RFI Hausa

Lafiya Jari ce

Science HA ↓ 38 Folgen

Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.

Besuch unbedingt die Website des Podcasts und unterstütze die Macher: www.rfi.fr

Autor

RFI Hausa

Kategorie

Science

Podcast-Website

www.rfi.fr

Neueste Folge

19. Okt 2026

Wo hören?

Podcasts in der App Replaio Radio Bald verfügbar

Podcasts kommen bald in die App. Installiere sie jetzt und erlebe als Erster einen ganz neuen Blick auf Podcasts

Bei Google Play herunterladen Kostenlos installieren Android fast 10 Mio. Downloads · Bewertung 4,8 iOS bald

Folgen

Tsadar maganin asibiti ya tilasta wa wasu jama'a komawa amfani da gargajiya 19.10.2026

A wannan makon shirin ya yi nazari kan yadda tsadar maganin asibiti ke tilastawa jama’a karkatawa amfani da magungunan gargajiya, kodayake akwai kiraye-kirayen masana game da illar waɗannan magunguna a mahangar likitanci. A ƙasashe irin Najeriya magungunan na gargajiya na matsayin hanyoyin neman waraka wanda aka gada tun kaka-da-kakanni kuma aka yi amanna da tasirinsu, duk kuwa da kiraye-kirayen ƙ...

Ƙalubalen lafiyar da matsalar birkicewar al'ada ke haifarwa ga mata 12.10.2026

Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi nazari kan matsalar birkicewar al’ada a tsakanin mata, matsala ce da ke matsayin ruwan dare a wannan zamani lura da cewa kusan dukkanin 1 cikin mata 3 akan iya samunta da wannan matsala wadda kuma ba safai aka fiya mayar da hankali akanta ba, duk kuwa da ƙalubalen hakan ga lafiyar mata. Mata da dama ne dai suka shafe shekaru suna...

Yawaitar ɓarkewar cutar Diptheria a sassan jihohin Najeriya 05.10.2026

A wannan makon shirin ya yi duba kan cutar Diptheria, ko kuma mashaƙo, cutar da a baya-bayan nan ake yawan ganin ɓarkewar annobarta a wasu sassa na jihohin Najeriya wadda kuma ke kisan ɗimbin mutane baya ga kwantar da dama a asibitoci, inda wasu alƙaluma ke cewa daga watan Janairu zuwa Agustan shekarar nan mutane dubu 16 da 997 suka kamu da cutar a sassan Najeriya. Masana sun yi ittifaƙin cewar ma...

Rawar da Ungozomar gargajiya ke takawa wajen ceton rai a yankunan karkara 28.09.2026

Goyon ciki da haihuwa na cikin mayan ƙalubalen Lafiyar da suka addabi ƙasashe masu tasowa irin Najeriya, ta yadda a kowacce rana ake ganin mutuwar ɗimbin mata a lokacin haihuwa ko kuma renon ciki, baya ga tarin jarirai da ke rasa ransu. A irin wannan yanayi galibi Ungozomar gargajiya ke matsayin masu ceto a irin wannan yanayi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir...

Lafiya Jarice: Muhimmancin tazarar haihuwa ga lafiyar uwa da jaririnta 21.09.2026

Bisa ga zubin halittar ɗan adam kowacce mace kan iya haihuwa aƙalla sau 15 zuwa 30 a tsawon rayuwarta, a wani yanayi da ƙasashen Afrika ke sahun gaba wajen yawan haihuwar, kodayake liktoci na jan hankali game da muhimmancin bayar da tazara ko kuma hutu koma taƙaita haihuwar baki ɗaya saboda dalilai na lafiya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.

Mata dubu 14 ke kamuwa da cutar kansar mahaifa a Najeriya duk shekara-Rahoto 14.09.2026

Shirin Lafiya jari ce na wannan mako ya mayar da hankali ne kan cutar dajin mahaifa da ke addabar mata musamman a Nahiyar Afrika. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashi Aminu.

Illar da ke tattare da shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba 07.09.2026

Shirin lafiya jari ce a wannan karon ya mayar da hankali kan ɗabi'ar shan magani ba tare da shawara ko umarnin likitoci ba, wanda a turance ake kira Self-medication da kuma illar hakan ga lafiyar jama’a. Wasu alƙaluma sun nuna cewa fiye da kashi 70 cikin ɗari na ƴan Najeriya ne yanzu haka sun bijirewa ziyartar asibitoci ta yadda suke shan magungunan tarin cutuka ba tare da umarnin ƙwararru ba, mus...

Yadda cutar damuwa ke zama ruwan dare a tsakanin al'umma 24.08.2026

A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce zai yi duba ne kan lalurar Depression ko kuma damuwa mai tsanani a harshen hausa, cutar da ke ƙoƙarin zama ruwan dare tsakanin al’umma a baya-bayan nan, wataƙila ko saboda yanayi da matsin rayuwa. Ku danna almar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.

Yadda wuraren saida magunguna ke samun karbuwa a jamhuriyar Nijar lokacin damuna 17.08.2026

Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya leƙa jamhuriyyar Nijar inda ya yi dubi kan yadda ake samun kafuwar wuraren saida magunguna birjik musamman a lokaci irin na damuna, wato dai lokacin da ake ganin yawaitar cutuka irin zazzaɓin cizon sabro. Danna alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....

Yadda cutar kwalara ta jefa ɗumbin mutane cikin firgici a jihar Bornon Najeriya 10.08.2026

A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan sake ɓarkewar cutar kwalara ko kuma amai da gudawa a jihar Borno, lamarin da ya jefa ɗimbin jama’a a yanayi na matuƙar damuwa damuwa musamman bayan da rahotanni ke cewa an samu yaɗuwar annobar cutar har a yankunan da ake ajje da ɗimbin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu.

Yadda cutar Bilharzia ko Tsagiya ke barazana ga rayuwar ɗimbin ƴan Afirka 03.08.2026

A wannan makon shirin na lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba duba kan cutar Schistosomiasis (shustosumayusus) ko Bilharzia koma Snail fever kamar yadda wasu ke kiranta, cutar nan dai da aka fi sani da tsagiya a hausance, cutar alƙaluma ke nuni da cewa kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da ita na a nahiyar Afrika. Shiga alamar sauti don sauraron karin bayani.......

Yadda farashin magunguna ke tashi a lokacin damuna da aka fi fama da cutuka 27.07.2026

Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya yi dubi ne kan yawaitar cututtuka a irin wannan lokaci na damuna, daidai lokacin da bayanai ke nuni da cewa farashin magunguna ya yi tashin gauron zabbi. Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Azima Bashir Aminu...

Yadda gwamnatin Kano ta yi nasarar rage mace-macen mata a lokacin haihuwa 20.07.2026

Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu  ya mayar da hankali kan nasarar da jihar Kano ke iƙirarin samu bayan fitar wani rahoto da ke cewa an samu raguwar mace-macen mata a lokacin haihuwa a sassan jihar wadda a baya ke sahun gaba wajen asarar rayukan ɗimbin mata a lokacin haihuwa ko goyon ciki Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin..........

Matsalar ƙarin mahaifa ko fibroids ga lafiyar mata 13.07.2026

Shirin Lafiya Jari Ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar ƙaba ko ƙarin mahaifi ko kuma fibroids da ke addabar tarin mata ta yadda da dama ke rayuwa da shi ba tare da sani ba, yayinda wanzuwarsa a mahaifa kan haddasa matsala ga yanayin haihuwa ga matan. Galibi mata a tsakanin shekaru 35 zuwa 37 ne suka fi kamuwa da wannan lalura ta Fibroids, a wani yanayi da ƙidi...

Yadda cutar Typhiod ke barazana ga rayuwar miliyoyin mutane a Afirka da Asiya 06.07.2026

Shirin na Lafiya Jari ce zai  a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan zazzaɓin Typhoid, cuta mai haɗari wadda ƙwayar cutar Salmonella Typhi ke haddasawa, inda ta kan yaɗu ta hanyar abinci ko ruwan da ya gurɓata. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

Ƙaruwar masu fama da cutar sikila a Jamhuriyar Kamaru 29.06.2026

A wannan makon shirin ya yi duba ne kan ƙaruwar masu fama da cutar sikila a jamhuriyyar Kamaru bayan fitar wani rahoto da ke cewa cikin shekara 1 kaɗai an tattara alƙaluman sabbin mutum dubu 6 da aka gano suna ɗauke da cutar. Wannan cuta mai alaƙa da nau’in jini, na daga cikin matakan yaƙi da ita shi ne tabbatar da gwaje-gwajen jini tun kafin aure don kaucewa haifar yara masu ɗauke da ita, ganin c...

Illolin da ke tattare da sauya launin fata da wasu mata ke yi 08.06.2026

Shirin lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda mata suka rungumi tsarin gyaran jiki ta fannoni daban-daban kama daga magungunan sha ko mayukan shafawa ko kuma salon amfani da na’ura da nufin ƙawata sura. Wasu daga cikin batutuwa mafi jan hankali a wannan babi na gyaran jiki shi ne tayar da komaɗar fata da sauran sassan jiki don killacewa ko kuma kange kai daga bayyanar tsufa, k...

Illolin magungunan matsi ga lafiyar mata 01.06.2026

Shirin a wannan mako zai ɗora ne akan wanda ya gabace shi a makon jiya, sai dai a wannan karon zamu karkata ga illolin da magungunan matsi ke haifarwa ga lafiyar mata, duk da ya ke matan kan yi don bajinta ko nuna isa a wajen mazajensu. Danna alamar sauti don sauraron karin bayani.....

Abubuwan da ke haddasa cutuka ga al'aura ko matantaka ga mata 25.05.2026

Shirin Lafiya Jari ce na wannan makon ya yi nazari kan ƙaruwar matan da ke fama da cutuka masu alaƙa da al’aura ko kuma matantaka, tare da laluben hanyoyin magancesu ta hanyar tattaunawa da ƙwararru a wannan fanni, cutukan da ƙwararrun ke alaƙantawa da rashin baiwa al’aurar kariya wanda a lokuta da dama ke haddasa gagarumar matsala. Ku lasha alamar sauti don sauraron shirin tare da Azima Bashir Am...

Abubuwan da ya kamata a sani kan sabuwar cutar Hantavirus da ta ɓulla 18.05.2026

Shirin Lafiya Jari Ce a wannan makon ya yi nazari kan cutar Hantavirus da duniya ta ga ɓullarta a baya-bayan nan, lamarin da ya sanya fargaba a zuƙatan jama’a, musamman ganin yadda ake alaƙanta wannan cuta a sahun masu haɗari da tarihi ya nuna yaddda suka yiwa duniya ɓarna matuƙa. Cikin watan jiya ne aka ga ɓullar wannan cuta a wani jirgi da ya taso daga Argentina zuwa Cape Verde, sai dai tilas ya...

Yadda ake gudanar da yaƙi da cutar polio tsakanin Nijar da maƙwaftanta 11.05.2026

Shirin lafiya jari Ce a wannan makon zai nazarci yadda ake gudanar aikin yaki da cutar polio tsakanin ƙasashen makwabtan juna wato Najeriya da Nijar a wani yunƙuri na kakkaɓe ɓurɓushin wannan cuta musamman a yankunan kan iyaka na ƙasashen biyu duk kuwa da saɓanin diflomasiyyar da ke tsakanin gwamnatocin ƙasashen biyu.

Wani bincike ya gano yadda kashi 13 na al'ummar Ghana ke rayuwa cutar ƙoda 04.05.2026

A wannan makon shirin na Lafiya Jari Ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi nazari kan wani bincike can a Ghana da ke ƙiyasta cewa kusan kashi 13.3 na yawan jama’ar ƙasar na rayuwa da cutukan ƙoda, galibi ba tare da masaniyar suna ɗauke da ita ba, lura da yadda cutar bata nuna alamu a farko har sai ta kai ga ta’azzara. Wannan na nuna yadda cutar ta ƙoda ke matsayin babban ƙalubale a Ghana. Binciken m...

Yadda tsananin zafin bana ke barazana ga lafiyar jama’a a Arewa 27.04.2026

A wannan makon, shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan tsananin zafin da ake fuskanta a wasu jihohi na yankin Arewacin Najeriya, wanda masana suka yi ittifaƙin ya kai matakin da ka iya haddasa wasu cutuka ko kuma tayar da kwantattu. Zafin na bana ya sha bamban da wanda aka saba gani a kowace shekara, domin jama’a na bayyana cewa ya daɗe bai lafa ba kamar yadda aka saba gani a shekarun ba...

An samu raguwar haihuwa a Najeriya sakamakon rungumar tsarin tazarar Iyali 20.04.2026

Shirin Lafi Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba ne kan wani rahoton sashen bincike da kula da lafiyar jama’a na NDHS da ke ƙarƙashin hukumar kula da yawan jama’a ta Najeriya NPC, wanda ke nuna cewa daga shekarar 2024 yawan haihuwa ya ragu matuƙa tsakan matan Najeriya daga kashi 5.3 zuwa kashi 4.8. Wannan sakamakon rahoto na NDHS a cewar masana manuniya ce kan yadda mata a...

Yadda Cutar Sankarau ke barazana ga wasu ƙasashen yammacin Afirka 13.04.2026

Shirin Lafiya Jari ce a  wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya yi  duba ne kan cutar ɗan sanƙarau ko kuma meningitis, cutar da a yanzu haka wasu ƙasashe ke cikin haɗarin fuskantar ɓullarta musamman a yammacin Afrika, waɗanda dama ke a tubalin fuskantar wannan cuta lokaci zuwa lokaci.

Höre den Podcast Lafiya Jari ce in Replaio

Radio und Podcasts in einer App - kostenlos und ohne Anmeldung. Installiere sie noch heute und verpasse den Start nicht

Bei Google Play herunterladen

Replaio ist kein Herausgeber von Podcasts; die Namen der Sendungen, Cover und Audioinhalte gehören ihren Autoren und werden über öffentliche RSS-Feeds verbreitet