tarin yawa suka jingine harkokinsu na kasuwanci saboda tsad...

Damarmaki da kuma ƙalubalen da manoman Albasa a arewacin Kamaru ke fuskanta 29.04.2026

Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon, ya duba  ƙalubale da kuma damammaki a ɓangaren noman albasa a arewacin Kamaru. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

Matakan da bankin CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗi a Najeriya 22.04.2026

Shirin Kasuwa akai miki doke na wannan mako ya yi duba ne kan matakan da babban bankin Najeriya CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗaɗe, domin rage hauhawan farashin kayayyaki a kasuwanni da kuma daga darajar kuɗin ƙasar wato Naira, ta hanyar rage kuɗaɗe da ke yawo a hannun jama’a. Babban Bankin Nigeria, ya fito da bakin alƙalamin adadin kuɗaɗen da ke bankuna da waɗanda ake hada-hada d...

Yadda matsalolin tsaro ke kassara kasuwanci a arewacin Najeriya 08.04.2026

Shirin na wannan makon ya mayar da hankali ne kan irin fargabar da 'yan kasuwar arewacin Najeriya da ke fatauncin kayayyaki zuwa wasu sassan jihohi ke ciki, sakamakon ayyukan bata gari da ke tare hanya wanda a wasu lokuta kan kai ga rasa rayuka. Abune da aka saba gani, ‘yan kasuwar dake hada Hada tsakankin jihohi daga wannan kasuwa zuwa waccan ko tsakanin kasuwannin kauyuka. To sai dai Kuma irin w...

Yadda matasa ke fatan cin gajiyar yarjejeniyar tattalin arziki tsakanin Nijar da Algeria 01.04.2026

Matasa a Agadez da ke arewacin Jamhuriyar Nijar na cike da fatan cin moriyar sabuwar dangatakar da aka kyautata tsakanin kasar da makwabciyarsu Aljeriya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

Koma bayan da kasuwancin duniya ya fuskanta sakamakon rikicin Gabas Ta Tsakiya 18.03.2026

Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" tare da Ahmed Abba a wannan mako ya ɗora ne kan inda ya tsaya a makon jiya, game da gagarumin koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arziki da duniya ke fuskanta masamman a bangaren makamashi, sakamakon yaƙin da kawancen Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran, da kuma martinin jamhuriyar musuluncin kan Isra’ila da muradun Amurka a kasashen labarawa suka janyo. A...

Listen to the Kasuwanci podcast in Replaio

Radio and podcasts in one app - free, with no sign-up. Install today and do not miss the launch

Get it on Google Play

Replaio is not a podcast publisher; show names, artwork and audio belong to their authors and are distributed through public RSS feeds.